*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*28*
UNEDITEDFetta sun dawo garin Agadez cike da kewar mutanen Niamey, sun so ta k'ara musu ko sati d'aya, Amanukal ya nuna yana buk'atar dawowar ta, da alk'awarin zata rik'a zuwa musu akai akai, Tasha alkharai mai yawa wurin dangin mahaifiyar ta, Sanah ma ba k'aramin alkhairi suka mata ba.
Azagas tasa an shirya musu abinci kala kala, kai kace wata babbar bak'uwa ce, Fuska d'auke da murmushi tace "Tanti wannan abinci haka ai da kala d'aya ma ya isa", Hararar ta tayi tace "Ba a gidan sarauta ba, kuma yar gatan masarautar", Tayi dariya tace "Bara nayi wanka da sallah", Sanah tace "Nikam sai na fara cin abinci", Azagas tace "Ke ai dama acici ce", Suka yi dariya.
Suraj kwanaki bakwai yayi su ne cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali, baccin sa ragagge ne, ya rasa meke masa dad'i, Kullum aikin sa ya d'auki hoton Mimi da Fetta yayi ta kallo, Ya rasa dalilin da yake son kallon na Fetta, gashi tunanin ta ya kasa barin k'wakw'alwa da zuciyar sa,
Kwance yake d'akin sa shiru, ya lumshe idon sa, cikin sa na masa kukan yunwa but baya jin zai iya saka wani abu a ciki, Wayar sa ya lalubo ya kunna karatun Qur'ani yana saurare ko zai samu natsuwa a zuciyar sa.
Tasleem tasha ado cikin wata arniyar gown, hannun ta da k'afafun ta sun sha adon k'unshi ja da bak'i, kallo d'aya zaka mata kasan Amarya ce, Tsaki taja a karo na ba adadi, Ta kalli Sophy ta dake gefe "Ni fah na soma gajiya da jiran sa, wane irin ango ne zai bar Amarya na jira", "Kiyi hak'uri maybe wani uzuri ya tare sa", Ta sake jan tsaki tana hard'e hannayen ta a k'irji tare da jingina jikin motar dake harabar gidansu Sophy, Anan ta shirya mai makeup tazo ta sameta kasancewar gidan su mutane sunyi yawa,
Tsinkayo motar ango ta k'ara b'ata rai, ita a dole sai yaga fushin ta, Abokin sa ne ya fito daga motar yace "Tuba muke Amarya, tela ne ya mana wulak'anci bai kammala d'inkin ango ba", Ta sauke ajiyar zuciya da yin murmushi tace "Har nayi fushi", "Ayi mana hak'uri", Ta jawo hannun Sophy tace "Mu tafi"
Sophy ta shiga gaban mota, Tasleem ta shiga baya, Bello yana zaune fuskar sam ba annuri kamar ba ango ba, Kallo d'aya ya mata yayi faking smile, ya juya ya cigaba da danna wayar sa, Kwata kwata baya farin ciki, babu telan da ya b'ata musu lokaci, shine baya ra'ayin zuwa, sai da Kawu Lamid'o yaci masa mutunci, Ya shirya yazo.
Gagarumin kamu aka yi a ranar, Bello murmushin dole kawai yake, but idan ka mishi kallon tsaf zaka fahimci babu walwala a tare dashi.
Feena gyaran jiki sosai ta shiga yi, Da kanta tacewa Hajiya ta samu mai mata gyaran jiki, Hajiya mamakin rawar kai irin na Feena take, Komai sai tace da kanta zata yi, tun tana mata fad'a har ta zuba mata ido.
"Umma sati d'aya fah kenan amma shiru kake ji, daga Hajiya har Suraj babu wanda ya nemi mu", Cewar Bilkisu fuska d'auke da damuwa, "Me kike ci na baka na zuba, zasu nemi mu", "Ni dai gaskiya ba zan iya jira ba, zan fara neman sa da kaina", "Toh ai shikenan"
Ta mik'e ta nufi d'akin ta, Wayarta ta d'auka, ta kai kan number Suraj, ba tare da wani tunani ba ta danna kira, shigowar kiran ya katse karatun Qur'anin da yake saurare wanda yake jin natsuwa a hankali na saukar masa, ya bud'e idon sa dake masa yaji tsabar rashin isasshen bacci, Ganin bak'uwar number ya danna reject, wani kiran ya sake shigowa, rai a b'ace ya d'aga,
"Hello Ya Suraj ina wuni?" ta fad'a tana kashe murya, "Lafiya", "Dama na kira ne na maka jajen abunda ya faru Allah ya kyauta gaba", "Amin" bai jira ta sake cewa komai ba, ya kashe wayar,