12

3.5K 271 5
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*12*
*Unedited*

   *Bayan wasu shekaru*

   A cikin shekarun abubuwa da dama sun faru, ciki hadda girman Fetta, Ta zama tsaleliyar budurwa, Kyawun ta ya k'ara fitowa, Ga diri da cikar dukiyar fulani, Da zata samu hutu ba k'aramin kyau fatar ta zata k'ara ba, Shekarar ta 17 tana ajin k'arshe a secondary, Shirin zana Waec suke.

    Mu'azzam tuni ya bayyana soyayyar sa gare ta, Yasha wahala kafin ta amince, Soyayya suke zubawa kamar ba gobe, Duk bayan kwana biyu yake zuwa wurin ta zance, Duka yan gidansu sun san da Fetta, Mahaifiyar sa bata goyon ba, a cewar ta bata da asali, kullum yana k'ok'arin fahimtar da ita da saka mata k'aunar Fetta.

    Suraj tun da aka d'aura auren sa da Bilkisu babu wata alak'a da ta shiga tsakanin su ta aure, Ya rage zuwa Kano sosai, Hajiya Tumba babu yadda bata yi dashi ba, ya rik'a tafiya da Bilkisu, ya kawo mata excuses, Ta kawai k'yale sa ne ba dan ta yarda ba, Bilkisu bata damu ba, arzik'in ta take ci hankalin kwance, babu abunda ta nema ta rasa, Aunty Jummai ma ta shaida yar'ta ta auri Suraj Sa'idu, Taci mai kyau tasha mai kyau.

   Mutane sunyi ta tsegumi Shekara biyar da aure babu haihuwa, Da yawa sun d'auka matsala ta rashin haihuwa, d'ayan su ke d'auke da ita, Wanda sunfi zargin Suraj, a cewar su da Bilkisu ce, da tuni ya k'ara aure.

    Zulaihat kullum tana gidan, watarana ma anan take kwana.

    Mahaifin Bashir bai yarda Dan' sa yayi ciki ba, Haka Karima tayi ta rainon ciki tana shan kyara da hantara wurin iyayenta, Har Allah ya sawwake ta lafiya, Ta haifi yaronta namiji, Da k'yar Kawo Sule ya siya rago aka yanka aka saka mishi suna Aliyu, Ta cigaba da jego, Yanzu Shekarar sa hud'u, ita ke wahalar yi mishi komai da taimakon Hajiya Tumba.

    Tsaye take bakin madubin dake manne jikin bangon d'akin, Powder ta ta shafa a fuska, sai lipstick, Lips d'inta pink ne sai ka rantse ta saka janbaki, Ta yafa mayafin ta, Tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tayi ba.

    Yana zaune a dakalin soron gidan, Sanye yake cikin yadi da ya mishi kyau, Mu'azzam nada kyaun sa daidai gwargwado, shi ba bak'i ba, shi ba fari  ba, Za'a iya kiran sa da chocolate color, Mutum ne shi mai sanyin hali da yawan far'a, Hakan yasa ya k'ara shiga zuciyar Fetta,

   Cikin tafiyar ta mai d'aukar hankali ta shigo da sallama, Fuska d'auke da murmushi ya d'ago ya amsa "Sarauniyar mata barka da zuwa", Tana dariya mai d'auke da kunya ta zauna tace " Ina wuni?", "Lafiya lau mai kyau, kullum k'ara kyau kike, fad'a mun sirrin", Hannu tasa tana rufe fuska, " Sarkin Kunya", Ya fad'a yana jin k'aunarta na sake shigar sa.

   "Bari na kawo maka ruwa", " A'ah zauna abin ki, idan ina buk'ata zance ki kawo mun", Tace "Toh" Tana k'ara gyara zama,

    "Kullum na ganki sai naji na k'osa ayi auren mu", " Yar' k'arama ta dani zanyi aure sai na k'ara girma", Ta fad'a da shagwab'a, Ba k'aramin burge sa shagwab'ar ke yi ba,

"Wai aiko ba zan yarda ba, latecomer yazo yamun k'wace", " Ashe kai ba jarumi bane a fagen soyayya in har kana tunanin wani zai k'wace maka", "Aikuwa ni sadauki ne idan akan soyayya ne, ba zan yarda wani ya k'wace mun sarauniyar mata ba", Dariya tayi tace " Yawwa haka nake son ji"

    Haka suka cigaba da hirar su ta masoya, Da zai wuce ya mik'o mata leda mai d'auke da kwali,

   "K'aramar waya ce na siyan miki, da zamu rik'a waya ko bama tare, zata rage mana kewar juna, akwai sim a ciki", Ajiye mishi tayi kan cinyar shi tace " A'ah Ya Mu'azzam, ka barshi, idan kazo ma yi hirar, ko ka rik'a kirana ta wayar Umma",

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now