10

2.9K 393 78
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*10*
UNEDITED

   Mik'ewa yayi ya d'auki mukullin motar sa, Yan sandan wurin ya umarta su mayar dasu cell, "Ranka ya dad'e yaushe za'a sake mu, Dan Allah a sake mu wallahi mun tuba" cewar Jangwal, Ko kallo bai ishe shi ba balle ya bashi amsa, ya fice daga station d'in, ya nufi gida cike da sak'e sak'en yadda zai yi maganin Tasleem.

    Mimi ke ta kuka, Hajiya da Fetta sun rud'e sun rasa me zasu mata ta daina kuka, Fetta ta bata nono tak'i sha, "Ko cikin ta ke ciwo" Cewar Hajiya, Fetta tace "Nima nayi tunanin haka", "Kira Suraj yazo mu kai ta asibiti" Hajiya ta fad'a tana karb'ar ta,

    "Kaii yarinyar nan anyi yar' banza" Su'ad ta fad'a tare da jan tsaki, Feena dake gefe tace "Wallahi duk ta cika mana kunne, kamar naje na shak'e ta", Su'ad tace "Daga ita har uwar ta na tsane su, sun zo sun zamar mana annoba cikin gida"

    Shigowar Suraj yasa Fetta tsayawa, Da sauri ya nufi Hajiya yana tambayar "Lafiya?, me ya same ta?", "Ina tunanin cikin ta ke ciwo, muje a kai ta asibiti", Ya mik'a hannu zai karb'e ta, Hajiya tace "A'ah kai da zaka yi tuk'i"

    Cikin minti 30 suka kawo asibiti, Dukkansu a rud'e, Ba b'ata lokaci suka samo ganin likita, Ya duba ta yace "Cikin ta ke ciwo da zazzab'i", Ya mata allura, ya rubuta musu drugs, a pharmacy na asibitin suka siya suka koma gida.

   Hajiya ta riga fita da Mimi wacce tayi bacci ana mata allura, Fetta tazo fita yace "Ki kula da ita sosai", Kai ta mishi nodding ta fice daga motar, Tana mamakin ta haifi ya' sannan a fad'a mata kula da ita, Yana wa Mimi wani irin so ne, baya son ko kad'an abunda zai tab'a ta ko ya raba shi da ita, zama part d'in su Hajiya ma dan ba yadda zai yi ne, Ya so ya fake da attacking nasu da akayi su dawo part d'in shi, Fetta ta buk'aci komawa,

   Falon sa ya zauna yana huce gajiya, Ya lalubo wayar sa, ya shiga text messages, Number da aka mishi message yayi dialing, wanda zuciyar sa ke masa zargin Tasleem,

   Tasleem na kwance d'akin ta, tana duba hotunan Suraj, wanda shine aikin ta kullum, Taga kiran shi, tayi saurin zabura, gabanta ya fad'i, "Ko dai sun fad'a mishi nice, na shiga uku na", Har wayar ta tsinke bata d'auka ba, Kira na biyu ya sake shigowa, Cike da zullumi ta danna receive tare da kangawa a kunne,

   "Tasleem", Ta jiyo muryar sa, sai da numfashin ta ya d'auke na wucin gadi, Wani sanyi taji na ratsa zuciyarta jin wanda take tsananin k'auna ya kira sunan ta, "Ko ba ita ba ce", "Ita ce", Ta fad'a murya na rawa,

   Ya cije lips d'in shi na k'asa, yana jin tamkar ya shak'aro ta ta cikin wayar, Ya danne abunda yake ji, Yace "I just call to say hi", Tasleem ji take tamkar a mafarki, farin ciki ya lullub'e ta, tama kasa magana, "Are you there?", "Eh eh ina ji", "Ok bye", Kafin ta sake magana, ya kashe, Wayar tabi da kallo ta kasa yarda, Ta cillar kan gado, Ta buga tsalle cike da murna, "Suraj ya kirani", Ta mari kanta, "Ko mafarki nake, ba mafarki nake ba, Suraj ne ya kirani, wayyoo dad'i, zuwan da nake gidan marayun sa ashe na shiga ran sa", Tayi wani juyi cike da farin ciki.

     Suraj na kashe wayar, yayi murmushin gefen baki sanin plan d'in shi will work, Ya ajiye wayar kan bedside drawer, Ya mik'e ya gabatar da sallar isha'i.

   "Ka kiyaye ni wallahi idan baka so ganin mummunan b'aci rai, duk yarinyar da kaje wurin ta sai ka samu rashin mutuncin da ka mata tace bata so, toh ka kiyaye ni", Kawu Lamid'o ya fad'a cike da fad'a, Bello dake durk'ushe gaban shi yace "Kayi hak'uri Abba amma wallahi bana musu wani abu, sune basa ra'ay...", Gwaggo ta katse shi "Dallah rufewa mutane baki, tunda kai kafi kowa bak'in jini, baka da muguwar kama, kana da abun hannun ka, me zai sa mata har uku su guje ka", "Abunda na gani kenan, toh wallahi ka maida hankalin ka, ko ka had'u da b'acin rai, ka koma wurin yar' Alhaji ka bata hak'uri, ka tabbatar ka shawo kan ta" Cewar Kawu Lamid'o,

   Wani zufa yaji ta keto masa, dan gaba d'aya baya sonta, tsarin ta da komai nata bai mishi ba, ga uwa uba wulak'anta shi da yayi, Kawu Lamid'o ya katse mishi tunani "Kana ji na ko?", Ya had'iye b'acin ran da ya taso mishi yace "Eh", "Tashi ka bani wuri", Ya mik'e yana jin tamkar ya fasa ihu tsabar bak'in ciki.

Tasleem farin ciki kamar ya kashe ta, Suraj ya kira ta, Ta kira Sophy ta sanar da ita, Tace "Ina miki murna, Allah ya bar soyayya", Ta kashe waya, Tasleem tabi wayar da kallo ganin tayi saurin kashewa kafin tace komai, "Dama nasan bak'in ciki take, bata sona da Suraj, toh sai dai ki mutu wallahi", Taja tsaki, ta kunna data, taje kan contact d'in shi tayi sending Hy, bai yi delivering ba, Suraj whatsapp bai dame shi ba, is hardly ga kanshi online.

    *12:30 na rana*
  
   Fetta na folding kayan mimi da aka wanke, Suraj yayi sallama ya shigo, k'amshin turaren sa mai dad'i ya ziyarci k'ofofin hancin ta, "Sarkin son turare", Ta fad'a a ran ta, Ba tare da ta d'ago kanta ba tace "Ina kwana?", "Lafiya lau", Ya amsa tare da zuba mata ido, Doguwar riga ce ta atamfa a jikin ta, Ta kamata d'ass a jikin ta, ta mata kyau sosai, Yaji tamkar ya rungume ta, Yayi saurin kwab'ar kan sa, Ya k'arasa bakin gado, Ya d'auki Mimi,

   "Ya jikin ta?", Ta amsa da "Da sauk'i bata sake wani kuka ba", "Kin bata magani?", "Eh", "Ok, ki kiyaye bata akan lokaci", Tayi nodding kai, Ya sumbace ta a goshi, "Get well soon My angel",
 
  Tana so ta tambaye shi, sun fad'i waya turo su, tana fargabar amsar da zai bata, Tana so tasan su wa ke farautar rayuwarta da na yar'ta, Me tana so taji laifin me ta musu?, me ta tare musu?

   Ya kwantar da Mimi, ya mik'e zai fita, Ta dake tace "Uhmm sun fad'i wanda ya turo su?", "Idan kinji waye me zaki yi?", "Ba abunda zanyi amma ina so nasan waye, da kuma dalilin shi", "Wata ce mai sona", Ya fad'a tare da kafe ta da ido, kamar mai son gano abu a tare da ita,

  Kalmar taji ta daki k'irjin ta, ranta yayi mugun b'aci, Bata san sanda ta furta "Mai son ka", Ya d'aga mata kai, "Meye had'in son da take maka da son kashe mu, tayi ta son ka mana, ka aure ta ma, but plss she should stay away from me and my daughter", Ta fad'a idonta sun rins sunyi jajir, "Bata son sharing d'ina da kowa shiyasa taks son kawar da ku",

  A fusace Fetta ta d'ago kai tace "Then ka sakeni ka aure ta who cares, an gaya mata ina son ka ko na damu da kai", Zafin furucin ta yasa shi kasa cewa komai, Ya juya ya fice daga d'akin,

   Ta fad'a kan gado tare da fashe da kuka,

   "Who cares, an gaya mata ina son ka ko na damu da kai", Shi ke mishi yawo a kwak'walwa, Yana jin zafi cikin zuciyar shi,

  Shi kad'ai ke driving, yana nanata maganganun ta a ranshi, har ya kawo bakin gidan su Tasleem, Wayar sa ya jawo yayi dialing number ta, bugu d'aya ta d'auka,

   "Ina bakin gate", Ya kashe bai jira cewar ta ba, Tsalle ta buga ta diro daga gado, "Unbelievable Suraj a gidan mu",

   Wadrobe ta bud'e ta fiddo wani dank'areren lace ta saka, ta d'auko sark'a da yan kunni tasa, ta chab'a kwalliya, ta bad'a jikin ta da turare ta fito tana yanga.

   _Yawan comments d'inku yawan typing d'ina, Comments dinku shi ke bani k'arfin gwiwar typing_

FOLLOW
VOTE
COMMENT

ZEELISH💓

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now