44

3.5K 288 8
                                    

*FETTA*

NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

*44*
*Unedited*

   _Am sorry kun jini shiru kwana biyu nayi tafiya ne_

   Fetta bayan ta kammala ayyukan gida da taimakon Shafah, Tayi wanka ta shirya tsaf, Early morning Suraj ya fita ana neman sa gidan marayun sa, Zazzab'in da taji na son rufe ta, Ta d'auki zamzam da Mallam ya aiko mata, tasha tare da shafawa a cikin ta, Ta k'ara da addu'o'i.

      "Assalamu alaikum Ina masu gidan?", Ta jiyo muryar Yasmeen daga falo, " Wa'alaikumus salam", Ta amsa tare da mik'ewa ta fito falo, "Maman Unborn", " Babynku na wahalar dani fah", Ta fad'a tana zama kan kujera, "Mu dai we are eager yazo duniya", " Sai kuyi ta addu'a Allah ya kawo shi lafiya", "Muna yi sai dai mu k'ara",

   Ta bud'e baki zata yi magana, mararta ta masifar murd'awa, wani zugin azaba ya ziyarce ta, tana jin tamkar marar zata cire, K'asa ta kai tare da furta " Innalillahi wa inna ilaihir raji'un", A rud'e Yasmeen tayi kanta tana tambayar lafiya, Kasa bata amsa tayi sai murd'e murd'e take, Tana karanta duk addu'ar da tazo bakin ta,

    Wayar Fetta ta jawo tayi dialing number Suraj, Yayi mamakin ganin kiranta coz bata tab'a kiran shi ba, Yayi receiving yana jin gaban sa na fad'uwa, "Fetta bata da lafiya", Ta fad'a tana kuka, Hankalin sa a matuk'ar tashe ya kashe wayar, ya d'auki mukullin motar sa ya fita har yana tuntub'e,

    Ya fisgi mota a 360, minti 3 ya kawo sa gida, Shigowar sa yayi daidai da d'aukewar numfashin ta, Yasmeen ta saki k'ara tana fad'in " Ki tashi Dan Allah Fetta kada ki tafi ki barni",

    Hankalin sa yayi mummunan tashi ganin ta kwance bata numfashi, Yayi kanta tare da ture Yasmeen gefe bai ma sani ba, Yayi kanta yana jijjigata, "Fatima ki tashi please", Ko gezau batayi ba, Iskan bakin shi ya shiga hura mata still bata motsa ba, " D'ebo ruwa", Ya umarci Yasmeen, Jiki na rawa ta d'ibo, Ya watsa mata still bata motsa ba,

    Wani ihu Yasmeen ta saki tare da fad'in "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Fetta ta rigamu gidan gaskiya", 'Bata mutu ba, wallahi bata mutu ba, zata haifa mun baby, mu rayu tare tana haifa mun wasu", Ya fad'a hawaye na bin gefen kuncin sa, D'aukarta yayi cak, Ya nufi mota, Yasmeen tabi bayan sa,

    Driver ya kira yaja su, ba zai iya driving ba, ya zauna baya rungume da ita, Yasmeen ta zauna gaba, Suka nufi asibiti.

   Ba b'ata lokaci likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa, Kusan awa d'aya suna kan ta but sun kasa gane meke damun ta, Suna da tabbacin bata rasu ba, amma bata numfashi,

    Suraj ya kasa zama sai faman zirga zirga yake a passage na d'akin, Bai tab'a shiga tashin hankali irin na yau ba, Yasmeen kam sai faman kuka take, Hajiya ce ta shigo hankali a tashe, Aliya da Mallam a bayanta, Aliya nata kuka, hijab ma a jirkice ta saka, " Ya jikin nata?", Hajiya ta tambaya, Da k'yar ya iya furta "Basu fito ba", " Allah ubangiji ya tashi kafad'unta", Duka suka amsa da "Amin"

  Babban likita ne ya fito, duk ya had'a zufa, Suraj yayi kansa yana tambaya "Ta farka, taji sauk'i?", Ya dafa kafad'ar sa yace " Relax, kwantar da hankalin ka", "Taya hankalina zai kwanta, My wife is unconscious", Dr yayi shiru cike da tausayin sa, " Likita Dan Allah ka fad'a mana wane hali take ciki?", Cewar Mallam, "Baba muma kanmu bamu san meye matsalar ta ba, munyi iyakacin k'ok'arin mu mun kasa ganewa", Salati da ambaton sunan Allah kowannen su ya shiga yi hankali a tashe, Suraj rik'o Dr yayi yace " Do your possible best please ta tashi, kada ku bari ta rasa ranta", "Dr Ameer babban likita ne zai zo yau from India, zuwa dare zai dubata, In Shaa Allah zata tashi", " Allah ya yarda", Cewar Aliya tana sharar k'walla,

    Suraj d'akin ya shiga kai tsaye ba tare da jiran umarnin Dr ba, Gadon da take kwance ya nufa, Ya kamo hannun ta cike da tausayin ta, Addu'o'i ya shiga tofa mata.

   "Zamu iya ganin ta?" Yasmeen ta tambayi Dr, Ya d'aga mata kai,

   Shigowar sa bai sa ya janye hannun sa daga rik'on da ya mata ba, Kallo d'aya Aliya ta mata, ta kawar da kai tana sharar k'walla, cike da tausayin ta.

   "Kada ki b'ata mun lokaci, shiryawa kamar wacce zata gidan gwamna" Aunty Jummai ta fad'a tana gyara hijabin ta, Bilkisu ta fito tasha kwalliya, tana rambad'a k'amshi, "Wannan kwalliyar fah", " Umma yau ranar farin ciki ce, ina so idan Ya Suraj ya ganni ya rikice", Aunty Jummai tayi murmushi tace "Ai auren ki da Suraj kamar an mayar an gama", Bilkisu tayi dariyar farin ciki.

    Basu tarar da kowa gidan ba sai yan' aiki, Su'ad da Feena sun tafi bikin k'awar su, Samee na makaranta.

   D'aya daga cikin masu aikin suke sanar dasu Fetta na asibiti bata da lafiya, Farin ciki ya ziyarci zuciyar su, Aunty Jummai ta tambayi wane asibiti, ta sanar dasu, Basu tsaya ba suka fito.

    " Dama na gaya miki aikin sa tamkar yankan wuk'a", "Na yarda wallahi Umma", Ta fad'a tana washe baki,

     A harabar asibitin suka ci karo da Mallam ya siyo ruwa, Suka gaisa, Ya musu jagora zuwa d'akin, Suraj na kusa da Fetta yak'i matsawa ko'ina, Bilkisu wani kishi taji ya tokare mata wuya,

    " Ya mai jiki?", Aunty Jummai ta tambaya, "Sai addu'a", Cewar Hajiya, " Meke damun ta ne?", "Muma bamu sani ba, duk bincike likitoci sun kasa ganewa", "Kuma ba cikin bane", " An gaya miki bamu sani ba" Suraj ya fad'a a fusace sam ya manta matsayin ta a wurin shi, Dole taja bakinta tayi shiru, zuciyar ta fal farin ciki sanin aikin su ne,

   Basu jima ba suka tafi, "Umma ni wallahi raina duk ya b'aci ya wani manne mata", " Kwantar da hankalin ki, saura k'iris zaman su tare ya k'are", Ta sauke ajiyar zuciya, haushin da take ji ya rage.

    Throughout Suraj na asibiti bai fita ko'ina ba, Magana ma baya yi sosai, Fatan sa Allah ya tashi kafad'un ta, He is eager dare yayi Dr yazo.

    Around 11:00pm Dr Ameer yazo asibitin, Fetta ce patient ta farko da zai fara dubawa, Aka umarci su Hajiya su fito d'akin,

   Har Dr Ameer ya shigo Suraj na d'akin, Ya bashi hannu suka gaisa, "Please Dr do your best ta tashi, tana d'auke da babyna, ina so yazo duniya, mu rayuwa tare", Dr Ameer yace " Babyn ka kake so yayi surviving ko Maman baby", "I need them both", " In Shaa Allah zan yi k'ok'ari, Kuyi mana addu'ar samun nasara", Suraj yayi nodding kai yana jin hankalin sa ya kwanta da Dr Ameer,

    Masallaci ya nufa, Ya shiga nafila da rok'on Allah, Su Aliya basu gaza ba wurin rok'on ubangiji.

    Dr Ameer duk yawon sa na asibitocin fad'in duniya, bai tab'a cin karo da aikin da ya bashi wahala ba kamar na Fetta, Duk iya bincike sa ya kasa gano matsalar ta, Gashi dai bata rasu ba, But sam bata motsi, Hankalin sa ya tashi, lamarin ya bashi tsoro, Tuni ya fad'a gumi, handkerchief dake gefe ya d'auka yana gogewa.

    Kusan awa biyu ya kasa fitowa ya sanar meke faruwa, Yana tausayin Suraj, a yadda na gansa bai san wani hali zai shiga ba,

    Ganin kusan awa biyu Suraj ya fito daga masallaci yana kyautata zaton Dr Ameer ya gama binciken sa, A passage yaci karo dasu Hajiya, "Bai fito ba?", " Eh", Hajiya ta basa amsa,

   D'akin ya lek'a ya hango Dr Ameer zaune yayi tagumi, Ba tare da wani tunani ba, ya bud'e k'ofa ya shigo,

   Dr Ameer ya d'ago kai ya kalle sa, yana jin tausayin sa na shigar shi,

      "Ya jikin nata?", Suraj ya tambaya, " Am sorry na kasa gane meye matsalar ta, ban tab'a cin karo da aikin da ya gagare ni kamar wannan ", Suraj bai san lokacin da ya kai k'asa ba, Ya dafe kai, Bai zai iya misalta yanayin da ya tsinci kansa ba, Tunanin sa ya tsaya cak.

    Dr Ameer k'wararre kuma shaharren likita ne da aka san shi a k'asashen daban daban, Duk rashin lafiyar ka, Allah ya bashi baiwar iya treating, Da izinin Allah yayi treating d'in ka sai ka samu sauk'i.

*Follow*
*Vote*
*Comment*

*ZEELISH*💕

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now