*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*39*
*Unedited*Tamkar wad'anda akaiwa mutuwa haka Aunty Jummai da Bilkisu suka isa gida, Fuskar su sam babu walwala.
Kujerar dake tsakar gida Aunty Jummai ta zauna tana fad'in "Fetta da ciki tirk'ashi", Bilkisu tace " Umma idan ta haihu na shiga uku", "Ke dallah daina kiran ta haihu, ke har fata kike ta haihu", Bilkisu ta girgiza kai, " Bamu ga ta zama ba, kawar da cikin shine mafita", Bilkisu tace "Ban tab'a jin tashin hankali irin na yau ba", Aunty Jummai tace " Nifah yarinyar nan gani nake tamkar tana tsafi, kome muka mata baya kamata" (K'arfin addu'a kenan", "Ba zata rasa tsafi ba, duk asirin mu baya cin ta", " Ba tsafi take ba, ko itace bokan sai na b'arar da cikin", Tayi assuring kanta.
Fetta kusan awa biyu ta d'auka tana bacci, A hankali ta bud'e idonta tana jin ta wasai, Zazzab'in ya sauka, ciwon kan ma ya rage sosai, Suraj dake zaune kan kujera yana operating system, Ya d'ago kai ya kalleta, Idonsa cikin nata, Gira ga d'aga mata alamar "Ya dai" Kawar da kanta tayi gefe,
"Ya lafiyar babyna?", Ba ma lafiyar ta yake ba, ta babyn sa, Haushi taji ya bata, da jin dama cikin ya b'are, Banza ta masa tana nufar hanyar toilet, Ji tayi ya juyo da ita, suna fuskantar juna, Hannun sa ya d'aura saman wuyanta, Yaji babu zafi, Ya shafa cikinta yace " Allah ya k'ara ma babyna lafiya", Da kallo tabi sa, Ya kashe mata ido d'aya, Yana ficewa d'akin,
"Huu", Ta fad'a tana sauke ajiyar zuciya, Ta shiga toilet, Ruwa masu d'umi tayi wanka dasu, Ta k'ara jin k'arfin jikin ta.
Fitowar ta falo yayi daidai da shigowar sa tare da Hajiya, da wata Yar' budurwa a baya d'auke da basket na abinci." Ina wuni?", Ta gaishe da Hajiya tana rissinawa, Hajiya tayi saurin d'agata "A'ah tashi, ki daina duk'awa kinsan bake kad'ai kike ba", Kunya taji ta zauna k'asan carpet tana sunkuyar da kai, Fetta bata tab'a zama kan kujera, Hajiya na zaune, wanda hakan ke k'ara sa Hajiya ganin tarbiyar ta.
" Ajiye abincin kan dining", Hajiya ta umarci yarinyar, "Tuwo ne nayi miki da kaina, kici zaki k'ara jin k'arfin jikin ki", " Mama ki mata fad'a, sam bata son cin abinci", Cewar Suraj yana tsare ta da ido, "Fetta ki rik'a cin abinci kinji, kinga yanzu bake kad'ai kike ba", Tayi nodding kai, " Ga yarinya na samo miki, zata rik'a zuwa tana taya ki aiki", Ta amsa da "Toh", tana godiya, Dan kar Hajiya taga ta mata gwaninta, ta nuna bata so, yasa ta amince da zaman mai aikin, sam bata son mai aiki, " Zan koma, tana sashena idan kina buk'atar aiki, ki aiko a kirata", "Toh" ta amsa.
Ta mik'e ta fita, Yarinyar tabi bayanta.
Suraj mik'ewa yayi ya shiga kitchen, Ya d'auko plate, Yayi serving tuwo,
Kusa da ita ya zauna, Ya ajiye plate d'in a k'asa, "Babyna zanyi feeding", "Ya k'oshi", Ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa, Ya jawota ta fad'a kan laps d'inta, Saurin sauka tayi, " Wallahi zan miki d'ure", Da kallo mai cike da takaici tabi sa, Ya d'aure fuska "Ba za'a haifar mun baby ramamme ba",
Tuwon ya d'iba ya nufi bakinta dashi, Ta kawar da kai, Yasa d'ayan hannun ya juyo da kanta, " Kina so na baki na bakina", Ya fad'a fuska ba alamar wasa, bata tanka sa ba, har ga Allah bata jin tuwo, Ganin yana k'ok'arin sa tuwon bakinsa, Tayi saurin bud'e baki,
Ya saka a bakin sa, Ya kamo bakinta ya matse ya juye mata tare da had'e bakinsu wuri d'aya, ba shiri ta had'e, "Zaki bud'e baki, ko na cigaba da miki haka", Bakin ta bud'e ya shiga bata, Zuciyarta fal da takaicin sa.