*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*17*
Kiran sallar asuba da ya zama jikin Fetta, Duk kiran asuba a kunnen ta, Yau ma hakan ce ta kasance, Kiran farko ta tashi da sunan Allah a baki, Mik'a tayi ta tashi, Ta shiga toilet tayi alwala, Ta fito ta gabatar da raka'atanil fajr, ta sallame tayi sallah.
Zama tayi tana karanta surorin da ta haddace, Cikin kira'ar ta mai dad'i, Bata d'aga murya ba gudun kada ta tashi Hajiya tana buk'atar hutu.
Kamar a mafarki Hajiya taji karatun Qur'ani mai dad'i, Bud'e ido tayi ta sauke su kan Fetta, idon ta a lumshe yake, tana zuba karatu, Hajiya a ranta tace "Allah ya bata baiwa, ina ma su Su'ad ne ke karatu haka, sun k'i maida hankali ba yadda bata yi dasu ba, har yanzu basu yi sauka ba"
Tarin da ya taso mata, Ta dakata da karatun tare da bud'e ido, "Sannu", Hajiya ta fad'a, Ta kai dubanta gare ta, " Laah an bud'e miki idon, yanzu kina gani", Ta fad'a with full excitement, Hajiya tabi ta da kallo tana murmushi yadda take murna ko su Su'ad basu nuna farin cikin su haka ba,
"Allah ya k'ara miki lafiya", " Amin Amin", Ta mik'e ta shiga toilet.
Wayarta ta d'auki ruri, Murmushi tayi ganin masoyin ta ne mai kiran, "Amincin Allah ya tabbata a gare ka", " Tare da ke, kin tashi lafiya?", "Lafiya lau, ya gida da ayyuka?", " Alhamdulillah, sai dai kewar ki da ta dame ni", "Nima haka", " Anjima zan zo na ganki, dan gaskiya ba zan iya jure har ki dawo ba", Tana murmushi tace "Sai kazo", " Zuwa la'asar idan nazo zan kira ki", Tace "Toh", " I love you ", " Same", Ya mata blowing kiss, Tayi saurin kashe wayar tana sunne kai a pillow tamkar yana gabanta.
"Ina jin Fetta tamkar jini na, kwana biyu da bata gidan nan, sai ina jin duk ba dad'i", Aliya ta fad'a tana shanya kayan da ta wanke a igiya, Malam yace " Wallahi nima haka, Yarinya ce mai tsantar hankali da tarbiya", "Yau zan je na ganta, naga lafiyar ta", " Allah ya kaimu, ni zan wuce kasuwa", Ya fad'a yana saka takalmi, "A dawo lafiya", " Allah yasa"
Gari ya waye, hasken rana ya b'ullo, Su Feena suka zo asibitin da karin kumallo, Ko kallo Fetta bata ishe su ba, Itama ta d'auke kai kamar bata gan su ba,
"Wai nikam yarinyar nan bata iya gaisuwa bane", Cewar Feena (Zata ba Fetta shekara 3-4), Su'ad tace " Kema kya tambaya", "Sai mutum ya shigo wuri ta d'auke kai, kamar wata shegiya", " Sister kinsan wanda ba kowa ba yafi komai jin kan sa"
Fetta yi tayi tamkar bata san da ita suke ba, Tana game a wayarta hankali kwance, Wanda hakan ba k'aramin k'ular dasu yayi ba, Feena a fusace tace "Ke!", Ko gezau bata yi ba balle ta nuna wata alama na tasan da ita take, Ta tsani ace mata Ke, bata amsa kalmar ke,
" Fetta kike ko uban wa dake nake magana", Ta d'ago "Au wai dani kike ai KE naji kince", Tayi maganar hankali kwance, Rai a b'ace zata yi magana Hajiya ta fito daga toilet, Tayi shiru.
Yau Hajiya da kanta taci abinci lafiya ta samu, Su'ad ko Feena da sun had'a ido da Fetta suke watsa mata harara, Ta d'auke kai daga sabgar su tana nata,
Ana azahar suka ce zasu je gidan k'awar su anyi kidnapping baban ta,
" Al'amarin kidnapping d'in nan sai addu'a, Gwamnati ya kamata ta d'auki mataki, Allah ya k'ara tsaremu shi kuma Allah ya bayyana shi", Suka amsa da "Amin", Suka fice.
" Yau Suraj bai zo ba, na kira wayoyin sa a kashe, Allah yasa lafiya", "Maybe wani ayyukan ya tare sa, anjima zaki gan shi", " Allah yasa", A zuciyar ta tace "Ba ameen ba, Allah yasa ma kada yazo asibitin kwata kwata",