22

2.7K 319 50
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*22*

  Zuciyarta ke ingiza ta ta bud'e, wani courage taji yazo mata, Ta murd'a handle d'in tare da tura k'ofar d'akin da k'arfi, Tsaye tayi bakin k'ofa tana bin d'akin da kallo, babu gado balle katifa a cikin sa, akwatuna ne na k'arfe a k'alla zasu kai biyar, gefe kuma wani k'aramin safe ne, jallabiyar da ya cire ta gani ajiye gefe, A hankali take taka k'afarta cikin d'aki, har ta kai bakin akwatunan, Safe dake gefe takai hannunta ta  bud'ewa taji a rufe, Kamar ance kalli gefe, ta hango wata yar' k'aramar jaka a sak'ale, ta jawo ta bud'e, keys ne da yawa a ciki, Ta d'auki d'aya wanda take kyautata zaton shine na safe d'in, Tana sawa ya bud'e,

   Takardu ne masu yawa a ciki, ta fiddo su, kowacce takarda tana d'auke da sunayen mutane wanda daga title na sunan, zaka san manyan mutane ne, hamshak'an masu kud'i, sauran takardun bayanai ne na kowane, address d'in su, shigowar su gari, wuraren da suka je, kud'ad'en da ake tunanin suna da a gida, Kud'in da suka yi withdrwaing, "Meye had'in sa da haka?, meyasa duka mutanen dake rubuce hamshak'an masu kid'i ne? Meye alak'ar shi dasu?", Ta jefawa kanta tambayoyin, "Dan' fashi yana buk'atar bayanai akan mutum kafin ya shiga gidan sa fashi", Zuciyarta ta bata amsa, K'irjin ta ya doka, takardun ta mayar ta rufe safe d'in,

   Akwatin farko ta bud'e, kayan sawa ne a ciki, wanda duka bak'ake ne, sai p-caps  a kalla zasu kai biyar, da facemasks irin wanda ba'a ganin komai a fuskar mutum sai idonsa, a k'alla zasu kai goma, "Meya had'in sa da wannan kaya?", "Kaya ne irin wanda yan fashi ke sawa su b'atar da kama", Zuciyarta ta bata amsa, gefen kanta taji ya sara, "Ya Allah", Ta furta tana jin karaya da sarewa, A hankali ta mayar da akwatin ta rufe,

    Abunda ta gani a d'ayar akwatin ya matuk'ar d'aga hankalinta, bindigogi ne kala kala da bullets, kanta ke juyowa mata tana ganin dishi dishi, Jikinta ya shiga kyarma, Zama tayi a wurin dirshan ta kasa koda k'wakk'waran motsi, Ta kasa wani tunani, komai nata ya tsaya, banda zuciyarta dake bugawa da tsananin k'arfi, Sunayen Allah take ambata, a hankali taji k'arfi da sassauci na saukar mata, Hannun ta na rawa ta rufe akwatin, Ta fito d'akin tana jin kanta na juyawa mata, Ta rufe ta mayar da mukullin wurin da yake.

   Da k'yar ta kai d'akin da suke, ta fad'a kan gado, Ta rasa tunanin me zata yi, "Suraj Dan' fashi", Tayi saurin kwab'ar kanta "Baki tabbatar ba", "Wacce hujja nake nema bayan wannan?", "Still kina neman k'wak'kwara", wani sashe na zuciyarta ya fad'a mata, "Ya Rabbi ka taimakeni Ya Allah ka fahimtar dani Ya Allah ka fitar dani a duhu, Ya Allah ni baiwar ce mai rauni kada ka d'aura mun abunda ba zan iya ba", Ta fad'a da k'arashewa da kuka mai tsuma zuciya, Kuka take zuciyarta na zafi tamkar ana hura mata garwashi, Kusan minti talatin tana kuka, kafin ta mik'e ta shiga toilet, ta d'auro alwala ta fara gabatar da nafilfili.

  Wuraren k'arfe hud'u na dare Suraj ya shigo d'akin sanye da jallabiya, a zaton sa tana bacci, ganin ta tana sallah, ya d'an tsorata, Allah yasa bata gane ya fita ba, Kan gado ya nufa ya kwanta, ya sumbaci Mimi dake ta bacci abun ta, Fetta sam bata ji shigowar sa ba, ta mik'a dukkan hankalinta wurin bautar ubangijin ta da kai masa kukan ta, shi kad'ai zai mata magani.

   Har aka kira sallar asuba, ta gabatar da sallar asuba, ta zauna tana karatun Qur'ani, Suraj tunda ya kwanta bacci mai nauyi ya d'auke sa, Kukan Mimi yasa ta tsaya da karatun, Ta juya ta d'auke ta, Ganin sa kwance yasa zuciyarta bugawa, ta kalli kayan dake jikin sa, "Mayaudariya mai fuska biyu", Ta tsinci kanta da furtawa, Haushin sa lokaci d'aya taji ya lullub'eta,

    Ta d'auki Mimi tana breastfeeding, tausayinta na ratsa ta, "Idan Suraj ya kasance dan' fashi, wacce rayuwa Mimi zata yi, ya zata taso taji Mahaifinta Dan' fashi ne", tana fatan kada hakan ya kasance, Yayin da zuciyarta ke son gaskata mata,

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now