02

3.1K 307 24
                                    

*FETTA*
*Kashi na biyu*
NA ZEE YABOUR

ZeeYabour@Wattpadd

In dedication to
Zainab Mohammed Yusuf

_*Haske writers association*_

*02*
UNEDITED

   Ita ta fara fita daga motar rik'e da basket na abinci, Jane tayi saurin karb'a a hannun ta, Suraj ya fito rungume da babyn , Key na motar ya jefawa d'aya daga cikin ma'aikatan yace idan sun gama kwashe kaya yayi locking.

    Fetta toilet direct ta nufa, ta tub'e kaya, ta fara wanka, Gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, wankan da tayi asibiti bai gamshe ta ba,

    Suraj motsin ta yaji a band'aki, ya kwanta kan gado tare da d'aura baby kan k'irjin sa, Cikin minti biyu bacci ya d'auke sa, dama bacci ne sosai a tare dashi.

    Fetta ta fito ta kai dubanta gare su, ta girgiza kai, ta shirya cikin kayan bacci, ta kwanta gefen su, in less than 5mins bacci ya d'auke ta.

    Bilkisu kullum sai ta duba Suraj a facebook da instagram, whatsapp tuni ya dad'e da blocking d'in ta saboda messages da take damun shi, ganin haka yasa bata mishi a facebook da IG amma duk post da zai yi sai ta kalla.

    Tana zaune tsakar gida tare da Aunty Jummai wacce duk ta rame ta fige, ba damar ta fita sai ta samu masu nuna ta, ana zund'en ta hakan yasa ta rage fita idan ba ta kama dole ba.

    Wayarta take faman latsawa tana tauna chingum kamar tsohuwar karuwa, Ta kai kan hoton jaririyar da Suraj yayi posting, K'irjinta yayi mummunan bugawa tace "Umma Fetta ta haihu", Aunty Jummai ta mik'e zumb'ur "Da gaske?", "Wallahi kinga hoton yar' ya saka a facebook", Tamkar an soketa da kibiya haka taji wani bak'in ciki ya soko zuciyar ta, "Umma mu kashe yarinyar nan kinga yadda yake nuna farin cikin sa, ina tsoro na rasa Ya Suraj"

    "Kwantar da hankalin ki ba zaki rasa shi ba, ai zasu dawo ba can zasu tabbata ba, dole ta daina numfashi a doran k'asa, wannan karon har uwar zan had'a", Bilkisu ta fad'a jikinta tace "Ki taimakeni Ummana Dan Allah wallahi ina masifar k'aunar Ya Suraj", Ta shafa bayanta tace "Kamar kin koma gidan Suraj kin gama", Bilkisu a ranta tana fatan hakan, da tafi kowa farin ciki.

   Kukan baby ya tashe su lokaci d'aya, Fetta tasa hannu ta d'auke ta, Ta shiga breastfeeding d'in ta, Suraj wayar sa ya jawo ya duba time, 10mins pass 7, Yayi salati ya mik'e yana mamakin irin baccin da yayi, Toilet ya shiga ya d'auro alwala, Ya gabatar da sallah.

    Babyn ta koma bacci, Ta tashi zata shimfid'e ta, Ya mik'o hannu alamun ta bashi ita, Ta mik'a masa, murya k'asa k'asa tace "Ina kwana?", "Lafiya", Ya amsa kamar dole, Ta tab'e baki ta shige toilet.

     Wayar sa ya jawo yayi kira, "Hello Sir", "Ya maganar ticket na 9ja da na maka", "Sir za'a samu amma sai nan da 1 week wasu sunyi booking since", Tsaki yayi yace "Ina so in less than 2days zanyi doubling kud'in da suka bayar", "Ok Sir", Yana kashewa, kiran Hajiya ya shigo, Yayi rejecting, Yabi kiran,

     "My mum ina kwana?", "Lafiya lau My son, Ya kwanan jikalle?", Yayi dariya yace "Alhamdulillah gata tana bacci", "Toh Mashaa Allah, Ina Maman ta?", "Tana toilet", "Yaushe zaku dawo, ya kamata ku dawo da wuri saboda wankan jikalle da ita kanta Fetta", "In Shaa Allah zuwa jibi, "Allah ya kaimu ya dawo daku lafiya", "Amin Mum", "A shafa mun kan jikalle", "Ok Mum", Yayi hanging up

   Shi ba ma dan wankan baby ba, Hankalin sa ya karkata 9ja tunda yaga ana attempting guduwar mishi da baby, duk da 9ja d'in ma akwai mak'iya masu harin babyn tun kafin tazo duniya, Zai yi iya k'ok'arin shi wurin kare yar' shi, "No harm will come to you my baby" Ya fad'a tare da sumbatar ta.

   Fetta ta fito daga wanka, tana goge jikin ta da toilet, Kallo d'aya ya mata ya kawar da kansa, "She is always glowing tana k'ara kyau", Ya fad'a a ransa, wata zuciyar tace "Ba dole ba ta samu hutu", Ya katse tunanin yace "Zo ki d'auke ta ki mata wanka", "Ban iya ma babies wanka ba", Wani banzan kallo ya watsa mata yace "Wankan baby har wani abu ne, oya zo ki d'auke ta kafin ranki ya b'aci"

   Ganin tilasta mata zai yi kuma ita har ga Allah bata iya ba, Ta shagwab'e fuska tace "Wallahi Allah ban iya ba", Yaja tsaki yace "Ragguwa, i wonder yadda kika haihu nasan sun sha raki", "Naji dai, tunda har na haihun" Ta fad'a tare da murgud'a mishi baki, "Wallahi zan zubar miki da hak'ora", Sanin k'aramin aikin sa ne, Tayi shiru ta d'auko cream tana shafawa,

   Bath na wankan yara ya d'auko ya zuba ruwan d'umi, ya d'auko sabon babies ya ajiye, Ya d'auki baby ya cire mata kaya, Yana sata cikin ruwan ta tsala ihu, yayi saurin cire ta, "Sorry my little angel", Kamar tasan abunda yake cewa tayi shiru, Ganin tayi shiru ya d'auki sabulu, ya goga mata, ya mayar cikin ruwa, santsi yaji yana neman sakinta ta nutse cikin ruwan, yana ta k'ok'arin rik'e ta, tana k'ara sub'ucewa, ya tsorata hankalin sa ya tashi, gashi sai tsala ihu take, Fetta na gefe na dariya,

   Suraj duk ya had'a zufa, ya santsi ya hana shi fitar da ita cikin ruwa, da ya d'agata zata koma, Fetta ganin idan ta k'yaleshi babyn zata iya nutsewa cikin ruwa, Tazo ta d'auke ta, Tana mishi dariya, Ajiyar zuciya ya sauke,

    Ganin tana mishi dariya ya wani maze kamar ba shi ba, "Ke lafiya zaki d'auke ta, kince baki iya ba, ina mata kuma zaki hana", Wata dariya ta sake fashewa da ita tace "Kana mata me, ko dai kana k'ok'arin nutsar da ita cikin ruwa"

    Ya d'aure fuska tamkar bai tab'a dariya ba "Wallahi zaki fuskanci hukunci, Suraj baya d'aukar raini", Yana fad'ar haka ya fice d'akin,

    "Borin kunya" Ta fad'a tana dariya, Jane ta kira ta kama mata, tana watsa mata ruwa ta mata wanka, Ta shirya babyn ta fito d'ass da ita, So cute kamar ka sace ka gudu.

    Suraj falo ya koma yayi breakfast, ya jawo system d'in shi yana dubawa, "What!" Ya fad'a da k'arfi, Wayar sa ya jawo yayi dialing number yaron sa Sabeer, Bugu d'aya ya d'auka, dama yana jiran kiran ogan nasa,

    "Sabeer me nake gani?", "Wallahi Sir", "Shut Up Useless naga ka fara sa wasa ko, kana so nayi smashing head d'in ka", "Kayi hak'uri Sir" "Make sure you clear the mess kafin na dawo" Yana fad'ar haka ya kashe wayar tare da buga k'afar sa.

    Fetta tunda ta shiga labour bata k'ara bi ta kan wayarta ba, sai yanzu ta d'auka taga missed calls na yasmeen sunfi a k'irga, Tayi dialing number ta, Sai da ta kusa tsinkewa tayi picking,

   "Hmmm Nasan matsayina ace kin haihu sai dai naji a gari", "Kiyi hak'uri k'awata wallahi sai yanzu na d'auki wayar, kinsan haka kawai bazan k'i sanar dake ba", "Naji yanzu dai kiyi pics na babyna ki turo mun shi zai sa ki wanke kanki", "An gama", Tayi hanging up

   Cikin minti 15 tayi ma baby pics ta tura mata, Sai ga kiranta ta whatsapp call, "Wow wallahi babyna so mashaa Allah kamar ta d'aya da babanta ko kad'an bata biyo ki ba", "Naji", "Ni dai ku dawo 9ja, can't wait to hold my baby", Kiran da taji yana mata yasa ta kashe wayar.

    D'aukar babyn tayi ta fito da ita, ba bacci take ba, Tun daga bakin k'ofa yake kallon su, wani kyau yaga sun mishi abun burgewa, kamar ya tashi ya rungume su, ya maze, Tazo gabanshi ta d'aura mishi ita kan cinya,

   Turaren ta mai sihitaccen k'amshi ya daki hancin sa yasa shi lumshe ido, bai san lokacin da ya kamo hannun ta ba, Ya bud'e idonshi cikin nata, ba wanda ya iya kawar da kansa, Wani abu suke ji game da juna da ba zai fassaru ba,

    Kusan minti uku suna haka, K'arar wayarshi yasa suka farga, tayi saurin janye hannun ta, ta juya, ta shige kitchen.

   Noodles ta dafa, ta had'a tea, ta gaji da cin abincin masu aikin, Dining table ta zauna tana ci, Suraj na satar kallon ta, Yau wani irin kyau yaga ta mishi.

   Tasleem gaba d'aya ta kasa natsuwa, kwata kwata bata runtsa ba, Breakfast da Fauzy ta kawo mata ta kasa ci, "Frnd wai meke damun ki ne?", "Ba komai", "A'ah tun jiya da daddare na lura akwai abunda ke damun ki", "Kar ki damu", "Shikenan tunda ba zaki gaya mun ba, zan tafi lectures", "Ok" Ta fad'a ba tare da ta d'aga kai ta kalle ta ba,

     "Ban tab'a neman abu na rasa ba, dan haka bazan fara akan ka ba Suraj", Ta mik'e tana zagaye d'akin.

*FOLLOW*
*COMMENT*
*VOTE*

*ZEELISH*💖

FETTA (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now