11

3.6K 282 2
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*11*
*Unedited*

   "Amma Bashir anyi tsinanne, yanzu cewa yayi ba cikin sa ba ne", Yelwa ta fad'a fuska ba annuri, " Baki ga rashin mutuncin da ya mana ba, cewa yayi shi bai ma san ta ba",

    Ta dungure kan Karima tace "Mai k'aton kai kamar k'odago, Kin ga abunda kika ja mana, ai sai ki zauna ki rainin cikin da babu Uba, ni na cire hannu na a lamarin ki",

   " Ni bak'in cikina, ta kore mana arzik'in da muke fatan samu", "Kasan wani yaron da k'ashin tsiya ake haihuwar sa, toh Karima nada shi", " Tabbas na yarda, kin cuce mu Karima", Yasa k'afa ya haure ta ya wuce cikin d'aki.

    Karima kuka ta fashe dashi, na takaicin irin iyayen da Allah ya bata, su bama cikin da tayi suke ma bak'in ciki ba, Fasa auren ta da Suraj wanda suke tunanin zasu samu wani abu, Haushi da tsanar rayuwar da take ciki taji.

    Labarin yabi mak'wabta Karima tayi ciki, Yaran mak'wabta sun shigo wurin su Binta, suka ji ana rikicin, Suka kwasa suka kaiwa iyayen su.

    Gidan Aunty Jummai da Kawo Sule babu nisa, gida hud'u ya raba su, Aminiyarta ce ta shigo, wacce gidan shine na uku a layin.

    "Albishirin ki Aminiya", " Goro fari tass", "Karima tayi abun da ta saba", " Kina nufin ciki?", Ta fad'a tana zaro ido, "K'warai kuwa, yanzu haka magana tabi unguwa",

    Mik'ewa tayi, tayi juyi tace " Kai Allah nagode maka, burina ya cika, ai sai ayi auren mu gani", "Ai baki ji dad'in da ya sameni ba, da labarin yazo mun", " Wallahi labarin nan yafi mun Komai dad'i, ji nake kamar an sani a aljanna", (Nace hmm daina murna rigar wani ta kama da wuta)

    Gyale da takalmi ta zura, Bata zarce ko'ina ba, Sai gidan Hajiya Tumba.

    Suna zaune falo ita da Suraj, Su Feena na gefe, Suna jefo bakin a hirar tasu.

     Aunty Jummai ta shigo, tana hawaye, Suka shiga gaishe ta babu wanda ta amsa gaisuwar sa, Sai faman jan majina da take,

   "Lafiya dai Jummai", Cewar Hajiya, " Ina fah lafiya, Karima ta jawo mana abun kunya da b'ata suna a gari", "Subhanallah me tayi?", " Ciki ta k'unsa"

    Suraj a razane yace "What Ciki! Karima", Hajiya Tumba kasa cewa komai tayi sai jikinta dake tsuma, " Wallahi ciki dan' nan", Ta fad'a tana k'ara sautin kuka,

    "Chabb Allah ya taimaki Yaya, bai jawowa kansa ba, dama daga ganin idonta sai tayi shaid'anci", Cewar Su'ad, " Shine aka so k'ak'aba mishi, Allah ya kubutar dashi", Feena ta fad'a tana tab'e baki,

     Suraj ya k'ara tsorata da lamarin mata, Kallon salihar mace yake wa Karima, Lallai tsoron Allah a zuciya yake ba fuska ba, Da yawa yan' matan yanzu sun lalata rayuwar su, Ya tsani zina ya zina mai aikatawa.

     Mik'ewa yayi da shirin barin falon, Kawo Sule da Yelwa suka shigo falo, Kallo d'aya zaka musu kasan hankalin su a tashe yake, Ganin Aunty Jummai hanjin cikin su ya kad'a, Duk saurin da suke kada ta riga su, ta iso, Suna da tabbacin ta kawo labari, daga ganin irin kallon da mutanen gidan ke musu.

    Cikin k'ask'antar da kai yace "Nasan labari ya kawo muku, amma Wallahi fyad'e aka mata, Ku....", Suraj ne ya katse shi cikin d'aga murya Yace " Fyad'e ko ba Fyad'e ba, Na fasa auren yar' ka, ba zan tab'a auren wacce da' namiji ya santa ba", Yana fad'ar haka ya fice, Matsayin sa na Yayan mahaifinsa yasa bai keta mishi rigar rashin mutunci ba,

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now