*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*29*
Ya koma d'aki, Ya kwanta, k'wakw'alwarsa cunkushe da tunani kala-kala.
Fetta a haka bacci ya d'auketa, bata farka ba, sai ana kiran sallar asuba, Da k'yar ta mik'e, jikinta is weak, Ta shiga d'aki,
Ya fito toilet yana sharce ruwan alwala, Ya kalleta ya kawar da kai, Ko kallo bai isheta ba, Ta shiga band'aki, Ruwan zafi ta tara, ta sake gasa jikinta, Tayi wanka, ta d'auro alwala,
Ya tafi masallaci, Taji dad'in shiryawa ba takura, riga da skirt d'inkin lace ta saka, Ta gabatar da sallar asuba, A wurin ta zauna tana karatun Qur'ani.
Tun daga falo yake jiyo k'ira'a mai dad'i na tashi, "Mashaa Allah" Ya furta, Zama yayi yana saurare baya so ya shiga, yayi interrupting d'inta, Karatun sosai yake shigar sa yana tsuma zuciyar sa, Ayar k'arshe ta kai, Yaji tamkar kar ta daina.
Ya mik'e ya shiga d'akin, Tana folding sallaya, "Ina kwana?", Da matuk'ar mamaki ya bita da kallo, despite abunda ya mata take gaishe sa, Tayi hanyar fita ya amsa " Lafiya lau", Ta fice ta nufi kitchen,
Dauriya take, jikinta baya mata dad'i, Breakfast ta fara k'ok'arin had'awa.
Kwanciya yayi ya d'aura kansa kan pillow, yana kallon pop, Tunani da nazarin ta yake, Yaja siririn tsaki ya mik'e, Ba zai samu baccin safe ba, akwai mutanen da zai had'a dasu 7 na safe.
Cikin awa d'aya ta kammala kunun gyad'a da fanke, Ta jera masa kamar kullum, Ta shiga gyaran gidan.
Tana turara turaren wuta, Ya fito sanye cikin shadda coffee colour sabuwa dal, Ko mai hassadar mutum k'aryarsa ya kushe Suraj, yana cikin jerin maza ajin farko, masu ji da tsantsar kyau, gayu, kud'i da k'uruciya.
"Ina ma yadda yake da kyawun halitta haka yake da na hali", Cewar Fetta, Tana cigaba da zagayawa da turaren wuta, zaka rantse bata lura dashi ba, but tsaf ta kalle sa ba tare sa ya sani ba, Da wutsiyar ido yake kallon ta, Ya zauna dining table, Ya cika cikin sa,
" Zan zo da bak'i anjima, kiyi abinci dasu", "Allah ya kawo su Lafiya", " Amin", Ya amsa yana gyara zaman hular sa, Hular ta zauna daram a gashin kansa ta k'ara masa kyau, Ya fita ya bar falon da k'amshin turaren sa.
"Ya Allah ka zab'a mun abunda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah ka shige mun gaba akan dukkan al'amurana", Fetta ta fad'a tana d'aga hannun ta sama, " Amin", Taji muryar Aliya ta amsa,
"Umma yaushe kika zo?", Ta fad'a tana rungume ta, " Shigowa ta kenan, jiya nayi mafarkin ki, na kira wayarki bata shiga, nace bari nazo na ganki", "Allah Sarki Ummana, Ina Ali?", " Yana koki ya tafi hutu", "Shine baki kawo mun ba", " A'ah kiji da mijinki", "Uhmm, bari na kawo miki karin kumallo", " A k'oshe nake wallahi", "Kai Umma", " Allah kuwa"
Ta nisa tace "Fetta", " Na'am", "Idan har kin d'aukeni mahaifiyar ki, ina so ki fad'a mun wane irin zama kuke da Suraj, mafarkin da nayi jiya yasa na kasa samun natsuwa", " Lafiya lau muke Umma", "Fetta kalleni", Ta d'ago ta kalleta, " K'arya kike, k'wayar idonki ta nuna kina cikin damuwa, ki fad'a mun matsalarki ni mai baki shawara ce", Tabbas tana neman wanda zatayi sharing problems d'inta dashi, tana neman mai bata shawara, but bata so Aliya ta shiga damuwa a dalilin ta.
"Ke nake saurare, nayi alk'awari zan taimaka miki", Bata b'oye mata komai ba, ta fad'a mata, Cike da tausayinta ta rik'o hannun ta, Tace " Meyasa baki sanar dani tun farko ba?", "Bana so ki shiga damuwa", " Matsalarki ai tawa ce Fetta, duk abunda ya shafeki ya shafeni", "Kiyi hak'uri Umma", " Ya wuce, hakan da kika yi ya nuna zaki rik'e sirrin mijinki",