*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*25*
UNEDITEDCikin Mintuna kad'an ya iso gidan, ba k'aramin gudu yayi ba, tuk'i yake kamar zai tashi sama, daga yanayin shigowar sa da parking d'in sa ya tabbatar wa ma'aikatan gidan ba lafiya ba, kowane ya shiga zancen zuci,
Part d'in sa ya nufa kai tsaye cike da fatan Allah yasa yaga Fetta, ya mayar da auren sa, bai san me ya shiga kansa ya rubuta sakin ba, "Zuciya da b'acin rai", Zuciyar sa ta bashi amsa, Tsaki yayi yana k'arasawa ciki, Ganin bata falo ya shiga d'aki bata nan, ya lek'a toilet da kitchen babu alamar ta,
Sashen Hajiya ya nufa cike da fargaba, nan ne lost hope d'in sa, babu natsuwa ya shigo falon ba tare da yayi sallama ba, Cirko cirko ya tarar dasu, Aliya da Mallam suma sun zo, hankalin su ya kasa kwanciya a gida, suka nufo nan ko zasu ji wani labari da zai kwantar musu da hankali, Kowa ka kalla fuska d'auke da damuwa, Mallam na ta faman jan charbi,
Hajiya ta fara ganin sa, "Suraj kai ne, ina kuka shiga tun jiya, kun jefamu a damuwa, Ina Fetta?" Ta fad'a tana mik'ewa tare da yin hamdala ga ubangiji, Aliya, Mallam da Yasmeen a tare suka kai dubansu ga Suraj, suna jere hamdala, Tambayar k'arshe da Hajiya ta masa yasa yawun bakin sa tsinkewa, bai san wacce amsa zai bata ba, sabon tashin hankali yaji ya lullub'e sa,
"Ina Fetta ko tana b'angaren ku?", Hajiya ta jefo masa tambayar da ta k'ara dagula lissafin sa, Ganin sa yanayin sa, ya tabbatar ma kowa ba lafiya ba, Aliya a rud'e tace "Wani abu ya sameta? Dan Allah ka sanar damu ina Fetta take?", Yau duk wata kunyar sa ta fice, lafiyar Fetta kad'ai take son ji,
Suraj ya kasa furta komai, sai zufa da ta shiga karyo masa, sanin Fetta bata da kowa sai su Aliya, idan suma basu san ina take ba, toh ina ta nufa, Hajiya ta k'araso gabansa tana rik'o hannun sa tace "Ka sanar damu ina Fetta? Me ya sameta?",
Bashi da wani option da ya wuce ya sanar dasu gaskiya, besides ita ta buk'aci saki a wurin sa, "idan ka fad'a kana da hujjar kare kanka, na dalilin da yasa ta nemi sakin?" zuciyar sa ta fad'a, wani b'angare na zuciyar sa yace "Hanya d'aya ce ka b'oye abunda ya faru tsakanin ku",
"Kayi ma girman Allah ka sanar damu ina Fetta take ko hankalin mu zai kwanta" Mallam ya fad'a cike da damuwa, "Nima bansan inda take ba, ban sani ba" Ya fad'a yana jin yadda zuciyar sa ke bugawa, Hankalin kowa ya matuk'ar tashi da jin furucin sa,
Aliya a wurin ta fad'i tana fashewa da matsanancin kuka, Malam jikinsa gaba d'aya yayi sanyi yana ambaton sunan Allah, Yasmeen zuciyar ta na tabbatar mata akwai wani abu a k'asa da Suraj ya b'oye, "Tabbas ta gano yana d'aya daga cikin yan fashin dasu kashe su Daddy" Cewar zuciyar ta, "But meyasa ta tafi ba tare da ta neme ni ba?" Ta jefawa kanta tambayar da bata da amsa,
"Ka fad'a mana abunda ka sani game da b'acewar Fetta, me ka mata?, Fetta ba zata tafi haka kawai ba tare da wani dalili ba", Hajiya ta fad'a cikin d'aga murya, Suraj wanda zuciyar sa ke tafasa, yana jin tamkar ya d'aura hannu a kai yayi ta tsunduma ihu ko zai samu sassaucin abunda yake ji, da k'yar iya furta "Ban sani ba Mama, ban sani ba", Ya nufi hanyar fita, dishi dishi yake gani har ya kawo bakin motar sa, Ya bud'e ya shiga, yaja motar yana ficewa daga gidan, gefen titi yayi parking, ya d'aura kansa kan sitiyari, bai san ina zai nufa ba, bai san a ina zai ga Fetta da gudan jinin sa ba, "Ya Allah" ya furta yana dafe zuciyar sa dake barazanar tarwatse wa.
Matashin saurayi wanda ba zai wuce shekaru goma sha takwas ba, ta hango ya fito daga wani b'angare na masarautar, yasha nad'i irin na buzaye, kallo d'aya zaka mishi kasan ya had'a jini da masarautar, ga kamanin sa da Addani, Ya nufo wurin da take, "Sannu" Ta fad'a da yaren buzaye, "Yawwa" ya amsa yana bin ta da kallo, ganin tayi kama dasu, gashi tana yaren buzaye, tun tasowar sa, bai tab'a ganin ta a masarautar ba, Tunanin sa ta katse da fad'in "Dan Allah ina ne b'angaren Azagas?", B'angaren da ya fito taga ya nuna mata, "Nagode" ta fad'a tana nufar b'angaren, yabi bayanta da kallo yana mamaki.
Girman b'angaren yasa ta rasa wacce hanya zata sadata da Azagas, Wata baiwa ta tambaya, ganin kamanin ta yasa babu musu ta mata jagora har turakar Azagas, Falo ne na alfarma, wanda an narka dukiya a ciki, yasha ado da tsarin gidan sarauta, sanyin Ac ta ko'ina yana bugawa, ga k'amshi mai dad'i na tashi, "Aljannar duniya" Fetta ta furta a ranta, tana zama d'aya daga cikin lumtsattsan kujerun dake falon,
"Kin zo a sa'a, yanzu ne lokacin fitowar ta, ki jira a anan", Cewar Baiwar, Ta gyad'a kai tana mata godiya,
Minti biyar da zaman ta, Dattijuwar mace ta fito, wacce kallo d'aya zaka mata kasan hutu ya zauna mata, zaka rantse bata yi shekaru sittin a duniya ba, saboda yadda fatar ta ke shek'i, Kayan alfarma ne a jikin ta wanda sai hamshak'an masu kud'i a cikin sarakuna ke sawa, sam bata lura da Fetta ba wacce tun fitowar ta, ta zuba mata ido tana jin k'aunar ta da farin ciki na ratsa ta na tozali da kakar ta, mahaifiyar Addani,
Manyan manyan tuntun na alfarma da aka zagaye wani b'angare na falon dasu, anan Azagas ta zauna, tana kishingid'a, d'ago kanta da zata yi suka had'a ido da Fetta, Gabanta ya fad'i tayi saurin tashi zaune, Kafin tayi magana, Fetta ta fad'a jikinta tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya wanda na farin ciki ne, Azagas tsintar kanta tayi da rungume Fetta, tana d'aura hannun ta kan Mimi dake goye a bayan ta,
Sai da ta tsagaita da kukan, Azagas tace "Ko baki fad'a ba nasan Fetta ce yarinyar Gabdullahi", Kanta ta shiga d'agawa tana hawaye, ina ma tare suka zo asalinta da Addani, da farin cikin yafi haka, ba zata tab'a gafartawa Suraj ba da ya zama silar kashe mahaifin ta, wani sabon kuka ya taho mata, "Kiyi shiru Fetta, ba kuka zaki yi ba, Ina Gabdullahi da Zainaba", Cikin sark'ewar murya tace "Sun rasu"
Azagas gabanta yayi mummunan fad'uwa ta shiga jere "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un", Hawaye na wanke fuskar ta, A kullum da burin sake saka Gabdullahi take a idonta, kullum addu'arta Allah ya dawo dashi gare ta, "Ashe ba zan sake ganin Gabdullahi ba, rabuwar k'arshe muka yi ba" Ta fad'a tana fashewa da kuka.
Tun fitar Suraj falon, babu wanda ya samu k'arfin gwiwar sake cewa komai, Malam ganin kukan Aliya ba mai k'arewa ba ne, Yace "Ya isa kukan Aliya, tashi mu tafi", Ta mik'e tana zubar hawaye, ba tare da sun cewa Hajiya komai ba, suka fice, Yasmeen itama ta mik'e tabi bayan su, Hajiya tagumi tayi ta rasa yadda zata b'ullowa al'amarin, zuciyar ta na tabbatar mata akwai abunda Suraj ke b'oyewa.
Kusan minti ashirin kansa na kan sitiyarin ba tare da ya d'ago ba, "Meyasa zaka damu da tafiyar ta bayan ita ta buk'aci sakin, bata son ka, bata son zama da kai" Wani huci yaji zuciyar sa na yi, "I will let her be tunda ita ta buk'aci hakan, bata son jin komai daga gare ni, zan k'yaleta, Mimi jini na ce dole watarana zata dawo gare ni", Ya fad'a yana k'arfafa ma kansa gwiwa tare da k'ok'arin yakice tunanin Fetta, yaja kan motar sa zuwa guest house, yana son kad'aicewa, baya son duk wani abu da zai kawo masa tunanin ta.
Azagas tayi k'ok'arin tsayar da kukan ta, ta shiga lallashin Fetta, k'aunar Azagas taji na ratsa ta wanda ya haddasa tsayuwar kukan nata, Azagas ta kalleta tayi murmushi, itama ta mayar mata, Hannu ta mik'a mata alamar ta bata Mimi,
Ta d'auketa tana jin k'aunar yarinyar, "Ina baban ta, ba tare kuka zo ba?", Fetta murmushin yak'e tayi tace "Ya rasu", "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allah ya jik'an sa, kin ga jarabawa mutuwar uwa, uba, miji Sannu" Ta fad'a tana kamu hannun ta, "Ki bani labarin ki da kika sani bayan tafiyar su Gabdullahi", Ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya ta shiga bata labari, rabuwar su da Suraj ta canza kanun labari cewar accident yayi ya rasu, a lokacin taga littafin Addani, ta gane asalin ta, ta yanke hukuncin zuwa gare su,
Azagas har da hawayen ta na tausayin Fetta jin ta taso cikin rayuwar maraici da rashin gata, Yaron ta Gabdullahi dan' sarauta a matsayin mai gadi, tsanar wanda suka kashe mata shi taji a ranta, ina ma zata gansu, tasa a yanke musu hukunci daidai da abunda suka aikata,
"In Shaa Allahu daga yau kinyi bankwana da maraici, zaki samu gatan da baki tab'a mafarkin samu ba, kin shigo shiga dangin ki Fetta inda zaki samu k'auna mara nn misaltuwa, tabon da kika dad'e dashi a zuciya na rashin asalin ki, a yau zai goge, ina miki alk'awari da d'umbin kulawa da gata"
Fetta sanyi da farin ciki taji na ratsa ta, tana fatan hakan, tana fatan bankwana da dukkan bak'in ciki, ta manta rayuwarta ta baya, tana son fara sabuwar rayuwa.
_Kusa kanwar Mamana a addu'a plss🤲🏻 Allah ya mata rasuwa_
FOLLOW
VOTE
COMMENTZEELISH💞