*Assalamu alaykum brothers and sisters I am back again with a romantic, secret and funny love story....*
Hope you people will enjoy it💡
🔊🔊🔊SANARWA 🔊🔊🔊
Duk Wanda yasan idan ya karantamin littafi zai kalleni a matsayin yar iska kada ya sake ya karanta, idan kuma ya karanta ya zageni to gaskiya ban yafeba❌*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM......*
*INA MIKA GODIATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA DAYA BANI IKON DAD'A KAWO MUKU WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA* 🎀ŞΔR̃₣ŘΔŽ🎀
Ina rokon Allah daya bani ikon gamawa Lapia 🙏(ameen)
ALLAH KAYI DADIN TSIRA GA MANZONKA ANNANBI MUHAMMAD (S, A, W)
ALLAHUMMA SALLI ALA MUHAMMAD, WA'ALA ALI MUHAMMAD, KAMA SALLLAITA ALA IBRAHEEM WA'ALA AHLI IBRAHEEM, INNAKAHAMIDUN MAJEED,
RABBANA ATINA FIDDUNYA HASSNA WAFIL AKHIRATI HASSNA WAKINA AZABANNNARR 🙏🙏🙏🙏🙏🙏
🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀1
*Written matar Rasheed*🖋
MADARASATUL TAHFEEZUL QUR'AN WA TARBIYATUL AULAD.........
🚶🏻♀Cikin makarantar na shiga, ban zarce ko inaba sai stairs,
Hawa stairs d'in nayi zuwa azuzuwan dake sama.
Ajin farko na kalla naga an rubuta *kisa'i Auwal* a Saman kofar Ajin, na biyu ma an rubuta *kisa'i sani*, na uku kisa'i salees.......
Haka Dai nayita wuce azuzuwa Dayawa ko wanne da sunanshi a sama.
Yawancin azuzuwan akwai malamai aciki Wanda babu kuma xakaji suna surutu sama-sama
Saida nazo Ajin karshe sannan na tsaya.
Cikin Ajin nakalla : gaba dayansu manyane, domin daga y'an sha takwas zuwa ishirin da uku za'a iya samu.....
Abinda yafi bani mamaki shine sunfi kowane aji surutu......
Saman Ajin na kalla naga an rubuta "(IBN KHATHEER)"
kubiyo bayana donjin labarin wadannan 'Daliban
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨Wani kyakkyawan saurayine Wanda shekarunshi baza su wuce ishirin da daya zuwa da biyu ba, zaune yake akan kujerar da'aka tanada Don zaman malamai ya d'ora 'kafa d'aya kan d'aya ya karkace hular dake kansa wadda daka kalla zaka gane mai tsadace......
"Wallahi malam Abdullahi (shugaban makarantar) ya rainamu kuma ya Raina mana wayau, yarasa malaman dazai ri'ka kawo mana sai 'yan 'kunanan yara?!
Mufa ba yara bane anymore domin Kaf cikinmu babu under 18yrs🔞, kuma naga ko a United States d'an 18yrs yanada right ⚡balle a 9ja....
Sannan kuma dukanmu babu Wanda ba'a university yakeba......
ni abinma dayafi 'konamin rai shine maimakon ari'ka kawo mana malamai Maza sai a rika kawo mana mata, jifa wadda ta tafi ancemin ko shekara ishirin da uku dakyar in zatakai.
Dad'a gyara zama yayi "to wallahi ni kuma inanan duk wadda aka kawo saina koreta daga ajinnan.......
Raf raf raf 👏👏👏👏y'an Ajin sukad'au tafi, wani saurayine Wanda bazai wuce shekarun na farkonba ya mi'ke...
"Wow gaskiya safraz ka birgeni sosai, kuma duka abubuwan daka fad'a gaskiyane, muma kuma bazamu ta'ba watsa maka 'kasa a idoba....
kuma komai zakayi we are behind you and we will always support you dude.....
Mikewa daga kujerar safraz Yayi "badai yau akace za'a kawo mana Wata malamarba? To kabarni da ita kugani ko sati biyu baxatayiba zata gudu da kafarta...
y'an ajinne suka dad'a d'aukar tafi 👏👏👏yey safraz Muna godia.......
wani seat 💺 dake gefe ya karasa ya zauna, A'kidatul Islam ya bud'e yana karantawa....
his face look very innocent Kamar bashi bane tagama shakiyanci yanzuba.
Abdul ne ya zauna a kusa dashi "abokina kana muraji'a ne?
murmushi safraz Yayi eh Abdul, so nakeyi na haddaceta duka.....
dariya Abdul yayi "abokina ga brain ga iskanci "
tafawa sukayi 👋 sannan yaci gaba da karatun shi........
"Assalamu alaykum"
Wata siririyar murya sukaji tayi sallama a Ajin
Dasauri suka d'ago suna Kallonta, sanye take da dogon light blue d'in hijab har kasa sannan kuma fuskarta sanye da niqab.
Idonta 👀ne kawai a Waje ta 'bulin niqab d'in...
Atare suka Amsa "wa'alaikumussalam"
gefen white board d'in dake manne a jikin bangon Ajin ta matsa "sunana NAWAZ MUHAMMAD" ni aka turo a matsayin wadda zata ri'ka yi muku QUR'AN da fiqhu .
KUTUMAR UBAN CHANN.... cewar safraz, amma idan ka kalleshi zaka rantse bashi yaceba domin ya maze.....
cewa tayi "waye yamana ashar a ajih?
dukda y'an Ajin sunsan Wanda Yayi amma sai sukace "malama zagi kuma?
gaskiya mudai bamujiba.
shiru tayi sannan taci gaba "to yanzu inaso Kowa ya mike ya fad'a min sunanshi domin musan juna.....
babu musu suka mimmike suka fad'a......
"to Alhamdulillah, yanzu wace sura kuke?
had'a baki sukayi duka Abdul yace RUM fatima tace QASAS, zainab tace AL IMRAN , safraz yace ANKABUT,
Osman yace BAQRAH......
cewa tayi "to to to ya Isa, kuna nufin Kowa surarshi daban?
had'a baki sukayi Eh malama!
Kujera taja ta zauna "to babu komai Insha Allah zaku sameni me hakuri da sau'kin Kai, Abu d'ayane banaso shine idan na koyawa mutum karatu yacemin be iyaba.... Sannan kuma inaso muhad'a kammu domin tsintsiya d'aya bata Shara....
ESTÁS LEYENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...