31

4.1K 338 21
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*31*
*Unedited*

   Zaune take saman carpet tana gyara kayanta, Tana jera su cikin wardrobe, Yana zaune saman gado ya barbaza takardu yana dubawa, Jefi jefi yana d'ago kai ya kalleta, Dukkan hankalinta na kan gyaran.

      Wayarsa tayi ringing, Yayi receiving, "Ku kula da kyau, Gani nan zuwa", Shine abunda taji ya fad'a Ya kashe.

      "Ke!", Ta tsani kalmar tayi tamkar bata ji sa ba, " Fatima", Karon farko da ya kira sunan ta, sai taji sunan daban a bakin sa, ba kowa ke kiranta haka ba, "Na'am" Ta amsa murya a sanyaye, "Zo", Ta mik'e taje gabansa, " Tayani had'a takardun nan", Ya fad'a yana mik'ewa ya shiga toilet,

     Takardu ne masu yawa sosai, Ta shiga had'a su wuri d'aya.

    Wanka yayi ya fito, Ya shirya, ya d'auki mukullin mota ya fice, D'akin ya game da k'amshin turaren sa, "Uhmm" Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya sakamakon k'amshin sa da ya daki hancin ta,

   Sunayen mutane da wurare ne birjik a takardun, Ta tab'e baki tace "Kamar wani dan' lek'en asiri", Ta had'a su ta saka a drawer da taga yana ajiyewa.

     " Dad please ka taimaka ya aureni, wallahi zan mutu", Tasleem ta fad'a tana fashewa da kuka, ta dafe zuciyarta, A rud'e ya rik'ota "Sorry My daughter, ba zaki mutu ki barni ba", Mahaifiyarta taja tsaki tace " Alhaji wallahi kai ke biyewa yarinyar nan ace abunda take so za'a mata", "Idan ban mata ba, wa kike so nayi ma ita kad'ai Allah ya bani", Ta tab'e baki ta mik'e ta bar d'akin,

    Tasleem ta cigaba da tari tana dafe zuciya, Ya kwanto ta jikin shi, " Bana so kina tada hankalin ki, ba dai Suraj ba", Ta d'aga kanta sama, "Kin aure shi kin gama, meye amfanin dukiyata idan ba zanyi amfani da ita wurin samar miki farin ciki", " I Love You Daddy", "Love you too My daughter, bana son damuwar ki", Ta d'aga kai sama cike da shagwab'a.

    Alhaji Suleiman Tambari shine Mahaifin Tasleem, Matar sa d'aya Rakiya, Yana da tarin dukiya bana wasa ba, Kuma Dan' siyasa ne, Senator ne, Tasleem kad'ai ce yar'sa ya d'auki son duniya ya d'aura mata, Duk abunda take so, shi yake mata.

    " Ina jaririyar da aka kawo Yau?" Suraj ya tambaya, "Gata ranka ya dad'e", Matron ta fad'a tana rissinawa, Ya karb'i yarinyar, Kyakkyawa da ita tasha lullub'i, Cike da tausayawa yace " Waya kawota?", "Wani mutumi ne ya tsinceta a bola", " Ban san sai yaushe mata zasu yi hankali, su daina cikin shege, suna haifar yara suna zubar dasu, Kinsha wahalar rainon ciki wata tara, kin haihu raino ne ba zaki iya ba, wasu na neman haihuwa, yayin da wasu ke zubarwa, Allah yasa mu dace", Matron tace "Amin", " An rubuta details na komai akanta", "Eh ranka ya dad'e", " OK, ina so a yanka rago a saka mata suna Halima", Ta amsa da "OK Sir, Allah ya k'ara maka arzik'i ya sada ka da alkhairi, samun irin ka da wuya", Ya amsa da " Amin", Ya mik'e yana zagaya orphanage d'in, Yana tambayar yaran matsalolin su, Duk jariran da aka kawo sabuwar haihuwa, Shi ke musu hud'uba, ya saka musu suna a yanka rago.

  
        Hajiya ta aiko tana kiran Fetta, Tazo wucewa, Feena ta saka k'afa, taci karo da k'afar saura kad'an ta fad'i, Tayi saurin rik'e kujera, "Bakya kallon gabanki ne", Harara ta juyo ta watsa mata tayi gaba, bata da lokacin tsayawa sa'in sa da ita, Su'ad tace" Tabb kinga hararar da ta miki kuwa", Feena tayi k'yafci tace "Zata san tayi da ya' wallahi, jira kawai nake Ya Suraj ya auri Tasleem, ta raina kanta", " Nima shine burina, zaman gidan nan sai ya gagare ta", "Wallahi da k'afar ta zata gudu", Sukayi shewa.

     A d'aki ta sameta, Har k'asa ta duk'a ta gaishe ta, Ta amsa da sakin fuska, Leda ta jawo ta zazzage laces masu yawa, Tace " Laces ne nasa Suraj ya kawo miki daga Lagos, ki rik'a siyarwa, bai kamata kina zama haka ba sana'a, kinga ba zaki rasa kud'in kashewa ba",

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now