*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOURZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers association*_
*26*
UNEDITEDSautin k'ararrawar da Azagas ta danna, ya fargar da ita tunanin da take, Masu mata hadima ne suka shigo su hud'u, suna gurfanawa gabanta tare da kai mata gaisuwa, Fetta ta kalla tace "Taso muje", Ta mik'e tabi bayan ta, hadiman na take musu baya, har sashen Amanukal na yanzu, Fetta sakin baki tayi tana kallon had'uwa da tsaruwar shi, an narka dukiya ba kad'an ba, sai taga na Azagas ba komai ba ne, Kai tsaye suka shiga ciki ba tare da neman iso ba,
Ganin Azagas hadiman sa suka fice, Mai martaba da yasha ado cikin kayan sarakunan buzaye, yasha nad'i wanda baka ganin fuskar sa sai idon su, Ya gaishe da Azagas, ta amsa, Fetta ta zuba masa idanu tana so tasan waye ya zama sarki bayan tafiyar mahaifin ta, Ibrahim yazo mata a rai, but ganin yadda ya gaishe da Azagas cike da girmamawa yasa zuciyar ta shakku, ko ya canza daga halayyar sa na shekarun baya,
"Fetta ce yarinyar dan' uwan ka Gabdullahi", Cewar Azagas, "Tun shigowar ku naji a jikina Fetta ce, tsawon shekaru ba zai sa na kasa gane ta ba, k'aunar da nake mata mai girma ce", Azagas ta jinjin kai, ta juya kan Fetta tace "Elhidir ne yayan Mahaifin ki", Idanu ta zaro tana mamaki sanin bashi da lafiya, yaushe ya warke har ya zama sarki, Azagas ta katse mata tunani "Kina mamaki ko?", Ta gyad'a kanta,
Azagas ta numfasa tace "Bayan tafiyar Gabdullahi mun shiga tashin hankali ba kad'an ba, na dad'e kwance ina ciwo, mutanen gari ma sun girgiza da jin b'acewar sa, wanda da yawa suna zargin k'urciya aka masa, hakan yasa aka jinkirta da nad'in sarauta zuwa wata biyu ko Allah zai sa ya bayyana, Lele ta kasa hak'uri ta shiga ruwan bala'i kan a nad'a Ibrahim ba za'a jira dawowar sa ba, Kowa yace sam bara ayi haka ba, ganin an rinjayeta ta shiga cewa ni na had'a makirci, ciwon da nake na k'arya ne, ina bak'in cikin nad'a d'an ta Sarki, ban bi ta kanta ba, ciwon dake damuna da rashin Gabdullahi yafi komai ci mun zuciya,
Ganin ciwon nawa kullum gaba yake, Sule k'anin marigayi ya d'auka mun malami, A lokacin Elhidir na tare dani, kallo d'aya ya masa yace an masa sihiri shiyasa yake haka, Sule ba tare da wani ja ba, ya yarda kuma ya bashi damar ya karya sihirin, Nan take ya shiga aikin, kullum ana masa ruqiya da basu magunguna masu d'auke da ayoyin Allah, Cikin ikon Allah sati d'aya Elhidir ya warke ya dawo cikakken mutum, farin cikin hakan yasa na warke, kowa a masarautar yayi mamaki da al'ajabin warkewar sa, Lele ta shiga tashin hankali mara misaltuwa,
Aka yanke shawarar nad'a sa Sarkin Agadez, dama shine magaji, Ranar da aka nad'a yayi kukan farin ciki da mamakin hikima ta ubangiji, babu wanda ya tab'a zata Elhidir zai gaji sarautar Agadez, Lele kusan haukacewa tayi, Ibrahim har da kwanciya ciwo, ko a mafarki basu tab'a zato ba, Zakaran da Allah ya nufa da cara.....
Sati biyu da nad'in sa, Ya auri yarinyar Sule mai suna Kabidat, yaran su hud'u tare yanzu, biyu maza Abutalib wanda yaci sunan marigayi, Gabdullahi sunan mahaifin ki, biyu mata Safa da Sana,
Fetta mamaki da al'ajabi had'e da farin ciki yasa ta kasa furta komai sai jinjina kai take, Da hannu ya mata alama ta taso tazo kusa dashi,
Rungumeta yayi yace "Maraba da dawowa ahalin ki, nayi matuk'ar farin cikin sake ganin ki", Fetta k'aunar sa taji na ratsa ta tana jin sa tamkar Addani d'in ta, Ya sake ta yana fad'in "Ina dan'uwana da matar sa?", "Sun rasu" Cewar Azagas, "Innalillahi wa inna ilahir raji'un" Ya shiga maimaitawa yana jin hawaye masu d'umi na wanke fuskar sa, wanda tunda ya hau sarauta bai tab'a zubar dasu ba, Labarin da Fetta ta bata, ta sanar dashi, Yaji tausayin ta ya kama shi sosai, Ya kuma d'auki alwashi bata kula da gata wanda bata tab'a mafarkin samu ba.