*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*49*
_This page is for all the Fatimas reading Fetta One Luv💞_
Kusan minti uku yana haka, zuciyar sa na harbawa da k'arfi, Shafah na gefe duk ta had'a gumi,
"Fatima", Ya kira sunan ta cikin d'aga murya, Fetta wacce ta idar da sallar magrib kenan, Daga yanayin kiran tasan ba lafiya ba, Addu'ar neman tsari ta karanta ta fito,
Kallon da yake jefan ta dashi yasa jikinta yin sanyi, yau kuma wani sharrin aka k'ulla mata,
" Meye ribar ki na son mallake ni?, ana so dole?", Taji kalaman sa kamar daga sama, Kallon rashin fahimta tabi a dashi, "Am asking you", Ya fad'a a tsawace, Cikin dakewa tace " Ban fahimci inda kalaman ka suka dosa ba", "Kada ki raina mun hankali", Ya juya kan Shafah " Me na kama ki kina yi?", Cikin rawar murya tace "Ina sa magani a abinci", Fetta ta zaro ido, " Waya saka ki?", Ta nuna Fetta,
Kusan mutuwar tsaye tayi, tamkar a mafarki haka take gani, Shafah da ta d'auka da zuciya d'aya, lallai dan' adam ba abun yarda ba ne, Bakin ta taji ya d'aure ta kasa furta komai,
"A ina ta samu maganin?", " K'awarta ta kawo mata", Ta kafe Shafah da ido cike da tsananin mamaki, "Kina mamaki asirin ku ya tonu ko?", Ko gezau bata yi ba, sai ma k'ara matsawa kusa da Shafah da tayi,
" Me zaki mata?, dukan ta zaki yi dan ta tona miki asiri?, Allah ne ya kama ki, ashe zaki iya shirka",
Zuciyar ta ke tafarfasa, bara ta iya jure munanan kalaman sa akan ta, Hannu ta d'aga mishi cikin d'aga murya tace "Enough"
Mamaki ya kama shi, ya hana shi furta komai ba, "Na gaji! Na gaji! Ni kad'ai ce mutum a duniya da kowa ya tashi sharrin shi Fetta, me na tare ma mutane, meya sa baka kyautata zato a kaina, you always think negative of me, Zaman mu ya kamata ace kasan wacece Fatima?", Hawaye da suka yi biyo kuncin ta, ta share ta juya kan Shafah, " Kiji tsoron Allah, kiji tsoron had'uwar ki da ubangiji a filin alk'iyama, ki zab'a kunyar duniya ko ta lahira, na d'auke ki da amana, ashe cuta ta kike, me na tare miki a duniya, Suraj kike so, idan shi kike so gaki gashi, ba sai kin mun sharri ba",
Suraj zuciyar sa yaji ta karaya, tausayin ta ya kama shi, "What if she is forming an act", Wata zuciyar tayi saurin kwab'ar shi " No iya gaskiyar ta ce", Ta katse mishi tunani "Idan mallakar ka nake son yi, why on earth zan saka Shafah, da kaina zan yi, for how long muke zaune tare da kai kafin zuwan ta, idan har zan iya sawa da kaina a lokacin meyasa yanzu bazan sa ba, Manzo SAW yace mu kyautata zato, why a ko da yaushe baka bincike kafin ka yanke hukunci, am not as bad as you think, rashin imani na bai kai can ba, i can't take this anymore, zuciyata bara ta iya d'auka ba, Na gaji SURAJ", Ta fad'a tare da zubewa k'asan carpet, ta fashe da kuka mai cin rai,
Jikinsa ya sake yin sanyi, bai san lokacin da ya kai k'asa ba, Ya rungumota jikin shi, yana bubbuga bayan ta,
Shafah tausayin Fetta taji na shigar ta, Tabbas ta d'auki hakk'in ta, idan kuma ta cigaba da yi ma Tasleem aiki, zata k'ara d'aukarwa kanta hakk'i, Da taji kunyar lahira gara taji ta duniya, akan kud'i da yanzu Allah zai iya d'aukar rayuwar ta, Tsoron Allah taji na shigar ta,
" Ku gafarce ni", Cewar Shafah tana matsar k'walla, Fetta ta janye jikin ta daga jikin sa, "Wallahi ba Aunty ce ta sakani ba", A fusace Suraj ya taso, ya shak'aro wuyan ta, " Maganin meye?, kuma Uban wa ya saki?, akan me zaki ce matata?",Shafah ta shiga kakari ta kasa magana, ya sake ta ta bugu da bango, Ta dafe kanta cike da azaba, Ya take yatsun k'afarta, tare da murza su da k'afa, Tayi ihun azaba, ya bige bakin ta da k'arfi, Tuni ya shiga jini,