*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf*Haske writers Association*
*04*
K'arfe sha biyu da minti biyar daidai ya farka da sunan Allah a baki, Mik'ewa yayi ya shiga toilet, Wanka ya fara yi, Yayi brush, Ya fito, Cikin minti 15 ya shirya cikin wata arniyar shadda light blue, Ta matuk'ar amshi jikin sa, kuma ta mishi kyau.
Dining area ya nufa, Yayi serving kansa potato chips da egg sauce ya fara ci, Wayar sa tayi ringing, Murmushi yayi ganin farin cikin sa ce, Ya danna receive, tare da saka handsfree, "Mamana ina kwana?", " Lafiya lau Yaron albarka, ka tashi lafiya?", "Lafiya lau", " Naji ka shiru ne, na kira naji lafiya", "Am fyn Mamana, gani nan zuwa da na gama breakfast", " Toh sai kazo"
Yayi hanging up, Yana murmushi, Bai had'a mahaifiyar sa da kowa ba, Yana tsananin k'aunar ta.
Ya gama ci, yasa tissue ya goge baki, Ya fito zuwa sashen Hajiya Tumba.
Anty Jummai kamar zata kifa k'asa wurin gaishe sa, "Ina kwana Alhaji Surajo", Rai a b'ace ya kalle ta yace " Bana son irin gaisuwar nan da kike mun, matsayin mahaifiyata kike fah", Sam baya son irin gaisuwar nan da take masa, wanda yasan duk akan abun hannun shi ne take haka.
"In banda abun ka ai durk'usawa wada ba gajiya bane", Ta fad'a tana dariya, " Ni dai na rok'e ki da Allah ki daina", "Toh na daina, Allah yayi albarka", Ya amsa da "Amin"
Gaban mahaifiyar sa ya duk'a ya gaisheta, Ta amsa tare da shafa kansa kamar kullum, Zama yayi k'asan carpet, Hajiya Tumba ta nisa tace "Dama batun taimakon da aka saba kai was gidan marayu duk wata, lokaci yayi", " Ohh na manta gaba d'aya" Ya fad'a yana d'an dafe kai, "Akwai ka da mantuwa kamar wani tsoho", Yayi murmushi yace " Gobe In Shaa Allah za'a kai", "Allah ya kaimu, Ya k'ara arzik'i", " Amin"
Anty Jummai dake gefe tace "Akwai wasu marayu kusa damu, suna buk'atar taimako wallahi", Suraj yasan ba wasu marayu, ita ke so a bata kud'i ta cinye, Hannu ya saka a aljihu ya zaro bandir na 500, Ya ajiye gabanta yace " Gashi ki basu", Ta shiga zuba godiya, "Allah ya biya ka dan' albarka, Allah ya jik'an mahaifin ka", " Amin", "An gode an gode"
"Mamana zan fita cikin gari, ina so na duba shaguna naga ya suke tafiya", " Allah ya bada nasara", "Amin"
*Asalin su Suraj*
Marigayi Sa'idu Mai kasuwa shine miji a wurin Hajiya Tumba, Haifaffan garin kano ne, bafullatani d'an garin shanono, Mutum ne shi mai tsananin hak'uri da halin dattako, Sana'ar trader yake, Yana da k'aramin shago da yake siyar da kayan provision, Da sana'ar yayi aure har ya haifi yara hud'u, Suraj ne babba sai Su'ad, Safeena da Sameera autar su, Suna zaune cikin rufin asiri da matar sa Tumba,
Marigayi Sa'idu gidansu su 7 ne kuma cikin su shine bashi da k'arfi sosai, Dan haka suka k'aurace mishi komai basa shawara dashi, basa ma zuwa gidan sa sai dai shi yaje nasu, Bai tab'a nuna musu wani abu ba, Suraj tun yana k'arami abun na matuk'ar k'una masa rai yadda ake ware su cikin dangi.
Yana shekara 17 Allah yayi wa mahaifin su rasu, bayan yayi yar gajeruwar rashin lafiya, Daga lokacin suka fara d'and'ana wahalar rayuwa, da ganin tsantsar k'yamata wurin dangin mahaifin su, Sa'idu ya rasu bai bar musu komai na gado ba, Itama Tumba danginta ba masu k'arfi bane, Iyayenta sun dad'e da rasuwa,
Suraj ya fara fita kasuwa yin aikin k'arfi, shine d'aukar kaya, tuk'a barrow da sauran su, Yan' kud'in da ya samu dashi suke siyan abinci suci, Allah yayi shi yaro mai son neman nasa sam baya son raini, shiyasa baya shiga mutane, magana ma wahala take masa, Mutane da yawa kance ya cika fad'in rai,
Watarana suna zaune tsakar gida, Su'ad da Safeena suka shigo suna kuka an koro su daga makaranta basu biya ba, Cike da damuwa Tumba tace "Kuyi hak'uri ku daina kuka", Suraj ne ya daka musu tsawa " Dalla ku rufewa mutane, kukan me zai k'ara ko ya rage", Suka yi saurin yin shiru, sun san halin sa yanzu jikin su zai gaya musu.
D'aki Tumba ta tashi ta shiga, Ta saka hijabi ta fito, Suraj ya kalleta yace "Mama ina zaki je?" "Zan je gidan Sule na rok'e shi rancan kud'i na fara sana'a, idan na samu riba sai na biyasa, na cigaba da juya saura", " A'ah Mama kada kije, kinsan halin su kada su wulak'anta ki", "Rance zan karb'a, ba kyauta ba", Ya mik'e yace " Muje na raka ki"
Bayan ta gama fad'a masa buk'atar ta, Ya tura hula gaban goshi yace "Naji buk'atar ki, sai dai maganar gaskiya ba zan iya baki ba, dan bani da tabbas na zaki biya, kuma lalurori sun mun yawa", " Haba Yaya Sule yanzu dubu goma ai na dauka ko kyauta zaka iya bani", "Toh ba zan bayar ba, nace ba zan bayar ba, wani ya tayani neman kud'in", A fusace Suraj ya rik'e hannun mahaifiyar sa yace " Tashi mu tafi", "Eh ku tashi ku fad'i, shegen yaro mai mugun fad'in rai, dama talaka da fad'in rai, kayi zuciya mana kayi kud'i ka taimaki uwar ka, Dan' jakar uba"
Ransa ya kai matuk'a wurin b'aci banda kasancewar sa Yayan mahaifin sa ba abunda zai hana ya mayar masa magana,
Haka suka dawo gida rai ba dad'i, Tumba nata hawaye, Ya shiga share mata, "Ki daina kuka Mamana, In Shaa Allah sai na d'aga darajar ki, zan kula dake da k'annena ta yadda kowa zai dinga sha'awar ku da sun rab'ar ku, Dangin Abba sai sunzo suna neman taimako wurin ki", Murmushi kawai tayi, ba dan ta kama zancen sa ba, tana ganin abu ne da ba zai tab'a yiyuwa ba, A ina zai samu wannan arzik'i, A duniyar da ta zama kowa nashi ya sani, ramin kura daga ke sai yaran ki.
Suraj ya k'uduri a ransa zai nemi kud'i, Yayi arzik'i sosai da zai d'aga darajar mahaifiyar sa, Sati biyu ya jera yana aikin k'arfi sosai, Har ya tara kud'in motar zuwa Lagos, Da ya sanarwa mahaifiyar shi k'udurin shi na tafiya, Taso hana shi, Yayi k'ok'arin lurar da ita, har ta amince.
Ranar da zai wuce har tasha ta rakasa tana masa addu'o'i da fatan alkhairi, Ya tafi cike da kewar gida, Suma ya barsu da kewa.
Suraj ya shiga lagos da k'afar dama, zuwan sa kenan ya had'u da wani Alhaji hamshak'in mai kud'i, Ya jawo sa a jiki, Ya yaba da hankalin Suraj haka yasa, ya jefa shi cikin sana'ar sa ta kasuwanci na siyar da motoci, Lokaci d'aya Suraj ya kud'ance, Ya gina makeken gida, ya d'auke mahaifiyar sa da k'annen sa suka koma can, A lokacin ne dangin mahaifin su suka fara rab'ar su, Ba k'aramin kulawa yake ba mahaifiyar sa da k'annen sa ba, duk abunda suke buk'ata yana musu.
Yaba k'annen shi kyawawan tarbiya, Mutum ne shi mai zafin rai, miskilanci, Shekararsa 27 amma sam mace bata gaban sa, bai tab'a soyayya ba, dan bata cikin tsarin sa. Duk da matan dake nuna zalama a kansa, Wanda yasan ba dan Allah suke son shi ba, Sai dan kyawon sa da abun hannu.
Shagunan sa yake zagayawa yana ganin yadda suke gudanar da kasuwanci (Na sana'ar siyar da wayoyi da electronics).
"Suraj ne wallahi", Wata matashiyar budurwa ta fad'a tana nuna shi, " Wane Suraj?", "Mai gidan marayu fah, wanda yake taimakawa gajiyayyu da zawarawa wanda ake nunawa a TV", " Ohh" ta fad'a tana kallon saitin da ta nuna mata, "Wallahi shine kuwa, muje mu masa magana", " A'ah nikam bana son ya wulak'anta ni ance yana da girman kai", Tsaki taja tace "Duk fad'in mutane ne, mai girman kai ne zai dinga taimakawa al'umma", Taja hannun ta suna nufar wurin shi,
D'auke kai yayi tamkar bai gansu ba, " Ina wuni?", D'ayar su ta fad'a, "Lafiya", Ya amsa ba tare da juyo ba, Ya kalli d'aya daga cikin masu tsaron shagon yace " Attend to them, customers ne", Yana fad'ar haka ya fice abun sa,
Ya barsu tsaye cike da zafin rai "Kinga abunda kika ja mana ko, ya yarfa mu, mune yaran commissioner amma mun zubar da class d'in mu", Kasa cewa komai tayi, Suka yi hanyar fita, " Yan mata kun fasa siyayyar ne", Harara ta juyo ta watsa masa, Ya fashe da dariya a ransa yace "Shine daidai da irin ku mata masu rawar kai"*Kuyi managing wannan, Bani da lafiya ku sani a addu'a*
*Follow*
*Vote*
*Like**TEAM FETTA*💕