*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf*43*
*Unedited**Wannan page naku ne yan' clevers writers saboda k'aunar Ku ga littafin nan One love💕*
Bilkisu ta tashi da ciwon mara wanda take kyautata zaton zuwan al'adarta da suke matse yazo dan cikar burin sa, Gwaggo sai faman lek'owa take tana tambaya yazo,
Fitowar Bilkisu daga toilet kenan, ta tsaftace jikinta da ya soma b'aci, "Yazo ne?" Gwaggo ta jefa mata tambaya, "Eh", "Mashaa Allah, ina zuwa"
Cikin minti biyu ta dawo d'auke da k'aramar kwalba ta mik'a mata "Karb'a ki zuba ciki", Ta karb'a tana nufar band'aki.
Fetta ce tsaye jikin madubi, cikin shigar doguwar riga wacce ta kama jikinta ta zauna mata daram, Cool perfume ta d'auka ta fesa, bata son mai hawa kai, amai yake sata.
Hannun taji saman cikinta da ya fara tasowa (yau watan shi biyu da sati biyu), Idonta ta sauka kan hannun wanda ta tabbata Suraj ne, Ta jikin madubi yake kallon ta, Ba k'aramin kyau ta masa ba, Yayin da yake k'ok'arin hana kansa ganin kyan.
Cikin ya cigaba da shafawa cikin wani salo, Saitin kunnen ta ya mata whispering " Hope babyna na lafiya?", Kai ta d'aga masa sakamakon kasalar da ya saukar mata, K'ok'arin janye jikinta take, "Ina zaki ban gama gaisawa da babyna ba",
Ya dawo ta gabanta, ya duk'a ya sumbaci cikin, " My baby zan fita, sai na dawo", Ya kamo hannunta ya d'aura saman cikin ya sumbata, Ya mik'e ya fice, Tabi bayansa da kallo, Tare da sauke kasalalliyar ajiyar zuciya.
Gidan gonar sa ya nufa, Ya fito cikin shigar sa ta kamala da takun sa na k'asaita, "Oga akwai d'aukar wanka", Cewar wani ma'aikaci, D'ayan yace " Allah ya bamu danshin su", "Amin"
Yazo gaf dasu, suka rissina suka gaishe shi, Ya amsa da sakin fuska, "Ranka ya dad'e gashi akace na baka", Ya fad'a yana mik'a masa wata k'aramar jaka mai azabar kyau, Ya karb'a ba tare da yace komai ba.
Shigar sa office, Ya bud'e yaga me ye a ciki, Turare ne designer, sai flower da card mai d'auke da kalaman soyayya a k'asa an rubuta " From Your Sahiba", Tsaki yaja ya jillar da kayan gefe, Wayarsa ta d'auki ruri,
Yayi receiving, "Manyan k'asa" Cewar Jabir(Abokin business d'in sa) "Ai kune manyan", " Ku dai da kuka yi wuyar gani", Suraj yayi dariya yace "Ya harkoki?", " Alhamdulillah, An shigo da new model da motoci yaushe zaka shigo ka duba?", "Ai JB ina ga ka turo mun ta yawa na gani, sauran abubuwa kuma ka duba mun, shigowa ta Lagos ba yanzu ba", " Wane uzuri ne haka sai hana ka, kai da nasan baka wasa da neman kud'i", Ya fashe da dariya yace "Personal issue", " Toh Allah ya tabbatar da alkhairi", "Amin", Sukayi sallama yayi hanging up,
" Ina Karimar take?", Kawo Sule ya fad'a cike da fad'a, Ya hankad'a k'ofar d'akin ta ya shiga, Yelwa ta biyo bayan sa, Karima dake shirya Abdul ta mishi wanka, Tace "Gani Baba", " Ina Mijin da nace ki kawo", "Baba kayi hak'uri, wallahi kowa baya son aurena", " Dallah rufe mun baki, ba zan zauna da k'atuwar budurwa kamar ki cikin gida ba, a gari ana zagina ana cewa na ajiye karuwa, ki tashi ki tattara kayanki ki bar mun gidana, duk ranar da kika kawo miji kizo na miki aure",
"Dan girman Allah Baba kayi hak'uri, idan ka kore ni bansan ina zan je ba", " Cikin kwartayen ki d'aya ya kama miki gida, kuyi dadiro", Kuka sosai take tana rok'onsa yak'i sauraren ta, Uwa da ya' sai Allah, Yelwa tausayin yar' ta ya kamata , Tace "Kayi hak'uri a k'ara bata lokaci", A fusace yace " Ba zanyi hak'urin ba, sau nawa ina bata lokaci", Zata sake magana ya katse ta, "Kika sake magana wallahi a bakin auren ki, zaki bi ta", Dole tayi shiru cike da tausayin ta, Ya tasa ta gaba yace ta bar d'akin.