*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*26*
*Unedited**Nagode k'warai da addu'o'in ku*
_Murtala Muhammad International Airport_
Jirgin su na landing, Driver sa na garin ya iso, ba b'ata lokaci ya karb'i luggage d'insa ya saka a mota, Shima ya shiga, Driver yaja zuwa Victoria Island (Unguwar da Suraj yake).
Rigar sama ya cire, ya zauna yana huce gajiya kamar wanda yayi tafiyar mota, Cikinsa yayi kuka alamar yunwa, hanzari bai barsa yayi breakfast ba, Yaron sa ya kira yace yayi masa order chips da egg sauce.
In less than 30mins ya kawo, A plate ya zuba, Ya fara ci, sam bai masa dad'i ba, Wayarsa ya d'auka ya kira Kamal(Yaron sa)
"Ina ka siyo chips d'in nan?", " Wurin da aka saba siyowa", "K'arya kake, it taste different", " Wallahi Sir a can na siyo", Ya kashe wayar yana cewa sun b'ata abincin su, Haka ya cusa ba dan yaji dad'in shi ba sai dan yunwa, (Girkin Fetta ya fara tasiri, Mata a zage wurin iya girki, yana da matuk'ar muhimmanci a zamantakewa ta aure, yana k'ara miki k'ima a wurin miji, da hana miji cin abincin waje, yaji idan ba girkin ki ba, ba zai iya cin na kowa ba sai dole)
Fetta tattara kud'in tayi da takardar ta bud'e drawer ta saka, A ciki taga wani d'an k'aramin littafi, Hakanan taji tana son ganin rubutun dake ciki, "Idan sirrin sa ne da baya so kowa ya gani fah", Zuciyarta tace mata, Ta mayar ta ajiye, ta rufe drawer, Ta nufi falo ta kunna kallo.
"Aikin Malam yaci, Ya Suraj ya tafi lagos ya bar Fetta", Bilkisu ta fad'a cike da farin ciki, Aunty Jummai ta washe baki tace "Dama Aminiya tace aikin sa tamkar yankan wuk'a yake", " Na yarda", "Yanzu Hajiya zamu yi k'ok'arin cusa ma k'iyayyar ta", " Taya?", "Kawo kunnen ki", Aunty Jummai ta rad'a mata, Sukayi dariya suka tab'e kamar k'awaye.
Hajiya tace Su'ad taje ta taya Fetta kwana, Rai bai so ba ta shigo sashen.
Fetta bacci take ji but tsoro ya hana, ba zata iya kwana ita kad'ai, Ganin Su'ad taji dad'i, bata tanka ta ba, Ta wuce cikin d'aki, Ta hau gado ta fara waya, tana kashe murya, daga ji da saurayinta take.
Fetta bata bi ta kanta ba, Tayi shimfid'a a k'asa, cikin minti biyar bacci ya d'auke ta.
Da asuba da tashi, ta tashi Su'ad, tsaki ta mata ta k'ara gyara kwanciya, Sallah tayi ta zauna tana karatun Qur'ani har gari ya waye, Tayi wanka ta shirya, ta gyara gidan ta saka turaren wuta,
Tea da bread tasha, dama ita ba gwanar cin bacci ba, saboda Suraj take girki, har lokacin Su'ad bata tashi ba.
" Itama bacci ne da ita, kamar yayanta", Fetta ta fad'a, Wata zuciyar tace mata "Me yafi ransu basu da wata damuwa",
Kiran Yasmeen ya katse mata tunani, Tayi receiving, Da sallama, ta amsa tana fad'in " Nayi fushi, kin nuna dai bakya son zumuncin dani", "Ba haka bane", " Hakane mana, kiyi aure ba sanarwa, haba Fetta", "Aure ne yazo a bazata", " Na miki uzuri, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba", "Toh yaushe zaki zo?" Ta fad'a ba tare da tace Amin ba, "Gobe In Shaa Allah, ki turo mun address", " OK", Sukayi sallama ta kashe.
Suraj duk abincin da yaci baya jin dad'in sa, Ya rasa dalili, Yaronsa restaurant kusan 4 yaje yayi masa order abinci, but duka yace babu dad'i, Sai faman masifa yake mishi, Mota ya shiga da kanshi, yaje best restaurant na garin, in dai abincin ne babu wanda ya kaisu iyawa, Manyan mutum garin da bak'i a wurin su suke ci,
Yayi order fried rice da chicken, Spoon d'aya yaci, yaji ba dad'i, Tashi yayi ya bar abincin cike da takaici, Yoghurt ya siya yasha, Ya nufi company sa na siyar da motoci, Cike da tunanin Why kowane abinci baya jin dad'in sa, which is unusual, ko asibiti zai je a duba sa, Maybe daga laifin bakin sa ne.
Su'ad ta taso yana mik'a, Dining area ta nufa, taga wayam babu breakfast,
"Ina breakfast?", Ta tambaya tana bin Fetta da wani shegen kallo, " Kin bani ajiya ne, ki shiga kitchen ki dafa", "Baki isa kizo gidanmu ki raina mana hankali ba", " Yadda kike da iko da gidan, haka nake dashi, gidan Mijina ne", "Wallahi bada jimawa ba zaki bar gidan nan", Ta fad'a a k'ufule ta fice.
Fad'awa tayi jikin Hajiya ta fashe da kuka, Ta d'ago ta tana tambaya lafiya, " Matar Ya Suraj ce, ta hana ni breakfast, na shiga kitchen zan girka wai na fita, naje nayi aure ba yawon banza ba", Hajiya tasan k'arya Su'ad take, ta yarda da hankalin Fetta, bara ta tab'a yin haka ba,
"Ke Su'ad kiji tsoron Allah", " Wallahi Ma.....", "Rufe mun baki, tashi ki bani wuri", Ta mik'e rai a b'ace, taso ta had'a mata gwarama, ta rasa me tama Hajiya bata ganin laifinta,
Fetta wunin ranar ruwan tea ne a cikin ta, sai wainar fulawa da tayi taci, Da yamma Su'ad da k'awayenta suka cika falon, Fetta d'aki ta shige ta saka key, Ba irin knocking da basu yi ba, zasu yi fitsari tak'i bud'ewa, idan fitsarin gaske ne suje sashen su,
" Kun sakar ma matar nan da yawa fah", Cewar d'aya daga cikin k'awayen su, "Zamuyi maganin ta kafin Ya Suraj ya dawo", Suka yi rashin mutuncin su, da yada habaici, Suka fice,
Fetta na d'aki bata fito ba, balle ta nuna tasan da ita suke.
Suraj ya dawo gida a gajiye, yunwar cikin sa ta ishe shi, ba abunda yaji yana buk'ata kamar tausa, Kamal ya kira yace ya nemo masa masu tausa home service, Ya amsa da toh cike da ladabi,
Maza biyu ya d'auko masu tausa, Shago ne dasu mai so yaje a masa ko suzo har gida su ma, ka biya.
Suraj ya mik'e k'afa, Emmanuel na d'aura hannu, yaji kamar katako, Da sauri ya bud'e ido yace " Don't tell me da wannan hannun kake wa mutane tausa", Emmanuel yace "Sir ai duk garin nan, ba wanda ya kaimu iya massage", " You are not serious, you zo kayi", Ya fad'a yana nuna d'ayan,
Cike da nuna k'warewa ya d'aura hannun sa ya fara, Suraj ji yayi tamkar ana matsa mishi da dutse, " Karya ni zaka yi" Ya fad'a a tsawace, Da sauri ya janye hannun shi yace "Sorry Sir", " Kamal fitar mun dasu, hannun su kamar katako, jikina bai saba da wahala ba"
Emmanuel da Jacob sun nunawa Kamal b'acin ransu, Sunce ya kira su ne dan a wulak'anta su, Lagos kowa yasan sun k'ware wurin massage, but dan wulak'anci yace hand d'insu kamar katako, Kamal hak'uri ya basu, Suka tafi rai a b'ace,
"Kaje ka d'auko mun wanda hannun su duk kanta, Allah yasa basu ji mun ciwo ba", Ya fad'a yana dudduba jikinsa, " Zo kamun", Ya umarci Kamal, Shima dai cewa yayi hannun nasa ya cika tauri,
Kamal ya fita rai ba dad'i, Dawowar nan ya kasa gane kan ogan nasa, Ga dukkan alamu akwai abunda ke damun sa.
Fetta zaman ita kad'ai ya ishe ta, Ta lek'a sashen Hajiya, A falon k'asa ta tarar da ita, tana waya,
"Ka ganta yar' halak ana maganar ta", Cewar Hajiya, zancen ya dawo ya d'auki Fetta take mishi,
" K'araso ga mijin ki", Ji yayi kamar ya kashe wayar, sam baya son jin muryarta, Da yasan Hajiya zata mishi maganarta da bai kira ba, "Meyasa na shigo?", Fetta ta tambayi kanta, tana dana sanin shigowa da jin kamar ta koma,
Hajiya ta mik'a mata wayar, Ta kanga a kunne tare da yin sallama, Ya amsa, " Ya Ayyuka?", "Kina kewata ko, kinji dad'i kinji sweet voice d'ina", Mamaki ya hana mata magana, banda tana gaban Hajiya ta da fad'a masa maganar da zata dad'e tana ci masa rai, " Duk jin muryar tawa ce ya kashe miki jiki", Mik'awa Hajiya wayar tayi, idan tana cigaba da jin talks d'insa, zata iya yab'a masa maganar ba tare da ta sani ba.
Sallama suka yi da Hajiya, Ya kashe wayar, Ya kwanta kan kujera, Yana lumshe ido, "Sorry Mama, zan fara karya umarnin ki, ba zan tab'a dawowa kano ba, sai bararojin da kika aura mun ta fita rayuwata",
_Kuyi managing wannan_
*Follow*
*Vote*
*Comment**ZEELISH*💕