*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*53*
*Unedited*Bai zarce da ita ko'ina ba sai gidan da Yelwa ta same shi, Da taimakon Dan' bala suka fitar da ita cikin mota, D'aki suka kai ta, suka kwantar kan gado, Ya umarci Dan' Bala ya fita, Kayanta ya shiga tub'ewa, hadda pant da bra d'inta sai da ya cire, Allura ya mata, idonta suka bud'e, ta zama mutum mutumi ba uhmm ba a'ah, hotona ya mata, Ya tub'e kayansa, boxer kad'ai ya bari, Ya rungomuta ya musu hoto tare.
"Sorry Hajiya Jummai", Ya fad'a yana dariyar mugunta, Kayanta ya mayar mata, Ya saka nashi, Ya kira Dan' Bala ya taimaka mishi suka fitar da ita zuwa mota,
Bakin gidansu ya ajiye ta, Yaja motar ya bar unguwar da sauri,
Kusan minti biyar da ajiyeta, babu wanda ya wuce balle ya ganta, A hankali ta dawo hayyacin ta " Wayyo Allah, me Sahabi yamun?", "Me kike anan waye kuma Sahabi?", Taji muryar mijinta kamar daga sama wanda dawowar sa kenan, Tayi saurin tattara natsuwarta tace " Ba kowa, ka dawo sannu da zuwa", Da kallon tuhuma yabi ta, Ya wuce ba tare da ya amsa ba, Ta sauke ajiyar zuciya ganin bai yi insisting on knowing ba, tabi bayansa.
Yelwa na kitchen na had'a miya, wayarta dake gefe tayi alamar shigowar message, Da sauri ta jawo wayar ta duba, hotonan Sahabi ya turo mata, ta bud'e,
"Ka biyani Sahabi, lokacin ramuwa yazo, ba'a tab'a Yelwa yar' gidan tabawa a kwana lafiya, sai na hana miki farin ciki Jummai"
"Yaushe zai turo ne a saka rana, bana so a d'auki lokaci ba tare da aurar daku ba, idan bai shirya ba, a mayar masa da kayan sa a nemi wani", Cewar Hajiya, " Mama cikin satin nan In Shaa Allah zai turo ", (Ta fad'a dan Hajiya tayi shiru), " Toh Allah ya tabbatar da alkhairi", "Amin"Ta juya kan Feena "Ke kuma kada ki yarda na sake miki maganar tsayar da miji, ina sane da samarin da kike kulawa, ciki ki fitar da d'aya, bana son shashanci", Tayi nodding kai, " Ku tashi ku bani wuri", Suka mik'e rai ba dad'i.
Bilkisu na kwance d'akinta kan katifa suna chatting da Zulaihat wacce duk hirar batsa ce, Taga an turo mata message da sabuwar number, Ta d'auka wata ce da suka had'u yau sukayi exchanging number, cikin rawar jiki ta bud'e, Hotonan da ta gani suka matuk'ar d'aga mata hankali, Ta saki wayar, "Um...ma d..a sa...h...a..bii, na shiga uku wayyo Allah na",
Ta fito ta nufi d'akin Aunty Jummai, " Why Umma, meyasa zaki yi haka?, da auren ki?, ban tab'a zaton zaki aikata haka ba", "Ke dan ubanki kinsan me kike fad'a?", " Umma me ya kai ki mu'amala da Sahabi?", "Sai yau kika san ki tuhume ni akan Sahabi, Kinsan duk wata alak'a da nake dashi dan ganin kin koma gidan Suraj ne", " Shine zaku aikata alfasha irin wannan? ", " Dan ubanki wacce alfasha?"Ganin bata fuskanci me take nufi ba, Ta koma d'aki ta d'auko wayarta,
"Meye hakan?", Ta fad'a tare da nuna mata hoton, " Na shiga uku na lalace, sharrin da Sahabi zai mun kenan, me na masa ya zab'i cutar dani ta wannan hanyar", Ta durk'ushe a wurin tare da d'aura hannu saman kai, "Da baki je wurin sa ba, ai ba zai muku hoto tare ba", " Wallahi ba da sanina ba, mamaya ta yayi", "Taya?", Ta zayyane mata abunda ya faru,
" Allah ya tsine masa albarka, me kika mishi zai cutar damu haka?", "Tsorona hoton nan yaje wurin baban ki", " Ta Baba mai sauk'i ne zaki iya fahimtar dashi mutanen duniya fah", Aunty Jummai tace "Na shiga uku ni Jummai", " Ki kira shi Umma mu rok'e shi, idan kud'i yake buk'ata mu bashi", Aunty Jummai ta jawo wayar ta tayi dialing number sa a kashe, "Shikenan na mutu na lalace wayyo Allah na", (Nace dama addu'a kika yi, da kin samu sauk'in ubangiji).