*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*23*
UNEDITEDKnocking k'ofar ake, ta kasa ko da k'wakk'waran motsi balle tayi yunk'urin bud'ewa, jikinta ke kyarma, bugun k'ofar ya tsananta, "Ya Hayyu Ya Qayyum" Ta furta tana mik'ewa, Da k'yar ta kai bakin k'ofa, ta murd'a mukulli, tamkar jira ake, aka turo k'ofar da k'arfi, Ganin Suraj tayi saurin ja baya kamar taga dodo, tana runtse ido, Office d'in yabi da kallo, yaga yadda ta fito masa da takardu, K'irjin sa ya doka, "Meye dalilin ta na mun bincike?" Ya tambayi kansa cike da mamaki,
"Waye kai? Meye sana'ar ka?, Ina son sanin ainihin d'abi'ar ka", Ta fad'a cikin karaji ba tare da bud'e idon ta ba, Da kallo yabi ta yana jin yadda zuciyar shi ke bugawa, "Baki da right na personal life d'ina and wa ma yace ki shigo office d'ina ki mun bincike", Idonta da suka yi jajir ta bud'e, tana kallon sa babu alamar tsoro ko shakku a tare da ita, "Ban damu da rayuwar ka da duk abunda zaka aikata ba, rayuwar ya'ta nake dubawa, mutuncina nake dubawa, kamar yadda bana fatan rayuwa da dan' fashi wanda yayi silar kashe Mahaifina",
Kalamanta yaji sun daki dodon kunnen sa, but sam ya kasa fahimtar inda ta dosa da zancen kashe mahaifin ta, "Suraj Sa'id ka fad'a mun wanene kai?, Meye had'in ka da mugayen makamai, meye had'in ka manyan mutanen da naga sunayen su?", Duk da ya girgiza da jin kalamanta ya dake yace "Ina ruwanki da rayuwata da abunda nake aikatawa, sake miki da nayi bashi zai sa ki saka kan ki cikin al'amura na ba, you should stay out", Murmushin takaici tayi tace "Ina fatan zargin da nake a kan ka kada ya tabbata, idan kuwa ya tabbata wallahi tallahi sai na mik'a ka kotun addinin musulunci inda za'a yanke maka hukunci daidai da abunda ka aikata"
"Idan kin shigo rayuwata ne dan ki tarwatsa ta kinyi kad'an, Suraj Sa'id ba zai tab'a bari kiyi nasara ba", Kallon takaici tabi sa dashi tace "Idan kana ja, ka sanar dani wanene kai?", Cikin d'aga murya yace "Dan' fashi da makami, sana'ar fashi nake, da ita na zama abunda na zama, itace sana'ar da na tara tarin dukiya, itace silar da kowa ke sha'awa ta, yake burin kasancewa tare dani, abunda kike son ji kenan, toh kinji kije ki fad'awa duniya, goo" Ya k'arasa cikin d'aga murya yana nuna mata hanyar fita,
"Dan' fashi da makami", Ke yawo a k'wa'kwalwar kan ta, Office d'in na juya mata, komai double take ganin sa, Kalaman sa tamkar saukar aradu haka taji su a dodon kunnen ta, zuciyarta na tsananta bugawa, zafi take ji a jikin ta tamkar ana hura mata garwashin wuta, hak'oran ta na karkarwa, tun daga ranar da Yasmeen ta sanar da ita, bata tab'a jin tashin hankali da firgici kamar yau da taji daga bakin sa, idonta taji suna lumshewa a hankali ta fad'i bata numfashi,
A gigice Suraj yayi kanta, yana jijjigata, Harshe shi tamkar an datse shi ya kasa furta komai, d'aukarta yayi cak ya fito office d'in a rud'e, Ma'aikatan wurin suka yi kansa, suna tambayar lafiya, bai bi ta kansu ba, Ya sakata bayan mota, Shima ya shiga, Driver da sauri ya shiga yaja mota, ko ba'a fad'a masa ba yasan asibiti zasu je,
Asibitin International ya nufa dasu, babu b'ata lokaci aka shiga da ita, Likitoci suka shiga bata taimakon gaggawa, Yaso shiga d'akin da ake treating d'in ta likitocin suka hana, Ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zirga zirga yake, yana addu'ar samun lafiyar ta, ya rasa tunanin me zai yi, kansa gaba d'aya ya k'ulle, kallo d'aya zaka masa kasan yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali.
Bello ya iso garin kano cike da k'udirin bin umarnin iyayen sa, maganun Karima sun yi tasiri a kan sa, kaso d'ari na damuwar sa, hamsin ya rage, Bai samu wata tarba daga wurin iyayen sa ba,
Kawu Lamid'o ya kai duban sa gare sa yace "Maza ka shirya yanzu ka tafi wurin Tasleem, kar na sake naji ka mata abunda ba daidai ba", Cike da ladabi ya amsa da "Toh" yana nufar d'akin sa,
Ruwa kad'ai ya watsa, ya canza kaya, Ya fesa turare shima dan yana so, ba dan zai je wurin ta, baya k'aunar sake ganin ta, dole ce kawai zata sa, Shigowar text d'in Karima ya katse masa tunani "Ina fatan Mijina ya sauka lafiya, kuma ina fatan baya tare da wata damuwa, ba zai bari wani abu ya b'ata masa rai ba", Yayi murmushi yana jin k'aunar ta na ratsa shi, Ya mata reply mai cike da kalaman soyayya.
Tasleem ta fito tana yanga, Bello dake zaune kan kujera a falon, ko kallo bata ishe sa ba, har ta zauna, "Sannu ko", Ta fad'a, "Yawwa, ya mutanen gidan?", "Lafiya", Ta fad'a tana tsare sa da ido, kyawun sa take gani duk da bai kai Suraj ba, kyan ya mata, Lemo ta tsiyaya a kofi ta mik'a masa, sip d'aya yayi ya ajiye, Tana ta jan sa da hira, bai jima ba yace zai koma akwai wurin da zai je, Ya karb'i number ta, ta masa rakiya har bakin motar sa, Ya tafi yana tunanin yadda zai yi rayuwar aure da yarinyar da baya jin ko d'igon son ta.
Dalelliyar mota ta sauke Bilkisu bakin gidan su, ta bud'e murfin seat na baya ta fito, Hajiya Rabi tasa a maidota gida bayan sun gama shek'e ayar su,
"Kin dad'e Bilkisu, tun d'azu nake jiran ki, kizo muje yima Hajiya Allah sanya alkhairi an sa ranar Feena", Cewar Aunty Jummai, Ta tab'e baki tace "Ba sai munje ba Umma, dan kawai ansa mata rana", "Ke dalla mara wayo kissa ce ai, hakan zai sa taji dad'i", Bilkisu mamakin makirci da kissa irin na mahaifiyar ta take, Gyale ta cire, ta kasa hijab, Aunty Jummai dama da shirin ta, Suka nufi gidan Hajiya.
A falo suka sameta ita da Feena suna lissafin abubuwan da za'a siyo, Aunty Jummai tana washe baki ta shiga zuba addu'a da nuna farin cikin ta, Bilkisu ma tayi addu'ar Allah ya sanya alkhairi, Hajiya ta amsa su da sakin fuska, Feena kam sama sama ta amsa su, Hajiya tace "Bilkisu yaushe za'a k'ara yin aure?", Aunty Jummai tayi saurin cewa "Kowa yazo sai tace bata so, ita dai Suraj", "Allah sarki", Hajiya ta fad'a tana d'auko wani zancen, Aunty Jummai ba haka taso ba, dan Boka ya fad'a mata Hajiya ta kanta zata ce Bilkisu ta koma gidan Suraj.
Idonta ta bud'e a hankali, tana jin yadda kanta ya mata nauyi, da kallo tabi d'akin, hakan ya tabbatar mata asibiti ne, drip dake sak'ale a hannun ta, ta fisge, Bata buk'atar kulawar kowa a yanzu, Ciwon dake zuciyarta ya girmi asibiti, idan zata shekara anan baza su mata maganin komai ba, Saukowa tayi daga kan gado, ta d'auki hijabin ta dake gefe ta saka, Ta fito d'akin tana jin jiri na d'ibar ta, tamkar zata fad'i, Suraj dake bakin k'ofa yayi saurin tasowa ya nufo ta,
Da hannu ta dakatar dashi, "Kada ka kuskura kazo kusa dani", Ya sake matso ta yana fad'in "Ina zaki je baki da lafiya, ki koma kada ki jawowa kan ki wani ciwo", Bata saurare sa ba, ta rab'a gafen sa zata wuce, yayi saurin shan gabanta, yana k'ok'arin rik'e ta, Taja baya tana fad'in "Kada ka tabani, kada ka sake yunk'urin hana ni fita daga asibitin nan", Ganin idan ya tsaya jayayya zaat tara musu mutane, yaja gefe,
Taka k'afarta take ba tare da tasan ina take nufa ba, natsuwa sam baya tare da ita, Har ta kai bakin gate, tsintar kanta tayi da tarar napep ta masa kwatancen gidan Suraj,
Suraj tana fitowa yabi bayanta, ganin ta shiga napep, ya shiga mota yabi bayan su, Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke ganin gida aka sauke ta,
Tana shigowa, Samee ta fito daga b'angaren Hajiya rik'e da Mimi nata kuka, "Tun d'azu take ta kuka, an bata madara tak'i dainawa", Karb'ar ta tayi ba tace komai ba, Ta rungume ta, Mimi shiru tayi kamar ba itace ke kuka ba, ta nufi b'angaren Suraj tana jin tsana da k'yamatar gidan da duk abunda ke cikin sa,
Tana ganin kiran Yasmeen tak'i d'auka har ya tsinke, Bata buk'atar magana da kowa a halin yanzu, bata buk'atar shawara kowa, zuciyarta zata bi, bata son duk wani da zai hana mata aiwatar da kud'urin ta,
Suraj babu natsuwa a tare dashi ya shigo, ganin ta falo tsaye rungume da Mimi, ya sauke ajiyar zuciya a zaton sa tana b'angaren Hajiya, ta sanar da ita waye shi, baya k'aunar abunda zai d'aga hankalin Hajiya ya jefata a damuwa, meyasa ya bari Fetta ta shigo rayuwar shi, da yasan haka zata kasance ba zai tab'a sake mata ba, ta yadda zata yi bincike a kansa, Fetta ta katse masa tunani, takarda da biro ta ajiye a gaban sa, "Ka rubuta mun takardar ta", Ta fad'a tana masa kallo mai cike da tsana.
FOLLOW
VOTE
COMMENTZEELISH💓