*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*21*
UNEDITEDHasken ranar da ya dallo d'akin, ya tashi Fetta wacce tayi bacci mai cike da mafarkan dangin ta, wayarta ta danna ta duba lokaci 7:30, Salati tayi ta sanar da ubangiji, mamakin irin baccin da tayi take, baccin da bata yi bane na kwana biyu ta rama.
Ta kalli Suraj dake baccin sa a natse, "Shima kenan bai tashi ba", Ta mik'e ta shiga toilet, ta gabatar da Sallah,
Bargon da ya lullub'e ta janye, tana kawar da kanta gefe, bata son ya zuba mata mayatattun idon sa, kallonsa na jefata a wani yanayi mai wuyar fassarawa,
Idon sa ya bud'e a kanta, yaga tana kallon gefe, Tari yayi wanda yasa tayi saurin juyowa, idon sa cikin nata, ya mata murmushi tare da kashe mata ido d'aya, Zuciyarta taji ta wani harba, tana jin zirr har zuwa tafin k'afan ta, Juyawa tayi ta fice d'akin ba tare da tace masa komai ba, Dariya yayi ya sauko daga kan gadon, ya shiga toilet, Da fuskar yaji yana so ya fara tozali, hakan ya saka shi yin tarin k'arya.
Zuciyarta cike da tunanin shi, da mamakin yanayin da take ji a kansa, ta nufi kitchen, dube dube tayi ba komai na girki a ciki, Dole ta koma falo ta zauna, bata kunna kallo ba, ta fad'a duniyar tunani, Tana son daidaita rayuwarta komai ya wuce, she want to live a happy life, tun tasowarta take facing challenges na rayuwa iri iri, duk da cewa kowane dan' adam da irin k'addarar sa, she is hoping tayi bankwana da bak'in ciki, fatan ta zargin da take akan Suraj kar ya zama gaskiya.
Ya fito cikin shirin sa na k'ananun kaya, sun mishi kyau sosai, komai ya saka kyau yake mishi, falon ya game da k'amshin turaren sa.
Bata d'aga kai ta kalle shi ba, har ya nufi k'ofar fita, Jin rufewar k'ofa ta d'aga kai ta kalli k'ofar, tana jin takaici na rashin bi ta kanta, bai da breakfast d'inta ba sanin sa ba komai da zata iya ci a gidan, ya fita ba sanarwa, Bud'ewar k'ofar ya katse mata tunani, ta kai duban ta, Suraj ne rik'e da leda mai tambarin restaurant, Sauke ajiyar zuciya tayi tana jin haushin kanta, na saurin judging d'in sa,
Kitchen ya shiga ya d'auko plate, ya juye chips da miyar k'odar a ciki, ya ajiye ruwan rubber gefe, Hannun ta taji ya kamo, yana mata alama ta sauko suci abinci, ta zauna ba tare da ta tace komai ba,
"Yau bazan samu gaisuwa ba", Ya fad'a yana jefanta da kallon sa dake kashe mata duk wata gab'a na jikin ta, Sam ta manta ta gaishe sa, Murya k'asan mak'oshi tace "Ina kwana?", "Ba zan amsa ba tunda sai da na rok'a", Ya d'auki spoon ya fara cin chips, Ta tsinci kanta da cewa "Kayi hak'uri shafa'a nayi", "Zan hak'ura amma da sharad'i d'aya, sai kinyi feeding d'ina, baki tab'a ba kullum nike yi", "Ya Allah mutum kamar mai juji", Ta fad'a a ranta, Gira ya d'aga mata alamar ya dai, Spoon ta d'auka ta fara feeding d'in sa, ba zata iya da rikicin sa ba, Shima ya shiga bata, Har suka cinye, ya d'auki tissue ya goge bakin sa, ya mik'a mata itama ta goge,
"Zan fita, anjima Kamal zai kawo muku abincin rana", Ya fad'a yana mik'ewa, "Allah ya bada sa'a", "Amin", Ya amsa yan ficewa.
D'aki ta koma, ta shiga dube dube, duka drawers har k'ark'ashin gado sai da ta duba, bata ga anything suspicious ba, Zama tayi kan gado tare da dafe kai ta furta "Ya Allah ka shige mun gaba, Ya Allah ka nuna mun waye Suraj Sa'id",
Wayarta tayi k'ara, Yasmeen ce mai kiran, Tayi receiving, Bayan sun gaisa, Tace "Ya binciken da kike?", Cike da karaya tace "Na kasa samun komai a tare dashi, ko a fuska banga wata alama ba", Yasmeen ta nisa tace "Kada ki karaya Fetta, kibi komai a hankali, In Shaa Allah komai zai warware and keep praying", "In Shaa Allah", "Allah ya shige miki gaba", Ta amsa da "Amin", Tayi hanging up, Hankalinta ba zai tab'a kwanciya ba sai tasan waye Suraj.
"Umma kinji Ya Suraj ya tafi da matsiyaciyar matar shi lagos", Cewar Bilkisu cike da b'acin rai, "Meye na b'acin rai, wallahi k'iris ya rage tsakanin su, ki daina damun kan ki" Aunty Jummai ta fad'a tana murmushin da ita kad'ai tasan ma'anar shi, Bilkisu tace "Ina fatan hakan", Aunty Jummai tace "Zaki sha mamaki a wannan karon", Tayi dariya tana jin hankalinta ya kwanta da furucin mahaifiyar ta.
Masu neman auren Feena sunzo, manyan mutane cikin shiga ta kamala, Su Kawo Sule ne suka masu bayar da auren, sun buk'aci a saka bikin nan da sati biyu, basa son wani shagalin biki sai d'aurin aure, sun nuna mahaifin yaron rik'akk'en dan' izala ne, Sun amince da hakan, bayan sun tuntubi Hajiya, suna tare da Feena, ta nuna itama bata so, burinta ta auri Fahad.
Mahaifin Tasleem ya zage yana ta shirye shiryen bikin yar' sa, Tana kwance d'aki tana chatting, Ya sameta, Ta mik'e zaune tana fad'in "Daddy", Ya zauna gefen gado yace "My daughter ana hutawa", Tayi murmushi, "Wane shiri kuke ke da angon na shagulgulan bikin da za'a yi", "Daddy nifah bai tab'a kirana ba, dama ina so na fad'a maka", A tsawace yace "What! Bai tab'a kiran ki ba, wane irin sakaran yaro ne, an gaya masa a banza zan bashi ya'ta"
Wayar sa ya jawo ya danna kiran Kawu Lamid'o, "Ranka ya dad'e ina wuni?", Bai amsa gaisawar ba ya rufe sa da masifa, "Me dan' yake nufi da baya kiran ya'ta ko baya son auren ne", "Kayi hak'uri Ranka ya dad'e, yana tsoron kiran ne, yasan da farko bai samu karb'uwa ba", "Ka gaya masa ya gyara, ya'ta ba'a banza take ba, ko wallahi a fasa auren", "A'ah ba'a yi haka ba, ayi hak'uri", Ya kashe wayar, Ya kai duban sa ga tilon yar' sa yace "Kwantar da hankalin ki babu wanda ya isa ya d'auke ki for granted", A zuciyarta tace "Sai Suraj Sa'id", A zahiri murmushi tayi.
Kawu Lamid'o Alhaji Tambari na kashe waya, ya kira Bello ya dinga zuba masa ruwan bala'i da masifa, "Ni kake so ka kunyata, toh wallahi baka isa ba, gobe gobe ka tattaro kayan ka ka dawo garin nan", Yana fad'ar haka ya kashe waya, tunda ya fara masifa bai bari Bello yace komai ba, Zufa ke tsattsafo masa yana jin tamkar ya had'iye zuciya ya mutu tsabar bak'in ciki.
2:30am na dare
Suraj tun fitar sa da safe bai dawo ba, sai yanzu, Fetta wacce tayi nisa a bacci, motsin sa ya tashe ta, ganin yana shiri wanda da alama daga wanka ya fito, Tayi lamo kamar mai bacci, Jallabiya kad'ai taga yasa, bai fesa turare ba, Wayar sa tayi k'ara, ya d'auka, "Gani nan zuwa, make sure ko shirya komai",
"Me zasu shirya a wannan tsohon daren?, ina za shi?", Ta jefowa kanta tambayoyin da bata da amsar su, Tana jin fitar sa, ta sauko gado a hankali tabi bayan sa, d'akin dake kallon wanda suke taga ya bud'e ya shiga, Ta koma bayan k'ofa ta lab'e tana jiran fitowar sa,
Shigar da ya fito da ita, tasa k'irjinta dokawa da k'arfin gaske, har kanta na sarawa, bak'aken kaya ne a jikin sa, riga da wando, kansa sanye da hula p-cap, hannun sa rik'e da facemask, Ya jawo d'akin ya rufe, tare da ajiye mukullin k'ark'ashin k'ofa, babu wanda zai lura dashi, Hular ya k'ara ja ta kare masa fuska, kafin ya wuce,
Fetta jikinta taji na kyarma, tunanin ta ya tsaya cak, k'wak'walwarta ta kasa tunanin komai, zuciyarta ke mummunan bugawa tamkar zata fasa k'irjinta ta fito, Da k'yar bakinta ya iya furta "Ya Allah", cike da k'arfafa ma kanta gwiwa, ta mik'e ta nufi d'akin da ya fito, mukullin da ya ajiye ta d'auka, tasa a jikin k'ofar, Ta bud'e key d'in, Ta d'aura hannun ta kan handle d'in, taji tamkar an rik'eta ta kasa murd'awa, jikinta ke rawa, tana jin wani tsananin tsoro da fargaba na ratsa zuciya da jikin ta.
FOLLOW
VOTE
COMMENTZEELISH💓