*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf*Haske writers Association*
*05*
*Unedited*Gidan marayun sa ya nufa, ya kai taimako kamar yadda ya saba, Ya duba lafiyar yaran tare da tambayar matsalolin su, Yara da manya a gidan marayun suna matuk'ar son sa, Har su suke yazo, Dan sun san duk ranar da yazo zasu samu sababbin kaya kuma suci dad'i, Kaji yake kawowa masu yawa yace a soya musu suci.
Ma'aikatan wurin har bakin motocin sa suka raka sa, Suna amsa addu'a da fatan alkhairi.
Gida ya umarce su da suna nufa, Motocin sa na shiga, Motar Yaya Sule ta biyo baya, Fitowa yayi cikin takun sa da kamar baya son taka k'asa, Yaga Sule yayi kamar bai gan sa ba,
"Ahh Suraj ne, sannu da dawowa", Juyowa yayi yace " Ina wuni?" Ba tare da ya duk'a ba, "Lafiya lau, ya ayyuka?", Ya fad'a yana washe baki, " Alhamdulillah", Ya amsa ya shige sashen shi, Bai nufi cikin gida ba yasan can Kawo sule za shi, baya son wata doguwar magana ta had'a su.
Babu kowa a falon ya zauna kan kujera, Yana raba idona "Arzik'i kashi, Allah ya bamu mu tattaka, dole na had'a auren Aysha da Suraj ko ma samu rabon mu", Yayi maganar a fili, Safeena ce ta shigo falon, dawowarta daga makaranta kenan, Ta gaishe sa, Ya amsa tare da cewa " Ki fad'awa Hajiya nazo", Ta amsa da "Toh", A zuciyar ta tace " Wasu dai basu san kunya ba, ko kunyar zuwa gidan nan baya ji, bayan irin rashin mutunci da ya rik'a shuka mana", Taja tsaki ba tare da yaji ta ba.
"Mama ga wancan mutumin nan yazo", Cewar Su'ad tana yatsina baki, " Wa kenan?", "Kawo Sule mana", " Shi kike cewa wancan mutumin, meyasa baki da kunya ne Su'ad, k'anin mahaifin ki ne fah", "Toh ai ba....", " Kar na sake naji bakin ki a wurin nan, fita ki bani wuri", Ta fita ta gunguni, da mamakin sanyin halin mahaifiyar su, banda tana hana su wallahi ko ruwan gidan nan, kawo Sule da yaran shi bara su sha ba, kai duk ma wani dangin mahaifin su, Hajiya Tumba duk abunda suka aikata gare ta bata k'ullace su ba, kuma ba zata tab'a zumuncin dake tsakanin su da yaran ta ya lalace ba, ko dan Mahaifin su har ya rasu yana son yan' uwan sa, bai tab'a k'ullatar su ba.
Hajiya Tumba gyalenta ta yafa ta sauko falon k'asa, Da sakin fuska tace "Sannu da zuwa Yaya Sule", " Hajiya ina wuni?, Ya hidimomi?", "Alhamdulillah"
Masu aiki ta unarta suka kawo mishi ruwa da lemo, bayan yasha ya natsa, Yace "Uhmm dama maganar yaran nan", " Wane yara kenan?", "Suraj yanzu shekarar shi 27 ya kamata ace ya fara tunanin ajiye iyali, ya mallaki komai aure kad'ai ya rage masa", Hajiya tayi smiling tace " Nima na fara tunanin haka, kuma ina da niyyar yi mishi magana", "Toh Mashaa Allahu, dan aure shine cikar kamalar mutum", " Hakane amma a yadda na lura dashi, babu soyayya tsarin sa, ban tab'a ji ya kawo mun zancen wata ba"
Yar dariya yayi yace "Banda abun ki Hajiya, ga yan mata a gida ai sai a zab'i d'aya a bashi", " Suwa kenan?", "Kamar dai ba bahaushiya ba, ko Aysha aka had'a shi da ita, ai an k'ara k'arfin zumunci", Tasan za'a rina tunda yazo mata da zancen auren Suraj,
" Yaya Sule yaran yanzu, ba'a musu dole, tunda bashi ya gani yana so ba, ko ita ta gani tace tana so", "Babu maganar dole, yan'uwa ne, jini d'aya suke ba yadda za'a yi suk'i juna, ki kira Suraj ki sanar dashi, ni da kaina zan fad'awa Aysha, sai su fara ganin juna", " Shikenan, Allah ya zab'a mana mafi alkhairi", "Auren nasu shine alkhairi ma", Tayi murmushin takaici na sanin ba dan Allah da zumunci yake so ayi auren nan ba, sai dai abun duniya, Nuna rashin amincewar ga auren nan, zai iya haifar da matsala babba, ya zama dole ta nuna goyon baya, Fatan ta idan ba alkhairi bane Allah kada ya had'a kansu.
Cike da farin ciki Kawo Sule ya koma gida, ya sanar da matar sa, bakin ta kasa rufowa yayi dan itama lashe money ce, Ya kira Aysha yace ta dawo gida, Rai bai so ba ta koma, Tana da masifar son rayuwar k'arya, sam bata son zaman gidan su, can ba wani dad'i suke ci ba, gidan Hajiya Tumba kuwa sai abunda suka zab'a, Ta d'auke su tamkar yaran ta komai yi musu take.
Zancen da mahaifin ta ya mata, ya wanke zuciyar ta, Ta dinga tsalle a d'akin ta, zata auri Suraj, Ta shiga cikin sahun manya, ta kece raini, ta gurza naira yadda take so, Zama mata a wurin SURAJ SA'IDU SS ba k'aramin abu bane.
Labarun NTA suke kallo, Fetta ta lullub'e cikin hijabi sanyi take ji, Garin yayi sanyi sakamakon ruwan sama da akayi,
Suraj aka hasko yana mik'a taimako ga gajiyayyu a wurin wani taro da akayi na taimaka mara sa k'arfi, "Kamar mutumin kirki, yana nunawa duniya shi na kirki ne amma mugu ne", Malam da Aliya suka maido kallon su gare ta, Aliya tace " Fetta kinsan shine?", "Shine ya mare ni", Malam yace " Kai Fetta, wallahi na d'auka wani mugun abun yake", "Suraj ne d'an gidan Hajiya Tumba, akwai sa da zafin rai amma yana da tausayi da taimako",
Tab'e baki tayi, a ranta sam bata yarda yana da tausayi ba, mai tausayi ba zai mata marin da ya mata ba.
Sai da ya tabbatar Kawo Sule ya bar gidan, Ya shigo wurin Mahaifiyar sa, Bayan sun gaisa.
Cikin tattausan lafazi tace " Suraj girma kake, kana k'ara manyan ta ya kamata ace ka fara tunanin ajiye iyali", Far'ar dake kan fuskar sa ta d'auke, "Mama Dan Allah ki daina zancen aure yanzu", " Idan ban maka yanzu ba, yaushe zan ma Suraj, cikar kamalar da' namiji aure", "Kiyi hak'uri Mama, amma babu yarinyar da nake so", " Ga yan' mata da yawa na son ka, ka duba d'aya daga cikin su ", " Ban yarda da tarbiyar su, da son da suke mun, nasan akan dukiyata ne, ina son na samu yarinyar da zata soni tsakani da Allah", "Kana da gaskiya, amma me zai hana ka gwada Aysha yar' gidan Yaya Sule"
A razane ya d'ago yace "Mama da kanki, Aysha fah Yar' gidan Kawo Sule", Ta d'aga mishi kai tace " Eh", Zufa ce ta fara karyo masa, ya kasa yarda ace mahaifiyar sa ce ke cewa ya auri Yar' kawo Sule, bayan tafi Iowa sanin halin su, Ta rik'e hannun shi tace "Ka fahimce ni My son, Kawo Sule yazo mun da buk'atar, idan na nuna rashin yarda ta hakan zai iya jawo matsala, ina so ka nuna yardar ka daga baya sai mu san abun yi", " Na yarda dake Mamana nasan ba zaki tab'a cuta ta ba", "Allah ya maka albarka", Ya amsa da " Amin"
Yana jin b'acin ran na barin sa, babu aure a tsarin rayuwar sa, balle auren Yar' kawo Sule abunda ba zai tab'a yiyuwa bane.
_Zaku dinga ganin Post Kadan, kuma ba kullum ba, Am writing exams_
*Follow*
*Vote*
*Like**TEAM FETTA*💕