*FETTA*
NA ZEE YABOUR
ZeeYabour@Wattpadd
In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf_*Haske writers Association*_
*20*
Jin shigowar Aliya, Tayi saurin share hawaye, Aliya ta zauna gefen katifa kusa da ita, "Fetta tashi muyi magana"
Ta tashi zaune tana sunkuyar da kanta k'asa dan kar ta fuskanci tayi kuka, "Meyasa kika amince da auren Suraj bayan ba so kike ba?", Cikin sanyin murya tace " Ina so, har zuciyata na amince ", " Meyasa ki kuka?", "Ina tunanin rabuwa daku ne", " Fetta ki gaya mun gaskiya, idan bakya son auren nan, ba wanda zai miki, bana son kiyi auren da babu soyayya a ciki, bashi da dad'i", Ta had'iye miyau da take jin su tamkar ruwan zafi a mak'oshin ta tace "Na amince Umma, kada ki damu", Ta sauke ajiyar zuciya tace " Allah ya tabbatar mana da alkhairi, zanje nan mak'wabta", "Sai kin dawo",
Aliya na fita, wasu hawaye masu zafi suka wanke kuncinta, " Meyasa kika amince da mutumin da bakya so, Mutumin da a ko da yaushe kyara da hantara ce tsakanin ku, Mutumin da baya ganin girma da k'imar talaka, Ya d'auka kud'i sune komai" Zuciyar ta ta fad'a mata,
"Bani da wata mafita, bazan iya k'in amincewa da k'udurin Hajiya Tumba ba", Ta fad'awa kanta, Mik'ewa tayi, Kanta na sarawa, Ta shiga toilet ta d'auro alwala, Ta fara gabatar da nafilfili tana rok'on Allah ya kawo sanadin da za'a fasa auren, Ta amince da auren shi ne ba dan zuciya, ruhi da gangar jikinta naso ba, Taya zasu yi rayuwa a inuwa d'aya da mutumin da bata so wata alak'a na had'a su.
Hajiya tumba ta koma gida cike da murna, Fetta ta amince da auren, ita kad'ai ce fargabar ta, Suraj baya tsallake maganar ta, Jira take gobe ya dawo ta sanar dashi.
Fetta na danne damuwarta a gaban su Aliya, but deep inside her heart, Bak'in ciki, damuwa da tashin hankali ne cunkushe, Aliya ta lura da sanyin Fetta, but ta d'auka zullumin rabuwa dasu ne kamar yadda ta fad'a, Itama hakan take ji, Fetta ta zama part of them.
Da ta sanarwa Mallam ya kira Fetta Ya tambayi ra'ayin ta, Tace " Ta amince", Yayi addu'ar Allah ya tabbatar da alkhairi.
A daren bata runtsa ba, Faman juyi take kan gado, Ta rasa ina zata ranta taji dad'i, Cikin satin nan ta had'u da jarabawa guda biyu, wanda suka jefata a cikin matsananciyar damuwa, Rabuwarta da Mu'azzam tafi mata sauk'i akan auren Suraj, Mu'azzam zata iya manta shi, Suraj fah rayuwa ce ta aure zasu yi, wanda tayi imani ba rayuwa ce mai dad'i ba, watak'ila ma ya saketa idan har ya amince da auren nata, Addu'ar ta Allah yasa kada ya amince.
Yasmeen shiru tana ta jiran kiran Fetta, taji haushin rashin karb'ar number ta, Kayan ta kalla tace "Maybe bata buk'atar su, gobe sai a kai su gidan marayu na gaji da ajiya"
Suraj ya rasa dalilin da yasa wannan karan baya d'okin zuwa Kano kamar ko da yaushe, Yaran sa ja baya suka rik'a yi dashi ganin baya cikin good mood.
Kamar ko da yaushe, bayan yaci abinchi yayi wanka, ya huta, Ya fito da shirin gym, Hajiya ta buk'aci ganin sa.
Ya zauna a gaban ta k'asan carpet, "Suraj", Ta kira sunan sa in a serious tone, " Na'am", "Kayi auren farko wanda bashi da bambamci da baka yi ba", Ya gyad'a kai, " Ana auren mace da kyawun halinta da natsuwar ta wanda su na hango maka a tattare da Fetta, ina so ka cika mun burina na auren ta, na tabbatar ba zaka yi da na sani ba",
Mugun fad'uwa gaban sa yayi, Zufa ta karyo masa, Da k'yar ya iya cewa "Mama please ki bar zancen nan, haka Bilkisu na aure ta, a k'arshe ga muguwar d'abi'ar da take", " Halin Bilkisu da Fetta ba d'aya ba", "Haka kika ce akan Karima da Bilkisu, Mama meyasa kike son had'a ni aure da wanda basu dace dani ba, Bilkisu na aure ta a matsayin ta na yar'uwa ta, Wannan da kike son had'a mu fah, yar' mai aiki"