*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*11*
UNEDITEDTa cikin mota yake hango ta, yana jin tamkar ya fito ya shak'eta sai taji k'amshin lahira, Saitin shi ta tsaya tare da yin knocking glass, Ya sauke glass yana bin ta da kallo, Tasleem tamkar zuciyarta zata fasa k'irjinta ta fito, ba zata iya fassara a yanayin da taji ta ba, Son Suraj ke ratsa ta, Tayi k'arfin halin cewa "Mu shiga daga ciki",
Ba musu ya bud'e k'ofa ya fito, yabi bayanta, Tana karairaya, Falon bak'i ta nufa dashi, Ya zauna yana k'arewa falon kallon, Masu aiki suka shiga kawo abubuwan motsa baki,
Tasleem ta duk'a gaban sa, Ta tsiyaya lemo ta mik'a masa, Ya karb'a yace "Thank you amma bana shan orange juice", "Ayyah bari a kawo maka wani", "No Thank you", Sam bai yarda da ita ba, balle ya sha wani abu daga hannun ta,
Ranta bai b'aci ba, zuwan sa gidan yafi mata komai, Ya nisa yace "Ina son mutane irin ki masu nuna tausayin su ga rayuwa" Tayi murmushi tare da yin fari da ido tace "Marayu abun tausayawa ne, sun rasa iyayen su, wasu sun tashi basu san su ba, kaga ya kamata a taimaka musu", Yayi nodding kai yace "Hakane, shiyasa kika k'ara burgewa", Tayi murmushi tana jin dad'i na ratsa ta, "But babban abunda yasa kika burgeni naji ina so mu k'alla alak'a tsakanin mu shine yadda kike tsananin so na", Ta waro ido tace "Dama kansa ina son ka", Yace "Yes a jiya na sani, kuma na shaida kika tsananin so na, son da ya kai ki ga aika thugs su kashe matata da ya'ta",
Tasleem gabanta yayi mummunan fad'uwa, ta had'iye wani yawu da k'yar, tsoro ya bayyana k'arara kan fuskar ta,
"Ya dai?, ya naga kin tsorata, relax!, nasan soyayyata tasa kika aikata haka, naji dad'i da na samu mai k'auna ta haka", Ya fad'a hankali kwance, yana murmushi dashi kad'ai yasan ma'anar shi,
Ta sauke sanyayyar ajiyar zuciya tace "Ina tsoro na rasa ka Suraj, am deeply in love with you, wallahi na fad'a tarkon k'aunar ka, soyayyarka ta rufe muj ido, bana ji bana gani bana gane komai akan son ka, ka taimake ni ka aure ni", Ta kai gwiwoyin ta k'asa, Da hannu ya mata alamar ta tashi, Ta tashi ta zauna kan kujera,
"Tunda har na tako k'afa nazo gidan ku, kinsan na shirya miki something special, so taso muje", Ta mik'e cike da farin ciki tabi bayan sa, Gaban mota ta shiga ta hakimce, Yaja mota yana murmushin gefen baki.
Fetta taci kukan ta mai isar ta, Ta tashi zaune tare da fad'in "Kukan me ma nake?, akan me zanyi kuka?", Taja siririn tsaki tana share hawayen ta, "Allah ya jik'an Addani, ya bi maka hakk'in ka, Mamana Allah ya gafarta miki, Ya Allah ka tsaremu da dukkan masu sharri", Ta mik'e ta shiga toilet ta watsa ruwa, duk ta had'a gumi kukan da tayi.
Aunty Jummai taci ado cikin irin atamfar da ta ba Fetta, Bilkisu dake zaune falo tana kallo tace "Umma wannan kwalliya sai ina?", "Gidan Hajiya mana, baki ga kayan dake jikina ba", "Ohh ban gane ba wallahi sai yanzu, amma Umma kan ki naja fah", Tayi murmushi tace "Mu na wasa ne, tun duniya na kwance muke shu'uman ci", Bilkisu ta jinjina kai tace "Allah yasa yau naji labari mai dad'i", Aunty Jummai tace "Kwantar da hankalin ki zaki ji", Ta fice, Napep ta shiga, ta nufi gidan Hajiya, cike da k'udurin ganin k'arshen Fetta yau.
Suraj tunda suka shiga mota, bai sake magana ba, k'ira'ar Sudais da ya kunna yake bi, Tasleem baki ya kasa rufowa, farin ciki fal zuciyar ta tana tare da masoyin ta, har suka kawo wata unguwa mai tsirakun gidaje, layin da suka shiga gaba d'aya gida uku ne, Bakin wani madaidaicin gida yayi horn, Mai gadi ya bud'e gate, Yaja motar ciki, Cike da girmamawa mai gadi ya gaishe sa ya amsa, Tasleem babu tsoro ko fargaba a tare da ita,
YOU ARE READING
FETTA (COMPLETED)✅
RomantizmLabarin yarinya da ta taso cikin maraici da rashin gata