*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*05*
UNEDITEDYan'uwa da abokan arzik'i nata zuwa barka, Kowa yazo sai ya kawo abun arzik'i, Aunty Yelwa da Kawo Sule ma sun zo, Hajiya ganin bata ga Karima ba, Tace "Ina Karima?, kwana biyu na daina ganin ta", Mutanen dake wurin yasa Aunty Yelwa cewa "Tana gida, kwana biyu bata jin dad'i", "Allah sarki, Allah ya bata lafiya yasa zakkar jiki ce", "Amin", "Zan zo In shaa Allahu na duba ta", "Allah ya yarda", "Amin"
Professional mai lalle tazo ta tsantsanrawa Fetta ja da bak'i, ba k'aramin kyau yayi ba, Suraj already ya biya ta, a instagram yayi coming across page d'in ta, Yayi mata magana yana so tama matar shi, ba k'aramin dad'i taji ba ganin Suraj ne.
Kowa yaga lallen sai ya yaba, Yasmeen tace "Gaskiya yayi masifar kyau, kin ganki kamar wata sabuwar Amarya, Fetta yar'gatan Suraj da kanshi ya samo miki mai lalle", Ta wurga mata harara, "Kin dace miji, muma Allah ya samu a dashen ki", Wani banzan kallo ta watsa mata, Ta kamo hannun ta tace "Wallahi Fetta, Suraj yayi nisa a sonki, girman kai ne ya hana shi fitowa ya bayyana miki, a sannu zai furta, zaki ce na gaya miki", Fetta ko kad'an bata yarda da zancen Yasmin ba, ta d'auki komai da yake mata saboda babyn sa ne da Hajiya.
Tace "Uhmm yawwa ina ta so na tambaye ki, wai ya maganar case d'in su Alhaji", Yasmeen ta nisa tace "Tuni aka rufe case d'in, yan sanda sunyi bincike sun kasa gane komai", Fetta da damuwa d'auke a fuska tace "Allah yabi su Addani hakk'in su Allah ya tona asirin ko su waye", Yasmeen ta amsa da "Amin, Fetta ina tsananin kewar iyayena wani lokacin na kan ji tamkar nabi su, meyasa wad'annan mutanen basu da imani a ran su, sun tarwatsa family a dare d'aya", Ta k'arasa da hawaye,
Fetta tace "Gara ke Yasmeen kina da dangi, bani da kowa, bansan kowa nawa ba, Addani shi kad'ai ne gatana, sun rabani dashi, sun kashe shi, taya zan gane dangina?, ban tab'a jin tsanar halitta ba kamar wanda suka kashe Addani, bazan tab'a gafarta musu ba", Ta fashe da kuka mai tsoma zuciya, Yasmeen kasa lallashin ta tayi, sai ma taya ta da tayi.
Suraj tun daga bakin k'ofa yake jiyo shesshek'ar kuka, Hankalin sa ne ya tashi, ya k'arasa ciki, Yasmeen na ganin sa ta tashi ta fita, Fetta da ta kifa kanta kan cinya tana kuka, Ya d'ago ya rungume tsam a jikin sa, Har cikin ransa yake jin kukan ta, A hankali ya furta "Me aka miki?, Me ya saki kuka?", Kasa bashi amsa tayi sai kukan da ta cigaba, Lips d'inshi na k'asa ya ciza yace "Please kiyi shiru you are hurting me", bai san sanda ya furta haka ba, Fetta mamakin furucin sa tayi, Kukan ta tsagaita, hawaye na ambaliya kan kumatun ta, Ya d'ago ta yasa hannu yana share mata hawaye,
"Tell me what makes you cry?" Ya kafeta da ido, Kanta ta sunkuyar k'asa, cikin sanyin murya tace " Ina tuna Mahaifina ne, i want to meet my family", "Addu'a zaki rik'a mishi ba kuka ba", Tayi nodding kai, "Ina family naki suke?", "Nijar", "A wane gari", "Ban san komai a kan su ba, Mahaifina bai tab'a gaya mun ba", Tausayin ta yaji for the first time ya kama shi, "In Shaa Allah watarana zaki had'u dasu", Tayi nodding kai, "Ina baby?", "Tana wurin Umma", Sam bai lura da lallen ta ba, wanda shine dalilin sa na zuwa d'akin yaga mai lallen tayi yadda yace tayi.
Ya mik'e har ya kai bakin k'ofa, "Ina neman alfarma d'aya a wurin ka", Ya juyo yana kallon ta ba tare da yace komai ba, "Dan Allah a sawa baby Zainab sunan mahaifiyata", Juyawa yayi ya fice ba tare yace komai ba, Har ga Allah sunan Hajiya yake so ya saka, Fetta ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah yasa ya amince", Babban burin ta yaranta sunci sunan mahaifiyarta da Mahaifin ta.
"Wane irin aiki ne wannan da ya hana ka waiwayar gida" Kawo lamid'o ya fad'a cike da fad'a, Bello yace "Kayi hak'uri Abba In Shaa Allahu cikin satin nan zan shigo", "Allah ya kaimu", "Amin", Kawo Lamid'o ya kashe wayar tare da yin k'wafa.
Karima ta ajiye tray na abinci a gaban shi, ta zauna kusa dashi, "Cikin satin nan In Shaa Allah zanje Kano, Su Abba sun matsa a kan naje", "Allah ya kaimu", Ta fad'a murya a sanyaye, "Ya naga kamar baki ji dad'i ba", Murmushin takaici tayi tace "Ka gode ma Allah iyayen ka na neman ka, suna son ganin ka, tunda nasa k'afa na bar gida ba wanda ya k'ara nema na", Cike da tausayin ta ya jawo ta jikinsa, ya rungume, "Su Kawo na son ki, watarana zasu neme ki", Tayi murmushin takaici a ranta tasan bara su tab'a nemanta ba, basu damu da ita ba, da halin da take ciki ba, bata tab'a ganin iyaye irin su ba.
Shirye shiryen suna ake, kai kace bikin aure za'ayi, Ma'aikatan gidan nata faman aikin wasu na yanke-yanke su cabbaje, wasu na gyaran kaji, wasu na had'a zob'o da kunun aya, kowa da aikin da yake, Aliya na b'angaren masu aikin tana kula da ayyukan, wani kuma tasa hannu.
Bayan sallar magrib, Suraj ya shigo d'akin Fetta janye da akwati,
"Kayan fitar suna ne, ki gwada idan akwai wanda ya miki kad'an ko yawa, kiyi magana a mayar a gyara", "Nagode Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i da dauk'aka", Sosai yaji dad'in addu'o'in ta ya amsa da "Amin"
Yasmeen ta kira ta tayata duba kayan, Akwatin shak'e take da kaya, Laces tsadaddu guda biyu d'inkin riga da skirt stone work, shadda getzner guda d'aya d'inkin ta ya masifar yi kyau, sai atamfa super d'aya holland d'aya, da wani tsadadden material, Duka kayan charass a jikin ta tamkar an gwada ta,
"Wallahi Fetta kin more miji, ki kwanta kiyi ta bacci kawai", Fetta murmushi tayi dan har ga Allah taji dad'i sosai bata d'auka zai mata haka ba, Kwanakin nan kulawar da yake nunawa a kanta, yasa ta fara tunanin maganar Yasmeen gaskiya ce yana sonta, "Wannan ai ko matar gwamna sai haka", "Kai Yasmeen", "Wallahi Allah, Allah dai ya barku tare ya kauda shaid'anin mutum da aljani", Cikin zuci ta amsa da "Amin",
Sallamar Aunty Jummai ta katse musu hira, suka amsa a tare, Ta shigo tana washe baki, Fetta ta tsinci kanta da fad'uwar gaba,
"Mai jego ana lafiya", "Lafiya lau", "Dama na lek'o naga kina lafiya, ina jika ta?", "Gata nan", Ta d'auke ta tana fad'in "Amma ba'a mata wankan dare ba", "Eh", "Bara na mata", Ta shiga toilet ta had'o ruwan wanka, Tayi mata, ta shafe ta da cream.
Tana washe baki tace "Ina kayan da na kawo mata, ina so na saka mata naji dad'i", Fetta bata kawo komai a ranta ba, Ta bud'e akwati ta d'auko, ta mik'a mata,
Aunty Jummai cike da farin ciki ta karb'a, Overall ce pink mai kyau, ta shiga k'ok'arin saka mata.
_Bani da chaji😰_
FOLLOW
VOTE
COMMENTZEELISH💓