*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*38*
UNEDITEDMasu neman auren ta sun zo, an aiwatar da komai kamar yadda al'adar buzaye take, an saka biki sati biyu masu zuwa, sun koma da sha tara na arzik'i da yaba karamcin da aka musu, Sultan murna har fili ya kasa b'oyewa, yana ji tamkar yafi kowa sa'a a duniya.
Fetta idar da sallar la'asar kenan tana nad'e sallaya, kiran Sultan ya shigo, ta d'auka,
"Amarya ta", Tayi murmushi wanda yana jiyo sautin sa ta waya, "Saura sati biyu ki zama mallaki na", Tace "Allah ya nuna mana", "Amin Ya Rabbi, wallahi na k'osa ki zama matata", Tayi dariya wanda bai kai zuciya ba, bata jin farin ciki ko kad'an a ranta game da auren, "Anjima k'arfe shida jirgin mu zai tashi, kizo muyi sallama", "Toh", "Ina jiran ki a lambu", Ta amsa da "Toh" tana kashe wayar."Dalilin da yasa na kira ka ya kamata mu koma gida" Cewar Hajiya, Suraj dake durk'ushe gaban ta yace "Amma Mama bamu gamu shawo kan Fatima ba", "Wane shawo kai, baka da labarin manema auren ta sun zo, sati biyu masu zuwa za'a d'aura mata aure", A matuk'ar razane ya d'ago yana kallon Hajiya, yayin da yaji kalmar ta tamkar saukar aradu, zufa ta shiga karyo masa, idon sa suka kad'a jajir, bakin sa ya shiga kakkarwa ya kasa furta komai,
Tausayin sa ya kama Hajiya, tasan dole zai shiga tashin hankali jin Fetta zata yi aure, amma ya zama dole ya hak'ura, shi ya jawa kansa tak'i sa, "Hak'uri zaka yi, ka k'ara kiyaye gaba", Yaga bakin Hajiya na motsi but sam bai san me tace ba, kunnen sa basa jin komai, k'wak'walwar sa bata d'aukar kowacce magana, tunanin sa ya tsaya cak, Shigowar Su'ad da Feena yasa shi mik'ewa ya fita, ba dan yasan inda yake jefa k'afar sa ba,
Fitowar sa filin gidan yayi daidai da saukar furucin Sultan kunnen sa, "Zan yi kewar ki matuk'a Amarya ta, ina jin kamar kar na tafi nayi ta kallon ki", "Sati biyu ya rage na zama mallakin ka, kayi ta ganina har sai ka gaji", Cewar Fetta wanda da gayya tayi ganin tahowar Suraj,
Kalman ta tamkar saukar ruwan dalma a zuciyar sa, turnik'ik'in zafi take masa, yayin da yake ganin duhu-duhu na mamaye idon sa, kansa na tsananin sarawa kamar zai rabe biyu, jefa k'afafun sa yake ba tare da yana kallon gaban sa ba, taimakon Allah kad'ai ya kawo sa masaukin sa,
"No wallahi ba zan iya jure ganin Fatima da wani ba, ba zan iya ba", Ya fad'a cikin karaji yana dafe zuciyar sa dake barazanar tarwatsewa, kalaman Fetta ga Sultan na masa yawo a k'wakw'alwa, zafin zuciyar sa na k'aruwa, tuni jikin sa ya d'auki kyarma, cikin mintuna da suka gaza goma zazzab'i mai zafi ya rufe sa, duhu na mamaye idon sa duk da hasken fitilan da ya gauraye d'akin.
Hajiya tun fitar sa hankalin ta ya kasa kwanciya da yanayin sa, yayin da zuciyar ta ke hasassa mata taje ta duba sa, Ta kalli Su'ad dake gefenta tace "Kinsan masaukin Suraj", Ta gyad'a kai sama tace "Eh", "Muje ki rakani", Ta amsa da "Toh" ta mik'e ba tare da tambayar dalili ba.
Halin da suka gansa ya matuk'ar d'aga musu hankali, kwance yake baya numfashi, Hajiya salati tayi ta sanar da ubangiji, tana kururuwar neman taimako, Su'ad a guje ta koma sashen Azagas ta sanar dasu, babu b'ata lokaci aka nufi asibiti dashi, Hajiya sai faman zirga zirga take bakin k'ofar da aka shiga dashi, ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana addu'o'in da suka zo bakin ta, Su'ad, Feena da Samee na gefe na kuka, Aliya da Malam na tausar su, Azagas na gefe da masu tsaron ta, tana addu'ar samun sauk'in sa, Hajiya ba k'aramin tausayi ta bata ba.
Fetta na masarautar bata san meke faruwa ba, kukan Mimi ya dameta, tayi ta lallashin ta, ta bata nono amma kukan k'aruwa yake, tana tunanin kai ta asibiti, wanda take kyautata zaton wani ciwon ke damun ta,