50

3.8K 295 11
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*50*
*Unedited*

  *9:45am*

  Suraj yana tsaye bakin dressing mirror, yana saka cufflinks, Cikin shigar sa ta shadda light blue sai d'aukar ido take, Ya d'auki turare ya fesa, Ya gyara zaman hular sa,

   Ya juya kan Fetta dake gyara gado, "Zan tafi d'aurin aure", " A dawo lafiya",

   Har ya kai bakin k'ofa ya juyo "Kar ki sake kiyi shara", Tayi shiru tamkar bata ji sa ba, " Are you deaf ?", Ta sake mishi shiru, Takowa yayi cikin izza ya dawo cikin d'akin, Yazo daf da ita ta yadda tana jiyo numfashin sa,

    "Daraja d'aya kike ci", Ya fad'a tare da hura mata iskar bakin sa ya fice, K'amshin mouth fresh mai dad'i ne ya ziyarci hancin ta, ya saka ta lumshe ido, " Ya Allah", ta furta, Ta sauke ajiyar zuciya tare da mik'ewa ta fara goge dressing mirror.

    Sashen Hajiya ya nufa, ya umarci Inna mai aiki tazo sashen shi ta gyara,

    Sallamar ta ta jiyo daga d'aki ta amsa ta fito, "Mai gida ne yace nazo nayi gyara", " Ki bar shi kawai Inna", "A'ah ba'a yi haka ba, kina buk'atar hutu",

     Ta bud'e baki zata bata amsa mararta ta murd'a, Ta duk'a tare da ambaton sunan Allah, Inna ta rik'e ta tace " Subhanallah, sannu ki koma d'aki ki kwanta", "Yawwa", Ta amsa da k'yar, Tana dafa bango ta shiga d'aki, ta d'auki zam zam tasha, ta shafa, Tabi lafiyar gado cikin minti uku bacci ya d'auke ta.

    " Sister please tayani na saka rigar nan", Su'ad ta fad'a tana k'ok'arin saka riga tak'i shiga, "Mutum yayi ta sa ana mishi matsattsun kaya", Cewar Feena tana taya ta jan rigar, " Adnan ne yafi so ya ganni da irin kayan", "Ah lallai ai sa kiyi ta wahalar sawa da cirewa", " Idan munyi aure shi zai rik'a tayani", Feena ta bud'e baki tace "Ahh ko kunya", " Kunyar ki zan ji", Sukayi dariya.

    K'aramin gyale ta yafa, ta fice tana rambad'a k'amshi, Ta cikin mota ya zuba mata ido, yana jin wani feelings a tare da ita, Ta bud'e murfin gaba ta shiga, k'amshin turaren ta ya game motar, wanda ya sake jefa shi a wani yanayi(Mata a kula, a daina cika turare idan za'a waje saurayi)

   Rungumota yayi jikin shi, Yace "Kinyi kyau My baby", Ta sake kwantar da kai jikin shi tace " Thank you", Ya manna mata kiss tare da cusa hannun shi cikin rigar ta, bata hana shi ba, sai ma k'ara bashi goyon baya da tayi, suka shiga romancing juna, a kasalance ya d'ago yace "Baby please muje hotel", " Am scared", "Ba wani tsoro ni zaki aura fah, kina so na shiga wani hali", Ta girgiza kai, " Please ki amince muje", Tayi nodding kai, "Wow I love you", Ya fad'a tare da manna mata kiss.

   Bilkisu sun isa Dubai, Hajiya Rabi ta kama musu makeken hotel wanda sai masu kud'i ke sauka a can, suna ta masha'ar su, a tare suke kwana tamkar mata da miji.

    Karima ta shiga gyaran jiki, duk wani kayan gyaran jiki da maganin mata, ta siya tana amfani dashi.

    " Shiru kake ji Malam yaci shirwa" Aunty Jummai tacewa Aminiyar ta, "Hmm nifah lamarin nan ya soma bani tsoro, ba irin asirin da bamu yi ba amma ace cikin yak'i zubewa", Cewar Aminiyar ta, " Hmm mu zuba ido dai muga aikin Boka", "Toh ya zancen komawar Bilkisu", " Sai Yar iskar baroroji tayi gaba", "Yawwa haka ya dace ta wuce ajin kishi da baroroji yar' mai gadi",

    Fetta wuni tayi bacci, bata farka ba sai ana kiran la'asar, Ta tashi da sunan Allah, Toilet ta shiga, ganin mutum kwance cikin jacuzzi, tayi hanyar fita a tsorace, Taji an jawota, Ihu ta saki, bakinta taji  an toahe, juyowar da zata yi idonta ya sark'e da na Suraj, " Yaushe ya dawo?", Ta tambayi kanta,

    Soso ya saka mata a hannu, tare da nuna mata baya, Mamaki ya hanata ce masa komai, Gira ya d'aga mata alamar ya dai, Hannun sa ta jawo, ta saka mishi soson ta juya ta fice, Yabi bayanta da kallo cike da mamaki, "She  is taking advantage na babyn jikinta tana raina mun hankali dole na gyara mata zama", Ya fad'awa kansa, Ya cilar da soson gefe ya watsa ruwa ya fito,

    Fetta  baya wurin kitchen taje tayi alwala, Ta shigo d'akin ta d'auki sallaya ta shimfid'a ta saka hijab, Ta kabbara sallah ba tare da tabi ta kansa ba, wanda hakan ya k'ara k'ular dashi,

    Shirin sa yayi cikin kaya mara sa nauyi, Ya zauna gefen gado yana jiran ta idar,

   Minti biyar ya d'auke ta, ta idar tayi addu'o'i, Ta nad'e sallaya da hijab ta ajiye, zata fita d'akin, Yace " Zo nan", Cikin isa,

    Gaban sa taje, "Kin tsaya mun a kai tamkar soja", Ya fad'a cike da fad'a, Kujerar dake gefe ta zauna, Ya taso ya tsaya daf da ita, " Dan kina d'auke da babyna bashi zai baki privilege na mun rashin kunya da rainin hankali ba", Kallon bata fahimce inda kalaman sa suka dosa ba tabi shi dashi, "Wallahi ya zama na k'arshe da zan saka ki abu ki k'i yi, Suraj baya bada umarni a tsalleka", Ya fad'a tare da had'a yatsun sa ya basu d'ass,

   Murmushin gefen baki tayi tace " Shikenan, zan iya tafiya?", Bakin sa ne ya sark'e tsananin mamaki ya hana sa furta komai, Jin yayi shiru ta mik'e ta fice,

    "Yarinyar nan ta raina ni fah, kai ta raina mun hankali", Zuciyar sa ta fad'a mishi, Ya mik'e a fusace, " Idan kamata wani abu ya shafi babyn ka fah", Wata zuciyar tace mishi, "Zanyi maganin ta daga ranar da babyna yazo duniya", Yayi assuring kansa.

    " Haba My baby ki daina kukan mana, so kike kije gida a fuskanci wani abu", Cewar Adnan cikin sigar lallashi, Su'ad dake lullub'e cikin bargo taja majina tace "K'asana ke zafi sosai", " Muje na saki a ruwan zafi", Ya fad'a yana janye bargon, Ya d'auke ta zuwa toilet, ya tara ruwa a bathtub, ya saka ta, Tana ihun azaba,

    Tayi wankan tsarki, Ta shirya ya mayar da ita gida, bayan ya biya ,ya mata shopping mai yawa, Tana komawa gida sai baccin wahala, dan Adnan bai mata da wasa ba.

     Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, Cikin Fetta ya shiga wata bakwai, yau ciwo gobe lafiya, ga ciwon mara da take yawan fama dashi, Suraj na bata kulawa sosai, Hajiya, Aliya da Yasmeen suma ba'a bar su a baya ba, wajen bata kulawa, Malam na aiko mata addu'o'i akai akai, Ganin ciwon ba sauk'i, Yayi deciding su tafi Umrah, su rok'i ubangiji daga can su wuce London, baya so ta haihu a 9ja.

    Fetta ta fito da shirin ta cikin jallabiya da gyale, sun matuk'ar yi mata kyau, cikinta da yayi tsini ya fito d'ass, Da kallo yabi ta,

   "Koma ki saka hijab", Ba tare da tace  komai ba, ta koma tasa, still ya mata kyau,

   A mota ba mai cewa kowa komai ba, har suka kawo immigration office, Yace " Ta fito", Ta biyowa bayansa,

     Sun tarar da layi sosai, Amma abun ku da naira da kuma hanya, ba b'ata lokaci ta shiga aka mata passport.

    _Kuyi managing this bani da chaji, kuma am busy_

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now