*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*19*
UNEDITEDMURTALA MUHAMMAD INTERNATIONAL AIRPORT.
Jirgin su yayi landing, Fetta yau ce rana ta farko da ta fara zuwa lagos, Tabi airport d'in da kallo, tsarin sa ya burgeta sosai, Driver Suraj already yana airport, ba b'ata lokaci suna shiga mota, yaja zuwa Victoria Island.
Suraj ya kai dubansa ga Fetta yace "Zanje wani wuri, ki shiga ciki, idan kuna buk'atar wani abu ki kirani", Ta amsa da "Toh", Ta bud'e murfin motar ta fita, Kamal cikin girmamawa yace "Hajiya sannu da zuwa", Da sakin fuska ta amsa da "Yawwa", Yaja lugagge d'insu zuwa ciki, Gidan tsaf dashi, k'aramin falo ne mai d'auke da kujeru sai kayan kallo, D'akuna biyu ne d'aya na kallon d'aya, Na gefen dama ta bud'e ta shiga, Shima a gyare yake, Mimi ta shimfid'e kan gado, Ta cire hijab wanda Suraj ya tursasa mata sakawa, d'akin tabi da kallo tana tunanin ta ina zata fara binciken ta, "Ya Allah give me strength" Ta fad'a tana d'aura hannun ta kan k'irjinta dake buga mata, duk sanda zata tuna furucin Yasmeen, da kalar bugun da zuciyarta ke yi,
"This is the right time na karanta littafin kafin ya dawo", Zuciyarta ta fad'a mata, Akwatin ta jawo, ta d'auko littafin, Ta zauna k'asa tare da jingina cikin gado, Cike da fargaba ta bud'e shafin farko, Ganin rubutun da yaren buzaye, gabanta ya fad'i, Ta fara karantawa....
*GARIN AGADEZ*
MASAURATAR AGADEZMasauratar Agadez babbar masarauta ce a jamhuriyar Nijar musamman saboda yankin azbin, masaurata ce mai cike da d'umbin tarihi, yankin Agadez yafi kowane yanki girma a jihar Nijar, kuma garin ya kasance cibiyar ilimin addini a yankin sahara.
Mai martaba Abutalib Shuwairan shine sarkin garin, ya gaji sarautar ne wurin Mahaifin sa bayan Allah ya mishi rasuwa, Sarkin da ya mallaki tarin dukiya wanda duk k'iyasin mutum bai isa ya k'iyasta yawan dukiyar da Allah ya bashi ba, Mutum ne mai halin dattako da k'ok'arin adalchi a tsakanin al'ummar sa, Mutanen garin na kiran sa da Amanukal ma'ana Sarki, Duk da kasancewar sa sarki bai tara iyali da yawa ba, Matan sa biyu Lele da Azagas, Lele itace uwargida mace masifaffiya wacce k'iris take jira tayi fad'a, kowa a masarautar tsoronta yake, ta d'auki karan tsana ta d'aurawa Amarya Azagas da yaranta, Lele yaranta hud'u, uku mata Safah, Laila, Aminita, namiji d'aya Ibrahim, Taso haihuwar namiji a farko saboda ya gaji sarki sai ya zama shine na k'arshe, Tana da yara biyu Sarki ya auro Azagas, ba irin tashin hankalin da Lele bata yi ba lokacin auren,
Azagas macece mai sanyin hali, sam bata son hayaniya, magana ma wahala take mata, Hakan ya k'arasa Lele ta raina ta, kowane iskanci yi mata take, bata tanka ta.
Duk gidan sarauta ba'a raba shi da hassada, gulma, bak'in ciki, makirci da sharri, hakan take a masauratar agadez, duk da k'ok'arin da Amanukal yake wurin ganin ya daidaita gidan sa.
Azagas watan ta tara ta haifu d'anta namiji Elhidir, Farin cikin wurin Mai martaba ba'a magana ganin ya samu magaji, Azagas tasha alkhairai daga masoyan sarki, har ma da mak'iya masu neman gindin zama, masu bata zinari da dirham, da alkyabba na alfarma, kaya masu masifar tsada, haihuwar sa ba k'aramin d'aga hankalin Lele tayi ba, sanin shi zai zama magajin sarki, tun yanxu taga irin alkhairin da Azagas ke samu, A daren suna Lele ta aika a sace shi a kashe, Azagas na kwance d'akinta tare da Elhidir, taji tamkar ana buga k'ofa, masu mata hidima nauyayyen bacci suke, wanda Lele amintacciyar baiwarta tasa ta zuba musu maganin bacci a abinci,
"Waye ke buga k'ofa?, ina su Allam su...", Bata k'arasa ba taji ana fad'in "Gobara gobara", Cike da tsananin tashin hankali ta d'auki Elhidir tayo waje, sai ji tayi an matse ta da bango, an fisge yaronta, ihun da tayi ya farkar da hadiman ta, "Yarona sun gudu dashi", Ta fad'a cikin tsananin tashin hankali tana kuka, Kan ace me masauratar ta kicime, aka bazama neman yaron, Labari ya kai sashen Amanukal, yasa dogarai da fadawa su shiga neman sa,