*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*18*
*Unedited*_My habeebty is sick, Ku sata a addu"a, May Allah grant u shifah_
9:00am
Bayan sunyi breakfast, Fetta ta fito wanka tana shiri, Taji ana knocking, Dama idan zata shirya key take sawa, Doguwar riga ta zura, Ta nufi k'ofa ta bud'e, Suraj ne tsaye cikin English wears da suka matuk'ar yi mishi kyau, "Komai ya saka kyau yake mishi", Ta fad'a a ranta, Kanta ta sunkuyar k'asa tace " Ina kwana?", Bata jira amsar shi ba, Ta koma ciki,
Bai amsa ba ya shiga, Ya gaishe da Hajiya kamar kullum, "Takardar sallamar ki ce Dr ya bani yanzu", Fetta ajiyar zuciya ta saki mai d'auke da farin ciki, zata koma gida ta huta da wulak'ancin Suraj da k'annensa bata fatan wani abu ya sake had'a su.
Hajiya cike da murna tace " Mashaa Allah", Ita kanta ta k'osa ta bar asibitin ta koma gida, dama zaman asibiti sai dole.
Yace "Suyi packing zai je ya dawo su wuce", Hajiya tace " Kar ya dad'e"
Cike da murna da zumud'in komawa gida Fetta ta shiga had'a kaya, Hajiya ta kalle ta tace "Fetta sai murna kike zaki tafi ki barni koh", Kunya taji ta kamata tace " A'ah Hajiya zaman asibitin ne ba dad'i amma ina jin dad'in zama dake", "Toh idan hakane mai zai hana ki dawo gidana da zama",
Wata fad'uwar gaba taji, Ta had'iye miyau da k'yar, Ta lura da yanayin ta tace " Ba zan tilasta miki ba, ko ba zaki dawo gidana ba, Dan Allah ki rik'a zuwa kina tayani da wasu ayyuka", Tace "Toh In shaa Allah", Hankalinta ya d'an kwanta ko ba komai, zuwa zata rik'a yi tana dawowa ba zama dindin ba.
Suraj ya dawo, da envelope d'auke da kud'i 100k, Ajiye su yayi gaban Fetta yace " Ga kud'in ki kamar yadda na fad'a zan biya ki", Harara ta watsa wa kud'in ta mik'e tana d'aukar jakar kayanta, Hajiya tace "Fetta da kin d'auka, zasu rage muku wasu lalurori", "A'ah Hajiya Dan Allah nayi bana buk'atar biyan kowa sai na Allah", " Allah ya biya ki da mafificin alkhairi", Ta amsa da "Amin"
Suraj yace wa kansa "Yarinyar nan akwai fad'in rai, da yar' mai kud'i ce da anga isa da tinkaho",
Hajiya ce tace ya d'auki kud'in niyyar sa ya barsu a wurin, wanda zuciyar sa ke ce masa zata dawo da d'auka, Ya d'auka ya saka a aljihu.
Motoci biyu yazo dasu, Hajiya ta shiga d'aya shima ya shiga, D'ayar ya umarci driver ya kai Fetta, Ta shiga tana ta rab'a ido, bata tab'a shiga mota mai kyau da tsaruwar wannan ba,
A bakin k'ofar gidan su yayi parking, Tana k'ok'arin fita yace " Baiwar Allah ga sak'o inji mai gida", Ta kalli envelope da ya mik'o mata tace "Ka mayar mishi kace bana buk'ata", Ta fice abun ta, Driver yabi bayanta da kallo cike da mamakin k'in karb'ar ta,
Aliya tayi murnar ganin Fetta, nan suka shiga hira, ta sanar da ita buk'atar Hajiya na zuwa ta rik'a taya ta aiki, " Ke dai jinin ku ya had'u da Hajiya", Fetta tayi murmushi.Ma'aikatan gidan kowa murna yake da dawowar Hajiya, Wanda basu samu zuwa asibitin ba, Suna ta zuwa.
Suraj na garden na gidan, Yana shan iska, wanda most of the time nan ne wurin zaman sa, Driver ya rissina gaban sa cike da girmamawa, Yace "Ranka ya dad'e bata karb'a ba tace bata buk'ata", " Ajiye ka tafi", Ya umarci driver,
"Wacce irin yarinyar ce wannan mai fad'in rai da d'aukar kanta wani abu, idan tayi hakane dan ta burge sa toh bata burge shi ba", Yacewa kansa
Yau suka zana jarabawar k'arshe, Rigar ta duk an zane ta da signing, Ana ta bankwana, da exchanging phone numbers, Masu hotona nayi, Duk wanda da akwai maza a ciki bata shiga, Suma mazan sun san halinta babu wanda yayi attempting zuwa yace suyi hoto, Yau da ta kasance rana ce ta farin ciki, sab'anin haka Fetta take ji a ranta, Ta rasa dalilin da yasa bata jin dad'in ranta, ga gabanta da yake yawan fad'uwa, Ta bar hakan a bisa yanayi ne na rayuwa, Dama watarana kaji ka cikin farin ciki, ko sab'anin haka.Haka ta dawo gida sukuku, Bata tarar da kowa ba, Ta shiga d'aki ta kwanta tana tunanin rayuwa.
Mu'azzam ne durk'ushe gaban iyayen sa, Mahaifin sa yayi gyaran murya yace " Mun kira ne, mu baka umarni ba shawara ba", Cike da ladabi yace "Toh", " Zancen auren yarinyar nan ka janye", Ya razane ya d'ago ya kalli Mahaifin sa, Ya d'aga kai alamun Yes ya cigaba da cewa " Mun yanke shawarar had'a ka aure da yar' wajen yayan mahaifiyar ka", "Abba auren dole fah zaku mun, Dan Allah Ku barni na auri....."
Mahaifiyar sa ta katse sa "Nuna mana bamu isa da kai ba, banda baka san ciwon kan ka ba, Yarinyar da bata da asali zaka aura, Toh auren ka da Binta kamar anyi an gama", " Tashi ka ba mutane wuri", Mahaifin sa ya fad'a a tsawace,
Mu'azzam ya mik'e yana jin jiri na d'ibar sa, bai tab'a kawowa kansa rabuwa da Fetta ba, a yadda soyayyar ta ta kama shi baya jin zai iya cigaba da rayuwa, Da k'yar ya kai kanshi d'aki, Ya fad'a kan gado yana jin duniyar ta mishi zafi.
Fetta shiru bata ji Mu'azzam ya kira ta, Ta kira shi yafi sau biyar bai d'auka ba, Ganin har dare, Abun ya fara damun ta, Abinci loma uku tayi ta ajiye, Aliya na lura da ita, Tace "Meke damun ki ne Fetta?", " Ba komai, gajiya ce ta makaranta", "Kije ki kwanta ki huta", Tace " Toh",
Aliya tasan akwai abunda ke damunta, ba zata fad'a bane, Tana addu'ar Allah yaye mata.
Wayarta ta jawo ta sake kiran Mu'azzam a karo na ba adadi, Mu'azzam dake kwance yana ganin kiran, Ba zai iya d'auka ba, bai san me zai ce ba, bai san wani hali zata shiga ba, Har kiran ya tsinke.
"Ya zama dole ka sanar da ita da kan ka, idan taji a wani wuri zata d'auke ka mayaudari" Zuciyar sa ta fad'a mishi,
Wayar ya d'auka ya shiga rubuta mata message kamar haka " _Mu d'auki k'addara mai kyau ko mara kyau a duk halin da tazo mana, Allah ya k'addara haka zata kasance a tsakanin mu ba zama rayu da juna ba, iyayena sun zab'ar mun matar da zan aure, kiyi hak'uri Fetta, Ni mai k'aunar ki ne kuma har abada da sonki zan mutu, Allah ya sada mu da alkhairi_
K'arar text da taji, Ta jawo wayar, Ganin Mu'azzam ne, Cike da murna ta bud'e,
Tana gama karantawa, Ta saki wayar ta fad'i, Kanta taji na juya mata, tana gani dishi dishi, Duhu ne ya mamaye idon ta, ta fad'i.
*Kuyi managing wannan nima dishi dishin nake gani😫*
*Follow*
*Vote*
*Like**ZEELISH*💕