*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*27*
UNEDITED_Zainab Lawal, Ayshafareeda, Sa'adatu M Ya'u, Maryam M Ya'u, Shoter, Sophy, Murjanatu Sabi'u, Sarah, Reimxe ina jin dadin comment dinku😍😍_
Ba wanda take buk'atar magana dashi a yanzu sai Yasmeen, numberta ta saka, tayi dialing, Yasmeen dake kwance wayarta ta soma ruri, ganin number nijar, Tace "Wa ke kirana da number nijar", Sam tunanin ta bai kawo mata Fetta bace, Ta d'auka tana kangawa a kunne, "Assalamu Alaikum" Jin muryar Fetta tayi saurin tashi zaune da fad'in "Fetta ina kika shiga? Me ya kai ki nijar kika jefamu a damuwa",
Ta sauke ajiyar tace "Wurin dangina na tafi", "Dangin ki?", "Eh zan sanar dake komai amma sai kin mun alk'awari ba zaki fad'awa kowa ba har su Umma", "Na miki alk'awari babu wanda zai ji", Ta numfasa ta sanar da ita ba tare da ta b'oye mata komai ba, Yasmeen ta girgiza da ji at the same time ta taya Fetta murnar gane dangin ta, "Na taya ki farin cikin gane dangin ki, but meyasa kika tafi tsaya mun d'auki hukunci haka ba?, Me yasa kika tafi ba tare da cikar burin ki ba, bayan a ko da yaushe fatan ki a gano wanda suka kashe Addani ki mik'a su kotun addinin musulunci"
"Da wane baki kike so na furtawa Hajiya yaro mafi soyuwa a gare ta dan' fashi ne?, Da wane ido kike so na kalle ta idan na mik'a yaron ta kotu bayan halaccin ta gareni, ba tare da ta duba matsayina ba da rashin asalina ta had'a ni aure da gudan jinin ta, Taya kike so na fallasa sirrin mutumin da ya zama uban ya'ta, ko nak'i ko naso Suraj shine mahaifin Mimi, bana so a goran ta mata watarana, rabuwa dashi ita kad'ai ce mafita gare ni", Ta k'arasa da fashewa da kuka, Magangunta sun tsuma zuciyar Yasmeen, samun kamar Fetta a wannan zamani yana da matuk'ar wahala, despite shine silar kashe mahaifin ta har ta samu sauran rangwame a zuciyar ta,
"Kina ganin barin sa haka ya cigaba da ta'asa a doran k'asa taimakon sa kika yi?", "Komai nisan jifa k'asa zai dawo, a juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe, yadda na gano dan' fashi ne haka watarana asirin sa zai tonu, idan kuma Allah yayi nufin sa da shiriya sai ya shiryu, Ina rok'on ki da Allah Yasmeen kada ki zama silar rugujewar farin cikin Hajiya", "In Shaa Allah Fetta babu wanda zai ji, Suraj na bar sa da Allah tado case d'in a yanzu zai zama babban rikici", "Nagode da kika fahimce ni", Suka yi sallama ta kashe wayar,
Hawaye masu zafi suka cigaba da ambaliya kan kumatun ta, Magana da Yasmeen ya taso mata tabon da take k'ok'arin binnewa, "Why Suraj? Meyasa ka zab'i wannan mummunar d'abi'a ta zama hanyar ka ta ci da sutura?, Meyasa ka zama d'aya daga cikin masu kisan kai?", Turnik'in zafi zuciyarta ke yi, tana bugawa da tsananin k'arfi, ta dafe ta tana ambaton sunan Allah, Mik'ewa tayi kanta na tsananin sara mata, ta shiga toilet, ta d'aura alwala, ta fara gabatar da nafilfil tana rok'on Allah ya mantar da ita komai, ya saka mata natsuwa da kwanciyar hankali a zuciyar ta.
Suraj yadda yaga dare haka yaga rana, bacci ko da wasa bai d'auke sa ba, Tunda sassafe ya nufi gidan gonar sa, da hannu ya amsa gaisuwar ma'aikatan sa,
Files ya dauko yana dubawa yana lissafi ko zai d'auke masa hankali, but sam damuwa ta kasa barin sa, Knocking k'ofar da ake ya tabbatar masa Rabi'u ne, ya umarce sa ya shigo,
Cike da ladabi ya gaishe sa, Ya amsa, File ya ajiye a gabansa yace "Na samu dukkan bayanai akan Alhaji Barau, yau zamu iya zuwa gidan sa", "Ok ka shirya komai k'arfe uku na dare za.....", Kasa k'arasawa yayi sakamakon kalaman Fetta take masa yawo a kai "Taya kake tsammanin na cigaba da zama dan' fashi, wanda cin sa, tufafin sa, muhallin sa duka daga haramun ne, har nima ya ciyar dani ta wannan hanyar...kana tsammanin zan bari ya'ta ta taso cikin k'azamar haramtacciyar rayuwar ka, har abada ba zan bari tasan waye mahaifin ta ba, dan bara ta tab'a alfahari da kai ba......"