35

2.1K 397 27
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*35*
UNEDITED

Hannun Munir yaji saman kafad'ar sa yana fad'in "Be strong Suraj", Kansa ya d'aga a raunane, "Ka tashi kaje ka sanar da ita, zaka rage wani nauyi a tare da kai", Ya jinjina kai yace "Nagode Munir, hak'ik'a kai aboki ne nagari, da na bi shawarar ka tun farko ban tsinci kaina a wannan yanayi ba", Murmushi Munir yace "Ka d'auki haka bisa k'addara", Yayi nodding kai yana mik'ewa, Ya mishi sallama ya tafi.

   Zuciyar sa cike da zullumi had'i da fargaba ya tura k'ofar d'akin Hajiya, Ta idar da sallar la'asar kenan tana lazimi, Gefenta ya zauna, zuciyar sa na harbawa da tsananin k'arfi, karon farko a rayuwar sa da yaji Mahaifiyar tasa ta masa kwarjini na musamman, Ta idar da lazimin ta kai dubanta gare sa, "Ina wuni?" Ya furta tamkar mai jin tsoron kalmar, "Lafiya lau, har ka dawo?", "Eh", "Toh Madallah",

    Bakinsa yaji ya masa nauyi ya kasa k'ara cewa komai, Hajiya ta lura akwai abunda yake son sanar da ita, Ta nisa tace "Akwai wani abu ne?", "Uhmm d...ama da...ma", Ya fad'a cikin sark'ewar murya, "Dama me? Ka fad'a mana"

    Fargabar sa ke k'aruwa, zuciyar sa na tsananta bugawa, K'ok'arin tattaro kuzari da k'arfafa ma kansa gwiwa yayi yace "Tunda na taso naga irin tsangwama da hantara da muke fuskanta daga dangin Abba, dama yadda ake mana kallon k'ask'anci kasancewar bamu dashi, na k'uduri a raina sai nayi kud'i, dan a ganina kud'in sune komai, su kad'ai mutane ke darajawa, su kad'ai zanyi na zama wani abu a duniya a rik'a mana kallon mutane masu daraja, a lokacin da Abba ya rasu, rayuwa ta k'ara tsananta a garemu, naga irin wahalar da kike sha da k'annena, da wulak'ancin da muka k'ara fuskanta wurin dangin Abba, zuciyata ta k'ara hassasa mun neman kud'i ko ta wacce hanya, dan na d'aga darajar ki na miki dukkan gata, na maye ma k'annena gurbin Mahaifi na musu gata, mutane su fara rab'ar ku kamar kowa, furucin Kawu Sule a lokacin da muka je gidansa ya k'ara tunzara ni,

"A lokacin da na tafi lagos, tashin farko na had'u da wani Alhaji wanda sana'ar motoci yake, ya jawoni jiki, ya d'auke ni aiki kamfanin sa, sai dai albashin da nake samu dubu hamsin a wata, wanda na raina, ina ganin har yaushe zan tara irin kud'in da nake burin mallaka, na soma tunanin wata hanya da zan samu kud'i cikin k'ank'ani lokaci, sam na manta Allah ke azurta bawa a lokacin da yaso, ban kuma mik'a al'amurana da Allah ba, duba da ba wani ilimin addini ne dani, ana haka Ahmad yazo siyan mota, ni na mishi jagora wajan Alhaji, daga haka muka k'ulla alak'a mai k'arfi, har nake sanar dashi burina na son tara d'umbin dukiya, Yayi murmushi yace Akwai hanya mafi sauk'i da zan zama hamshak'in mai kud'in cikin k'ank'anin lokaci sai dai tana da had'ari, nace wacce hanya ce, Yace fashi da makami, na kid'ima a lokacin, amma da ya nuna mun alfanun da zan samu, a take na amince, daga ranar na tsunduma harkar fashi da makami, wanda da sana'ar na zama abunda na zama yau, ki yafe mun Mama, Dan Allah ki yafe mun, na ciyar daku, na tufatar daku ta hanyar haram" Ya k'arasa yana fashewa da matsananincin kuka

   Hajiya fuskarta ta jik'e shark'af da hawaye, jikinta na kyarma tamkar wacce ake zubawa k'ank'ara a jiki, yayin da take jin zantukan sa tamkar almara, tana jin ina ma mafarki take ta farka, a tsawon rayuwarta bata tab'a cin karo da tashin hankali irin yau ba, Yaron ta, jininta ya kasance dan' fashi, Sunan Allah take ambato ko zata samu sassaucin abunda take ji a zuciyata,

   Jin bata ce komai ba, hankalinsa ya k'ara tashi yace "Mama Dan Allah ki yafe mun ko rayuwata zata daidaita"

   Cikin shesshek'ar kuka tace "Hadda laifina Suraj, ina da laifi, ban tab'a tuntub'ar ka kan sana'ar ka ba, bana sa ido akan me kake ciki, ban tab'a bin diddik'in sana'ar da kake a lagos ba, ko da kayi kud'i lokaci d'aya ban damu da sanin taya ba, abunda ka gaya mun shi nake yarda, nayi kuskure na rashin saka ido sosai kan al'amur.....", Ta kasa k'arasawa sakamakon kuka da yaci k'arfin ta.

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now