*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*19*
Aliya zata shiga d'akin ta, Taga na Fetta a bud'e, "Yau kuma bud'e ta bar d'akin", Ta shiga ta jawo k'ofa, Ganin ta a sheme tasan ba lafiya ba, Ta tab'a ta taji bata numfashi, Hannu ta d'aura a kai ta fasa ihu, A guje Mallam ya shigo d'akin shima ganin Fetta yayi salati ya sanar da ubangiji, a rud'e ya fita, Ya ciko kofi da ruwan randa ya shek'e mata,
Tayi firgigit ta tashi "Ya Mu'azzam Dan Allah kace mun wasa kake, kada ka barni", Aliya ta fahimci meke faruwa cike da tausayin ta, Ta jawo ta jikinta ta rungume, Kuka ta saki mai d'acin rai, duniyar taji ta mata zafi, Ko shakka babu da gaske Ya Mu'azzam ya barta tunda har Umma bata ce wasa yake ba.
Kuka take sosai, Aliya na lallashin ta, Mallam yace " Kiyi hak'uri Fetta, Allah yayi Mu'azzam ba mijin ki bane, kuma watak'ila auren sa ba alkhairi ba ne, Wani baya auren matar wani, Allah ya kawo miki miji nagari da zai k'aunace ki saboda Allah",
A ranta ta cire soyayya ba zata k'ara ba, bata sha'awar sake son da' namiji, bata shirya zuciyarta ta tarwatse ba, A yanzu ma tana daf da.
Alamun bacci tayi, wanda yasa Aliya raba jikinta da nata, Ta kwantar da ita kan katifa, Tasa bargo ta lullub'eta, Suka fita cike da tausayin ta.
Wani sabon babin kuka ta bud'e, K'irjin ta yayi nauyi tamkar an d'aura mata dutse, Da tasan haka soyayya take da bata fara ba, "Ya Allah ka cire mun soyayyar sa, Kada ka k'ara samun son kowanne da' namiji",
A daren bata runtsa ba da zazzab'i ta kwana.
Aliya bayan ta idar da sallar asuba, Ganin Fetta bata fito alwala ba, Ta lek'a d'akin, Kwance ta ganta tana rawar sanyi,
" Subhanallah baki da lafiya ne", Ta fad'a tana tab'a jikinta zafi rau, Ta fita ta sanar da Mallam, "Ohh Kada ta jawo ma kanta wani ciwon", " Shiyasa tun farko banso soyayyar su tayi nisa ba", Ta fad'a cike da damuwa, "Bara naje nan mak'wabta na kira Halima Nurse ta duba ta",
Nurse ta duba ta tace zazzab'i ne, ta mata allura ta rubuta mata magani, Mallam ya karb'a, ba b'ata lokaci yaje yq siyo, Aliya ta lallab'ata tasha tea da bread, ta bata magani, Sai faman sannu suke jera mata, Ganin sun damu tayi k'ok'arin nuna taji sauk'i, Amma ina zazzab'in bai sake ta ba.
Mallam kad'ai ya tafi wurin sana'a, Aliya zama tayi jinyar Fetta, Da tayi motsi kad'an zatace meke damunta, ina ke mata ciwo, Fetta taga soyayya da kulawa wurin Aliya, Ba abunda zata ce musu sai Allah ya saka musu da alkhairi, Sun zama jininta ta d'auke su tamkar iyayen ta.
Suraj ne ya fito daga sashen Hajiya cikin shigar sa ta kamala, Daga yanayin tafiyar sa zaka san sauri yake,
" You have to drive fast, jirgin mu 10:00am zan tashi, an it's already 9:45am", Ya umurci mai tuk'i, Ya figi mota a 360.
"Ya Suraj idan yazo wurin har ya tafi, yana k'amshin sa", Cewar Feena, " Mayen turare yake amfani dashi, though wataran zaka ji yana wani k'amshi daban", Su'ad ta fad'a, " Yana yi ma mask turare ciniki",
Hajiya na jin su murmushi kawai tayi, Son turare gadon sa yayi a wurin Mahaifin sa haka yake da son turare, ko nawa zai iya kashewa ya siya.
Bata ga Aliya ba, balle tasa ran ganin Fetta, Ta tambayi masu aikin sun san dalilin rashin zuwan ta, Suka ce a'ah, Bata tab'a haka ba, idan ba zata samu zuwa ba, Tana aikowa, D'aya daga cikin yaran masu aikin ta umarta tace gidan ta taga lafiya.