07

3.7K 311 8
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

     _*Haske writers Association*_

*07*

    *Kuyi hak'uri zaku ga na canza sunan Yar' Kawo Sule daga Aysha zuwa Karima*

    Aunty Jummai kamar an jefo ta ta shigo gidan Kawo Sule, "Ina kike bak'ar munafuka", Ta fad'a tun daga bakin k'ofa, Yelwa ce ta fito tana yatsina fuska tace " Lafiya dai?", "Ba lafiya ta kawoni ba", " Toooh Allah ya tsare mu da rashin lafiya", "Kin je kinyi makirci an had'a Karima da Suraj bayan kinsan yadda Bilkisu ke mutuwar son sa", Dariya tayi tace " Haba, ai bani da labari, Suraj shi ya Kawo kansa, ba Karima ta nuna tana so ba"

     "Ke Yelwa, da Jummai kike magana ba wata ba, Nasan halin ki tun kina k'aramar ki, kar ki manta ke raino na ce, toh wallahi baki isa ba, In dai ina raye Suraj bilkisu zai aura", " Ahayye ai sai mu zuba mu gani, tunda har uwar sa na goyon baya", "Nasan ba banza ba, wallahi ba banza kika barsu ba, amma nice nan zanyi maganin ki", Ta fad'a tana dukan k'irji, Ta fice fuuu kamar zata tashi sama.

    Hab'a ta rik'e tace " Ohh kaji ni da mata, idan ke kika raine ni to nafi ki hatsabibanci, ai sai ya auri Bilkisu mu gani"

   Suraj jefi-jefi Karima na zuwa tunanin sa, sai yayi tsaki da k'ok'arin kawar da ita, Sam bai san meye soyayya ba, Kuma baya son ya fara ta, Dan yaga yadda take wahalar da mutane, ta jigata su, Yaga yadda abokin sa ya wahala akan so, Hakan ya k'ara sa baya sha'awar ta.

      Ya fito da shirin sa na sport, Duk yamma yana fita exercise, a wani recreational centre, Muscles d'inshi kad'ai zaka kalla kasan yana body building,  sai da ya fara biyawa sashen Hajiya.

    Tana zaune tare da yaranta suna hira, Kowaccen su ta shiga gaishe shi, Yana amsawa, "Mama zan tafi exercise", " Toh a dawo lafiya, Ka kula da kan ka", "In Shaa Allah Mamana",

    Da mota d'aya ya tafi, Amintaccen driver shi na jan shi, " Ina binciken da nasa kamun akan Alhaji Bello kotangora", Ya tambayi Driver cike da isa, "Ranka ya d'ade nayi bincike komai, gashi a rubuce", Ya zaro takarda a aljihu, Ya mik'a masa, Ya karb'a yana dubawa, " Azzalumin mutum, I will soon break you down", Ya furta.

    Har suka isa wurin yana nazarin bincike da aka masa akan Alhaji Bello.

    Fetta na wanke-wanke a tsakar gida, tana yan wak'e-wak'en ta, Aliya ta fito sanye da hijabi, Tace "Zan tafi wurin aiki, Ali na ciki na bacci, idan ya tashi yayi kuka, ki kawo shi", Ta marairaice fuska tace "Da kin tafi dashi Umma, Allah bana son zuwa gidan nan", " Saboda me Fetta, gidan da kowa ke son zuwa, gidan arzik'i cikin ma ana hana mutane shiga", "Ni dai kawai Umma", " Toh ai shikenan", Ta koma ciki, ta d'auki Ali ta goya, ta fice, Hakan ba k'aramin dad'i yama Fetta ba, bata burin ta sake had'uwa da wannan mutumin mara tausayi, mugu.

    Bayan ta gama wanke wanke, Duwatsu ta samu, ta zauna tana carafke, Har Aliya ta dawo ta sameta, Ta tambaye ta taci abinci, Tace a'ah,  fad'a ta mata, tare da tasa ta gaba, taci,

    Malam ya dawo musu da gasasshen nama suka ci, Yana jan Fetta da hira, da tambayar ta kan makaranta, Tana amsa mishi.
 
    Malam sosai yake tuna mata da Mahaifin ta, Kullum addu'ar sakayya take ma mahaifin ta akan wanda suka kashe shi, da addu'ar samun rahma shi da Mahaifiyar ta.

   Yelwa ta zayyane wa Kawo Sule yadda suka yi da Aunty Jummai, "Jummai bata san kunya ba, yanzu ita Yar' ta tazo tana ma fad'an auren Suraj, saboda tsabar kwad'ayi" (a zuciyata nace kaima ai kwad'ayin yaja ka), "Hmm, kada kayi mamaki, zamanin nan kowa nasa ya sani", " Toh wallahi kada ki sake ki d'aga mata k'afa, haukar banza take, Suraj kamar ya auri Karima ya gama, gobe gobe zanje na samu Tumba ayi maganar sa rana", "Yawwa gara mu hanzarta, kasan halin Jummai kafin tayi wani k'ullin", " Barni kawai da ita", "Toh", " Kawo mun abinci", Ta mik'e ta nufi kitchen, tana jin natsuwa a ranta.

     Bilkisu da taji zancen, Ana son had'a Suraj da Karima kuka tasha, Aunty Jummai ta lallashe ta tace ta kwantar da hankalin ta, Dukkansu sun koma gidan Hajiya Tumba, Harara da yan habaice habaice suke wa juna, Su'ad da Safeena kam tsakanin su dasu ido, Suna addu'ar kada ya auri ko d'aya daga cikin su, Sunfi so ya auri Yar' mai kud'i wacce aka san babanta a k'asar nan, a ganin su bai dace da middle class ba, dan Hajiya Tumba na kwab'ar su da yadda zasu k'yamaci talaka abun ba kad'an ba, Sun manta tsatson da suka fito.

    Suraj ya had'a kayan sa a trolley a ranar zai koma Lagos, Jirginsu k'arfe 7 na safe zai tashi, Tafiyar tazo masa a bazata.

    Hajiya Tumba bata tashi ba, ya bar mata sak'on wurin masu aiki, a yar' k'aramar takarda, ya kuma mata text message, Murna sosai suke ya tafi, zasu huta.

    Convoy na motocin sa uku suka kai shi airport, 7:15am jirginsu ya lula sama zuwa Lagos.

     Hajiya Tumba bata fito ba sai k'arfe 10, da tarar da sak'on sa, Ta kira shi wayar shi kashe, Hakan ya tabbatar mata ya shiga busy, Karin kumallo tayi, Ta koma d'akin ta sama.

   Yan' matan kawai ke ta bidirin su, kasancewar yau lahadi babu lecture, Su'ad tace "Feena kalli yarinyar dake son Ya Suraj", " Wow amma ta had'u, she is classy", "Bari sister, And babanta don ne, Yana da kud'i sosai gata Yar' gayu, suna da sarauta fah", " Gaskiya da ita ya dace, Ya Suraj classy babes ne type d'in shi",

  Karima dake gefe tana jin su wanda da biyu suka yi, Taja tsaki tana mik'ewa, Su'ad tace "Ke dawa kike?" Ta juyo ta watsa mata harara tace "Da wanda ya tsargu", " Kinyi kad'an kice zaki zo gidan mu ki raina mana wayo", "Dad'inta ba zaman ki nake ba", " Zaman Ya Suraj kike ya aure ki ko, toh ki sani ba zai tab'a auren ki ba gayyar tsiya", "Da ba'a san asalin balbela ba sai ace daga misrah take, matsalar mutum yayi hayen arzik'i kenan",

    Saukar mari taji a fuskar ta, Dambe ne ya kacame tsakanin su, Safeena ta taso ta shiga, Suka kama Karima suna duka, Bilkisu ce taje ta sanar da Hajiya, Tsawa ta daka musu, suka daina, Ta shiga tambayar ba'asi, Bilkisu ta fad'a mata, Dukkan su ta had'a tayi wa fad'a sosai,

    Karima kamar mayya k'ara nad'e k'afa tayi tak'i barin gidan, Duk da irin gorin dasu Su'ad suka mata, Su kansu sunyi mamakin rashin zuciya irin nata, Bilkisu abun ya mata dad'i, ko ba komai hakan zai sa Suraj ya fasa auren ta, tunda K'annen shi basa son ta, Zasu yi ta zuga. (Nace hmm kema baki tsira ba)

   Kawo Sule ya wanko k'afa yazo, Ya buk'aci a mishi sallama da Hajiya Tumba, Bilkisu sama sama ta gaishe shi, Ta mak'e bayan k'ofa taji me zasu tattauna.

   Bayan sun gaisa da Hajiya, Ya gyara murya yace "Suraj yaje yaga Karima, kuma na fuskanci sunyi na'am da juna, toh bai kamata mu b'ata lokaci ba, tunda dukan mu a shirye muke, a zauna a saka rana", Murmushi tayi tana gyaran d'aurin ta da ya soma warwarewa tace " Yaya Sule sha'ani na aure ba'a masa gaggawa, da an bari sun k'ara fahimtar juna", "Wane gaggawa abun nan na gida ne fah, kowa yasan halin kowa", " Toh idan ya dawo zanji ta bakin sa", "Au ya koma ne", " Eh", "Da kin kira sa ta waya kinji, kinsan ya kan jima idan ya tafi", " Toh" Kawai tace masa, a ranta tana mamakin wannan hanzari da yake.

   Bilkisu da sauri ta shiga d'aki, ta kira Aunty jummai ta fad'a mata, Tace ta kwantar da hankalin ta, auren nan da ita za'ayi ba Karima ba, Taji dad'i kuma ta yarda da Mahaifiyar ta, Tasan idan tayi niyyar yin abu to sai ta cimma burinta ko ta wacce hanya.

   *Toh kowa Suraj zai aura? Ku biyo Yar' mutant sakkwato😉*

*Follow*
*Vote*
*Like*

*ZEELISH*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now