34

2.2K 252 18
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*34*
UNEDITED

  Suraj ya k'ara kwana biyu garin Niamey but kwanakin nasa basu k'ara masa komai ba sai damuwa da rashin natsuwa na yadda baya samun wani cigaba daga b'angaren Fetta, sam ta daina yarda su had'u, Ganin haka ya shirya tattarawa ya koma Nigeria, ba dan zuciyarsa ta hak'ura da ita ba, sai dan bashi da wata mafita.

    Fetta tana k'ok'arin yak'i da zuciyarta wurin yakice duk wata damuwa da kawar da tunanin Suraj, ta cigaba da harkokin ta, suna shan shagalin biki, sai dai Sultan da ya matsa mata da kira, a rana sai ya kira ta sau biyar, bata k'in d'aga wayar sa, tana matuk'ar jin nauyin sa, amsa d'aya take bashi a ko da yaushe bata gama shawara ba, wanda k'asan zuciyarta bata jin zata tab'a amincewa dashi.

   K'arfe biyu na ranar laraba Suraj yana cikin garin Kano, bai buk'aci zuwan direbobin sa ba, Taxi ya tara ta kaisa guest house d'in sa, Sallar azahar ya gabatar, ya kwanta kan doguwar kujerar dake falon, kansa na tsananin sara masa, Ruri wayarsa ta soma yaja tsaki yana danna reject ba tare da ya duba mai kiran ba,

   "Umma kashe mun waya yayi", Bilkisu ta fad'a cikin tsananin b'acin rai, A fusace Aunty Jummai tace "K'aryar iskanci yake wallahi, bar ni dashi kawai", Bilkisu ta jinjina kai tana mik'ewa ganin kiran Zulaihat, bata so Aunty Jummai taji wayar da zasu yi.

   "Sweety kinyi kasuwa fah" Cewar Zulaihat, "Haba dai", "Wallahi wata Hajiya ce mai dollars taga hoton ki ta rud'e", Cike da farin ciki Bilkisu tace "Kice na garzayo", "Yanzu kuwa", "Gani nan zuwa" Ta kashe wayar, jiki na rawa ta hau shiri.

   
     Su'ad tana zaune tsakar gida sai faman hamma take na yunwa, yau kwana biyu bata saka komai a cikinta ba sai ruwa da garin kwaki, Adnan tun ranar da ya sanar da ita shi waye, bata sake ganin shi ba, Hawaye ke zirara kan kumatun ta, Murya a raunane tace "Ya Rabbi ka yafe mun zunubai na, Allah na tuba", Cikinta yayi k'ugin yunwa, "Ashe haka talakawa suke ji, ashe haka rayuwar talauci take", Ta fad'a nadamar  wulak'anta talaka da ta rik'a yi na dabaibaye ta, Fetta tazo mata a rai, tana tuna irin cin kashin da suka rik'a mata, tana sake nadama.

 
    "Fetta ba zaki k'ara mana kwana biyu ba", Cewar Amra, Fetta dake had'a kayanta a akwati tace "Ai zan dawo, akwai abunda zanyi a Agadez ne", k'asan zuciyarta bata jin zata dawo nan kusa, tana son gujewa Sultan, "Shikenan idan ma baki dawo ba, mu zamu zo", Tayi murmushi tace "Toh Shikenan", Shigowar Mummy ya katse musu hira da murmushi d'auke a fuskar ta tace "Jirgin ku ya kusa tashi, ina fatan kin gama shiryawa", Ta gyad'a kai sama tace "Eh", "Ban san me muka miki ba, sam bakya son zama niamey", Tayi murmushi tace "Ba haka bane Mummy", "Ba wani nan", Tayi dariya tana mik'ewa, Masu aiki suka shigo suka fita da kayan ta.

     Sanah tana jin saukar motar da ta d'auka su Fetta daga airport, ta fito a guje, kai kace ta shekara bata gansu ba, Ta k'ank'ame Fetta tana karb'ar Mimi, "Tumuqqartin nayi kewar ku sosai", "Muma munyi naki Sanah" Ta fad'a d'auke da murmushi, Suka shiga ciki.

  "Lale marhaban sannun ku da zuwa" Cewar Azagas fuska d'auke da far'a, "Tanti ina wuni?", Lafiya lau, ya hanya? Ya mutanen yamai?", "Alhamdulillah", "Mik'o min kishiyata na ganta, kwana biyu ban lak'aci hancin ta ba", Suka yi dariya,

  Bayan sun natsa, Azagas tace "K'anin mijin ki yazo, ina fatan ya same ki a can", "Eh mun had'u" Ta fad'a a dak'ile tana mik'ewa, "Zan je nayi sallah" Tayi hanyar fita falon, sam bata son zancen, Azagas tabi bayanta da kallo, cike da mamakin ta, "Ko shakka babu akwai abunda take b'oyewa" Ta fad'a a ranta.

   Shigar ta d'akin yayi daidai da shigowar kiran Sultan wayar ta, ta d'an ja tsaki kafin ta d'auka, Takurar sa ta soma damun ta,

"Gimbiyar mata nayi fushi, kin tafi ba sallama", Ta nisa tace "Tuba nake, nima tafiyar tazo mun a bazata", "Shikenan bakya laifi ai", Tace "Uhmm", "Ya gajiyar hanya?", "Alhamdulillah", "Bara na barki ki huta koh, sai anjima", "Ok" Ta fad'a tana ajiye wayar tare da sauke numfashi.

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now