41

3.6K 308 20
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

*41*

*Bansan da wane baki zan baku hak'uri na tsawon lokaci da na d'auka banyi typing ba, Masu kirana da masu mun message nagode da k'auna*

  "Ki k'irga wa'adin barin ki gidan Suraj", Take ta nanatawa a ranta, Message d'in ya kasa b'ace mata, Kiran sallar la'asar da ta jiyo, Ta mik'e ta shiga toilet ta d'auro alwala, Ta gabatar da sallah tare da addu'o'i, B'acin rai da take ji ya bar zuciyar ta.

    Falo ta tarar dashi zaune, Yana kallon news, Ya d'ago kai ya zuba mata ido, Sosai yaga ta masa kyau ta k'ara cikowa, Dukiyar fulaninta kamar su fasa rigarta, wani yarr yaji a jikinsa, kwana biyu ya d'aga mata k'afa saboda lafiyar babynsa, Da hannu ya mata alama tazo, Ba musu tazo kusa dashi ta zauna, Hannu yasa ya kwanto ta jikinshi, Tana k'ok'arin mik'ewa ya sake matse ta, Ya d'an d'aga rigarta, yana shafo k'asan mararta, tsigar jikinta ya tashi,  Ta d'an ture hannun sa, " Lafiyar babynsa nake dubawa", Ya fad'a yana d'aga mata gira tare da k'ara shafowa har can k'asa cikin wani salo,

   Jikinta ya mutu lik'is, Tuni ya shiga sarrafata cikin wani salo na daban, mai rikita zuciya da gangar jiki, Ta shiga mayar masa martani ba tare da ta sani ba, Basu dawo hayyacinsu ba sai da suka samu natsuwa, sam sun manta a falo suke, Rigarta ta shiga gyarawa tana k'okarin saka zip, Yasa hannu ya tsayar da ita, Kafin tayi magana ya d'agata sama, ya nufi toilet da ita,

Gajeran wandonsa yake k'ok'arin cirewa, Tayi saurin sa hannu tana rufe fuska,

    "Bana son kilibibi yau kika fara gani, naga yanzu kika gama yadda kike so dashi", Tamkar ta nutse a k'asa tsabar kunya, Ta sake gumtse idonta, " Ni dalla bud'e ido, na cud'a ki bana son babyna ya wahala",

   Babu yadda ta iya, cike da jin kunya tayi wankan tsarki, Ya mata wanka, Ya ma kanshi, Shi ya d'aura mata towel ya d'auko ta, Ya fito da ita, ya zaunar kan dressing mirror, Ya shafa mata mai, ya shirya ta tsaf, Kunya ta hanata ce masa komai,

    Ta mik'e zata fita d'akin ta jiyo muryar sa, "Don't feel too important darajar babyna kike ci", " Kai ma darajar babyn naka yasa na bar ka", Tana fad'ar haka ta fice, Yabi bayanta da kallo, tare da yin murmushin gefen baki.

    Kitchen ta nufa, Ta d'aura girki da taimakon Shafa(Yarinyar da Hajiya ta kawo mata).

     Aunty Jummai ke ta k'urmawa cikin daji, ta tattare zani saboda ciyayi da k'aya, Tafiya take tana waige-waige ita kad'ai kamar mayya, Har ta kawo wani k'ugu,

    "Kada ki shigo da k'afar dama", Taji an fad'a da razananniyar murya, A tsorace ta mayar da k'afar dama, ta shiga da hagu, Tana ta kutsawa tazo gaban wani k'asurgumin boka, Kallon sa kad'ai ya isa yasa ka firgita, Gabansa ta durk'ushe, " An sanar dani meke tafe yake", Jiki na rawa tace "Toh"

    "Zaki kawo jinin hailar yar' ki, da zuciyar zakara da gashin jab'a", Ba tare da wani shakku ba ta amsa da " Toh", Zuciyarta ta bushe komai zata iya aikatawa dan cimma burinta, "Sai kin kawo za'a yi aiki", Ya fad'a cikin murya mai karaji, Ta mik'e jiki na rawa, Ta tafi, Jikinta duk k'aya ta isa gida, Bilkisu ta tayata cirewa tana sanar da ita yadda suka yi,

    " Umma bakya tsoro, nifa ina tsoron mu'amala da irin su", "Dallah wane tsoro, irinsu ne aikinsu tamkar yankan wuk'a, Malam tsibbun nan da yawa kud'in mutum kawai suke cinyewa", " Yaushe zaki yi al'ada nan da sati d'aya", "Allah ya kaimu", " Amin Allah yasa dai a dace", "Zama a dace", Bilkisu tayi murmushin farin ciki.

   Su'ad ce kwance jikin Adnan a cikin mota gidan k'awar ta nan suke had'uwa, " Albishirin ka", Ta fad'a tana k'ara narkewa jikin sa, "Goro fari  tass", " Mama tace na fad'a maka ka turo", Ya sake rungumota jikin shi Yace "Wooo Am soo happy zaki zama matata", Farin ciki ya sake lullub'eta ganin yadda yake murna, tasan dama zai yi murna, " Can't wait naga mun zama husband and wife", Tace "Same my love", Tana manna mishi kiss, Sai da sukayi romancing juna sosai, suka rabu, Ta koma gida cike da murna.

    Suraj ya fito daga gidan gonar sa ya biya wani boutique na kayan manya da jarirai, Kaya sosai ya siya na babies(Nace zumud'i tun yanzu)

    Bakin k'ofar fitowa yaji an buge ledar hannun sa na dama, Kayan suka zube, Da sauri ta duk'a tana kwashewa, Ta d'ago idonta cikin nashi, Yayi saurin kawar da kai gefe saboda fad'uwar gaban da yaji, " Am sorry", Ta fad'a , Ya karb'a ba tare da yace mata komai ba, "But kamar na san ka",  Kafad'a ya d'age mata yace " Maybe", Yayi gaba abunsa, Sosai taji ya burgeta,

    "Sai na aure ka Suraj, This is part of my plan", Cewar Tasleem, Ta juya ta fice daga boutique d'in, ba abu tazo siya ba, shi ta biyo daga gidan gonar sa.

    Yana parking motar sa cikin gida, wayarsa tayi k'ara alamar text message " I will always love you Sahibina", Da same number ta ranar, Yayi tsaki, Ya kwashi ledoji ya shiga cikin gida.

    Fetta na zaune k'asan carpet tana cin fara wacce tasa Shafah ta samo mata, Idonsa ne ya kai kan bowl na farar, Ledojin dake hannun sa ya saki, Ya k'arasa gabanta, "Meye wannan kike ci?", Ya fad'a yana d'aukar bowl, yana sake dubawa, " Fara", Ta bashi amsa hankali kwance, "What!", Ya fad'a a tsawace, " Are you out of my sense", Da mamaki tabi sa da kallo, "Fara kike ci, babyna kike ba wannan abun", Ya fad'a yana nufar dustbin na falon ya jefa hadda bowl d'in,

    Ya dawo saitin ta " Wannan ya zama na k'arshe, ki bari idan kin haifa mun babyna kici kyankyaso bama fara ba",

Ya wuce d'aki abun sa, Ta tsinci kanta da jin zafin furucin sa, bata san sai yaushe zai fara nuna damuwar sa a kanta, wata zuciyar tace "Meyasa zaki damu da nuna damuwar sa a kanki", Taja siririn tsaki, ta d'auki remote, Ta kamo sunna TV, ana wa'azin Malam Aminu Daurawa mutumin, wa'azin ya tafi da dukkan tunanin ta.

     Kusan awa d'aya ya d'auketa tana kallo, ta maida dukkan hankalinta wa'azin na shigar ta,

   Suraj ganin shiru bata shigo ba, Ya mik'e ya lek'a yaga lafiya, Har yazo ya zauna kusa da ita bata sani ba, Saukar numfashin sa yasa ta juyowa, Idonta cikin nasa, ya kashe mata d'aya, Ta kawar da kai ta maida kallonta ga TV.

  Gama wa'azin yasa shi mik'ewa da fad'in "Ki kwashe su ki ajiye in a safe place", Ya nuna mata ledojin da ya shigo dasu d'azu, Bai jira amsarta ba ya shige d'aki,

    Ledojin ta shiga tattarawa, Kayan babies masu azabar kyau ta gani unisex wanda maza zasu iya sawa mata zasu iya sawa, Mamaki ya kamata tun yanzu ya fara siyan kayan babies, lallai ba k'aramin so yake wa cikin ba, Da tunanin haka ta kwashe, Ta shiga d'aki ta zuba a cikin d'aya daga akwatin ta na lefe.

   " Na gaji da irin zaman nan da muke", Karima ta fad'a tana raba jikinta daga Alhaji Mu'azu, "Haba swty yanzu kin gaji dani", Ya fad'a yana sake jawo ta jikin sa,  " Ba wai na gaji da kai bane, amma me zai hana muyi aure yadda zamu fi jin dad'in juna", Sakinta yayi ya b'ata rai "Kinsan me kike fad'awa kuwa, ai ni na rufe aure, kina so yarana suce na jawo musu abun kunya, tsofai tsofai dani zan auri yarinya", " Amma baka ji kunyar aikata zina ba, ai gara kayi aure akan su san aika aikar da kake", "Kar kimun rashin kunya", " Dama akwai kunya ne tsakaninmu kana taushe ni, Toh wallahi anyi na k'arshe tsohon banza", "Nine tsohon banzan", " Sosai kuwa", Taja tsaki ta d'auki bandir na dubu d'aya da ya ajiye mata, Ta jefa jaka ta fice.

   Yabi bayanta da kallo, cike da takaici yar' cikinsa na gaya mishi magana, Shi yajawa kansa, ya mayar da kansa mutumin banza, Da k'ima da darajarsa amma sun zube a idonta, da idon duk yarinyar da ya kwanta da ita.

  Karima cikin samarinta duk wanda tama maganar aure da dalilin da yake kawo mata, wasu ma k'iri k'iri suke fad'a mata baza su iya auren karuwa ba, Tana cikin matsananciyar damuwa, Ga Kawo Sule ya k'ara jadadda mata idan bata fito da miji ba, nan da kwana 3 zai kore ta daga gidan, taje can ta cigaba da yawon iskancin ta.

*FOLLOW*
*VOTE*
*COMMENT*

*ZEELISH*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now