02

5.4K 418 4
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

     *Haske writers Association*

   *Wannan littafin gaba d'aya sadaukarwa ne ga Zainab Mohammed Yusuf*(A friend  worth dying for❤)

*02*

   Ta galabaita sosai, jiri ya d'ibeta ta fad'i k'asa, Tana haki, Kuka take sosai tana tuna mahaifin ta, "Allah ya saka maka Addani, Allah ya jik'an ka", Shine abunda take fad'a.

    Tana kwance a wurin har aka fara kiraye kirayen Sallar asuba, Mutane suka fara fitowa sallah.

    Karon da yaji yayi da abu, yasa shi haska fitila saitin wurin, Ja yayi baya a tsorace, ganin mutum kwance, Hannu tasa tana kare hasken fitila da ya dalle mata ido, " Ke yarinya daga ina?", Kukan ta ne ya tsananta, Tausayin ta ya kama shi, Ya duk'a, Ya d'ago ta, "Tashi ki fad'a mun ina ne gidan ku", Cikin shesshek'ar kuka ta sanar dashi abunda ya faru a daren.

   Ya jinjina al'amarin, a ran shi yace " Wasu mutane basu da imani", Ya rik'o hannun ta yace "Tashi muje gidana", Ba musu ta mik'e tabi bayan shi,

    K'ofa ce babu gate, gida ne madaidaici mai d'akuna biyu, da falo d'aya, Daga gani ba mai kudi bane, Matar shi dake tsakar gida tana alwala, Tace " Malam ina ka samo yarinya", Ya zayyane mata abunda Yarinyar ta sanar dashi, Tausayin ta taji a ranta, Ta rik'o ta tace "Zo yarinya ya sunanki?", " Fetta", "Allah Sarki Fetta, Allah ya jik'an mahaifin ki, ya tona asirin wanda suka kashe shi"

    Ta amsa da "Amin", Tana sharar k'walla, " Ki d'auke mu tamkar iyayen ki kinji", Ta d'aga kai sama, Ya koma masallaci, Ya bar matar shi taja ta ciki.

   Gidan Alhaji Adamu(wanda anan mahaifin Fetta ke gadi), Ya cika da mutane, Ana ta fito da gawarwaki ciki hadda ta Mahaifin ta, Mutum hud'u suka kashe a gidan, (Alhaji, matar sa, babban d'an shi), Sauran yaran gida da yan'uwa nata kuka, duk sun fita hayyacin su, Yan sanda sunzo sunyi binciken su, Sun tafi.

     Fetta tagumi tayi tana tuna irin rayuwar da suka yi da mahaifin ta, ba zata tab'a yafewa wad'annan mutane da suka yi sanadiyyar raba ta da farin cikin ta, Shi kad'ai take dashi a duniya, Sark'ar da ya saka mata shekaru biyar da suka wuce, Ta jawo ta sumbata, Matar ce ta shigo, Tace "Ki daina kuka kinji, idan bakya so a mishi azaba, addu'a zaki mishi", Tana jin an ambaci azaba, tayi saurin share hawayen ta.

     Malam bala shine mutumin da ya tsinci Fetta, Nama yake siyarwa, Matar sa d'aya Aliya, gidan wasu masu kud'i nan kusa dasu take aiki, ana biyan ta duk wata, kuma tana d'inki, da haka suka rufawa juna asiri, Yaransu biyu Hajar da Aliyu, yaran k'anana ne.

        *Bayan kwana biyu*

   Fetta ta saki jiki dasu, But duk dare tazo kwanciya sai tayi kuka na rashin mahaifin ta, Malam Bala da Aliya sun d'auke ta tamkar yar' su, Har atamfofi roba ya siyo Aliya ta d'inka mata.

    Tana tsananin son yaran, Tana taya Aliya rainon Aliyu, yaron d'an wata bakwai.

      Kwance take d'aki shiru, tana tsananin kewar mahaifin ta, watarana sai taga kamar a mafarki bai rasu ba, Aliya ta lek'o tace " Fetta tashi ki rakani gidan Hajiya Tumba, yau akwai aiki sosai, ki rik'e mun Alee, bana son ya hana ni aiki", Tace "Toh" tana mik'ewa.

   D'an kwalin kayanta, Ta yafa ta d'auki Ali, Aliya na gaba tana bin ta a baya har suka isa gidan.

   Makeken gida ne, tun daga gate abun kallo ne, Yan' sanda dake tsaye bakin gate, Aliya ta gaisa dasu, Fetta ma ta gaishe su suka amsa, D'aya ya bud'e musu k'ofa suka shiga.

     Fetta sakin baki tayi tana kallon girma da had'uwar harabar gidan, tsaf zaka b'ace a cikin gidan, Saboda girman shi,  Ga motoci had'add'u guda biyar a fake, Sai faman raba ido take har Aliya tayi gaba ta bar ta, Da sauri tabi bayan ta.

      Ta k'ofar baya suka shiga wanda zai sada ka da k'aramin falo, wanda anan Hajiya Tumba ke ganawa da masu aiki, Duk safiya kowacce mai aiki nan take zuwa ta gaishe ta, "Aljannar duniya", Cewar Fetti, dan falon ba k'aramin tsaruwa yayi ba,Sai kalle-kalle take.

    A k'asan carpet suka zauna, kamar yadda sauran masu aiki suka zauna, Suna jiran fitowar ta, ta basu umarnin abincin da zasu girka.

    Da sallama ta shigo falon, Mace ce wacce kallo d'aya zaka mata kasan hutu ya zauna a jikin ta, Sanye take da wani tsadadden material, wanda ko ba'a fad'a maka kud'in sa ba, Kasan mai tsada ne, Tasha sark'a da yan' kunni na gwal, da zobuna, Ta zauna a kujera.

Duka masu aikin suka shiga gaishe ta, Tana amsawa da sakin fuska, Mace ce mai sanyin hali, Cikin ladabi Fetta ta gaishe ta, Ta amsa tare da tambayar " Wacece?", "Ya'ta ce", Aliya ta fad'a, Bata gamsu yar'ta bace, dan ta tab'a gaya mata yaran ta biyu, kuma bata ga suna kama, Yarinyar da an ganta an ga buzuwa, Taji kawai ta kwanta mata a rai.

    Ta kawar da tunanin ta hanyar cewa " Yau Suraj zai zo, ina so ku girka duk abincin da kuka san yana so, Kuyi mishi snacks, Kuyi drinks kamar kala biyar", Suka amsa da "toh", Duk ranar da Suraj zai zo to fa, basu da sukuni, Aiki ne sai sun sha shi, Yana iya zuwa yace abincin ma, Bai mishi ba.

    Fetta a ranta tace " Dan' gata ne", Gefe ta koma tana yiwa Ali wasa, Su Aliya nata faman aiki.

     Wuraren azahar suka gama komai, Suka jere a dining table na babban falon gidan, Hajiya Tumba tasa suka k'ara gyara gidan, aka saka turaren wuta.

     "Wash na gaji wallahi, bayana har ya rik'e", Cewar Asabe(d'aya daga cikin masu aikin), Rashida tace " Ke kika gaji ko ni, shiyasa bana son zuwan sa, idan zai zo mutum ba zai huta ba, baka k'ara samun wani hutu sai ya koma", "Hmm ke dai bari, ga shegen jin kai kamar dan' Sarki", " Ni zan iya k'irga sau nawa na gan shi", "Ai gara kar mutum ya gansa, dan kallon wulak'anci da k'ask'anci yake wa mutane, laifi kad'an zaka yi yaci mutuncin ka", " Yana tak'ama da kud'i, wannan da dan' Sarki ne da mun shiga uku"

    "Ku dai bakwa gajiya da maganar Suraj", Aliya ta fad'a, " Maman Ali Bawan Allah nan akwai murd'add'an hali", Dariya tayi ta girgiza kai.

  Aliya ta gama ayyukan ta, Tace Fetta ta tashi su tafi, Ta karb'i Ali ta goya shi, Tana gaba tana biye da ita a baya, Aliya Allah ya mata saurin tafiya, Fetta cikin natsuwa take tafiya kamar bata son taka k'asa, wanda idan ka ganta zaka d'auka yanga ce.

      Motoci uku ne suka shigo cikin layin a jere, masu azabar kyau, sun fi na cikin gidan had'uwa, Fetta ta shagala wurin kallon su, Har dan' kwalin ta na fad'i, Yabi iska, Ta juyo baya zata kamo, Motocin suka zo gab da ita, na gaban na mata horn, Rikicewa tayi, tama rasa ina zata yi, Wani wawan burki yaja, Motar bayan shi ta bege shi.

     Jingine yake jikin kujerar mota, Ya lumshe ido, Gaba yaji yayi, Yayi kaura da kujera, A fusace ya d'ago, Ransa ya matuk'ar b'aci, A tsawace yace "What d hell?", Driver a rud'e yace " Ranka ya dad'e ba laifi na ba ne, Modi ne yaja burki"

   Bud'e murfin motar yayi, Ya fito cikin takun sa na k'asaita, Farar shadda ce tsadadda a jikin sa, babu hula a kansa gashin sa bak'i wulik yana shek'i kamar na mace, Fari ne tass, Jikin sa zai nuna maka Dan' Hutu ne kuma naira ta zauna, Namiji ne da ya amsa sunan sa namiji, Mai kyawun fuska da na halitta.

    Modi na ganin sa yayi saurin kai k'asa yasan halin Maigidan nasu da zafin rai, Yace "Ranka ya dad'e tuba nake, ba laifi na ba ne, wannan yarinyar ce tazo ta gifta", Ya nuna Fetta daga rakub'e gefe a tsorace, Hannu ya d'aga ya zuba mata lafiyayyan mari, Kunci ta rik'e ta tsala ihu, "Shegun yara mara sa tarbiya, kuzo kuna tsallaka hanya bayan kun ga mota, salon ku ja ma mutane masifa, dama yaran buzaye so kawai suke mai kud'i ya d'an buge su, su mak'ale mishi ya biya su, saboda tsabar kwad'ayi ku salwantar da rayuwar ku", Yana fad'ar haka ya juya ya koma mota, Motocin shi suka d'aga, tare da bad'a mata k'ura.

   Duk da kasancewar ta mai k'ananun shekaru, maganganun sa sun matuk'ar k'una mata rai, Tun da tazo duniya ba'a tab'a wulak'anta ta irin yau ba, babu mahalukin da ya tab'a marin ta, Shine farko, tsanar shi taji sosai a ran ta,

" Wayyo Allah Addani, meyasa ka tafi ka barni, ka dawo kaine kad'ai gatana"

*Follow*
*Vote*
*Like*

*TEAM FETTA*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now