*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf*45*
*Unedited*_Murjanatu Sabi'u, Saudat, Mimi, Laweezat Imam, Zainab Lawal wannan shafin naku ne💕💞_
Dr Ameer ya taso yazo gaban Suraj, Ya duk'a tare da dafa kafad'ar sa yace "Musulmin k'warai yadda da k'addara aka san shi dashi, kada ka d'aga hankalin ka, ka dage da addu'a", Kai kawai ya iya d'aga masa, " Zanje na duba wani patient, na dawo", Ya d'aga mishi kai,Ganin fitowar shi, Su Aliya suka shiga d'aki, Har lokacin Suraj na zaune a k'asa, "Subhanallah Surajo ya haka, Dan Allah ka tashi, kada ka sawa kanka damuwa", Mallam ya fad'a yana kama hannun shi, Suraj ya mik'e tamkar wanda aka zarewa jini, Jikin sa ya matuk'ar yi sanyi,
Aliya da Yasmeen wani sabon babin kuka suka bud'e ganin Fetta bata farfad'o ba, Hajiya ma hankalin ta ya k'ara tashi,
Mallam ya k'arasa bakin gadon, Ya zuba mata ido yana nazari, Ruwa dake gefen gadon ya d'auka, Ya zuba a cup, ya shiga karanta addu'o'i yana tofawa, kusan minti 20 yana yi,
Ya zuba a hannu ya shafa mata a fuska, da tafin hannu, Ya bud'e bakin ta ya zuba wani, Sauran yace Suraj ya shafa mata a mara, Ya karb'a ya shafa mata, Mallam ya cigaba da karanta addu'a yana tofa mata,
K'ara tayi ta dafe kai, A razane Suraj ya kamo hannun ta, " Kin tashi?, meke miki ciwo?", Mallam ya masa alamar yayi shiru, Ya cigaba da mata addu'a, ta shiga fisge fisge, "Zasu kasheni, Marata, Cikina", Suraj dasu Hajiya lamarin ya basu tsoro, Saitin kunnen ta Mallam ya shiga karanta Bak'ara, A hankali ta daina surutai da fisge fisge, Bacci ya d'auke ta, Tana sauke numfashi a hankali, " Alhamdulillah" Malam ya furta,
"Meya sameta, meyasa take haka?" Suraj ya tambaya, wanda kowa a gurin yake son jin amsa, Malam ya nisa yace "Ture aka mata", Hajiya tace " Ture, ban gane ba", "Sihiri ne", " What!" Suraj ya fad'a a razane,
Kowa dake gurin ya girgiza, "Wane azzalumin ne?", Cewar Aliya, Yasmeen tace " Allah ya saka mata", Hajiya ta amsa da "Amin"
"Da zanga wanda ya mata sihiri, da na kashe shi da hannu wallahil azeem", Cewar Suraj cike da tsananin b'acin rai,
" Godiya ya kamata muyi ubangiji ta samu tashi, dan ga dukkan alamu abun yazo mata sauk'i akan yadda aka so", Cewar Mallam, Hajiya tace "Toh Alhamdulillah, Allah ya k'ara tsarewa", Aliya tace " Amin, Allah ya mata tsari dasu", "Amin"
Yasmeen tace "Mutane basu da kyau, basu da imani", " Wallahi" Aliya ta fad'a, Haka suka yi ta jimamin lamarin, Suraj yayi shiru yana nazarin waye zai yi wannan aikin.
Malam da Hajiya sun koma gida, Yasmeen da Aliya a asibitin suka kwana, Suraj ma anan ya kwana, Sam bai runtsa ba, Yana kusa da ita, Sallar asuba kad'ai ta tashe sa,
Ya dawo masallaci yana shirin zama, Ta bud'e idonta ta zube a kansa, "Fatima", Ya kira sunan ta, " Na'am", Farin ciki ya ziyarci zuciya da gangar jikinsa, "Meke miki ciwo?", " Ba komai", Ta bashi amsa but tana jin marar ta na murd'awa kad'an, "Allah ya k'ara miki lafiya", Ta amsa da " Amin" Tana mamakin sa,
Aliya da Yasmeen cike da farin ciki suka shiga jera mata sannu, tare da yin godiya ga Allah da ya tashi kafad'un ta,
Ba b'ata lokaci Suraj ya buk'aci sallama tunda abun ba na asibiti bane, Aka sallame su, suka dawo gida, Hajiya tayi matuk'ar farin cikin ganin ta samu lafiya,
Suraj ya buk'aci kowa yaje gida ya huta shi zai kula da ita, Mallam ya kawo mata zamzam mai d'auke da addu'o'i, ya rubuta mata wasu a paper yace ta rik'a yi,