🎀🎀SARFRAZ 🎀🎀
3
Matar Rasheed
Safraz ne ya fito rikeda wasu takardu,
Daddy ya naga ka tashi a dining d'in?
"nakoshine shiyasa, Amma anjima saikazo ka kuma bani koh?
Bata fuska safraz yayi, gaskiya dad baka koshiba, duka duka spoon nawa kaci?
Dad yace "Allah nakoshi ,anjima zan kara ai.......'bata fuska safraz yayi "shikenan dad ga takardun "
Cewa Yayi to my handsome zauna anan mana....
Zama safraz yayi kusa da dad...
"safraz kasan wadannan takardun meye ❓
"no dad ban saniba''
Dad yace "kakardun filin Dana siyan maka last year ne, shine da yake an gama ginin last week,
Nakai aka yimin na gida....
Murmushi safraz yayi "to dad nagode and I am very very grateful, thanks once again....
dad yace " mention not my dear, ai ka wuce komai agurina....
Mum sai murmushi take tana jin dadi.
E Eh eemm"gyaran murya dad yayi "fabulous yaushe zaka kawomin macen daka zabarwa 'ya'yanka?
Safraz yace dad ban ganeba?
Dad ya kuma cewa"i said when will you introduce the lady you choose for your kid's, to me ❓😢dad nifa nace Don Allah Adena wannan maganar domin ban Isa aureba....
Mum ce ta marairaice fuska "haba sweetheart, d'an Allah kayi hakuri mana, pls ka yarda kayi auren kai kanka zaka fi samun natsuwa da Lapia...Mikewa safraz yayi "nidai gaskiya bazanyi aure ba, fisbilillahi shekaruna 24 Taya zan iya ri'ke mace❓
dad yace haba fab kada Kace haka mana, nifa Lapia nake nemar maka, ko kafiso kayi tayin ciwo Kamar zaka mutu?
hanyar dakinshi yayi ko bi takan zancen dad beyiba "nifa narigada nasan cewa a gidannan an dena kaunata, yaza ayi ace Nayi aure at this age of mine??
D'aki ya shiga yafada kan bed Yana Ta faman zancen zuci.....a falour kuma dad ne yake cewa mum "nifa abin yaron nan ya Fara bani tsoro, ace mutum baya tausayin kanshi,,,
idan ciwon cikinshi ya tashi Kamar zai mutu Amma ana naiman mishi sauki shi baya nemarwa kanshi...
mum tace "abinda za'a yi Alhaji shine kadaina yamishi maganar aure kwata kwata, domin na lura bayaso..
come on shut up " idan ya mutu fah?
kinsan dai abinda likita yace koh?
Mum tace "Allah ya baka hakuri Alhaji, wai dama ni bacin ranshine banaso......
Alhaji yace "my dear ai bakiyimin laifiba, fitinar Yaronne take damuna......
to Alhaji abinda za'a yi shine muyi ta addu'a insha Allah zamu dace, "domin addu'a'u sinanil mumin.......
murmushi yayi "to madam muje ki had'a min ruwan wanka........WAYEE SARFRAZ ❓
Alhaji muhammad (mahaifin safraz)
kanuri ne d'an asalin garin maiduguri
Yakasance shi kadai mahaifinshi ya haifa namiji saboda yayanshi bakwai amma duka matane shikadaine na miji....
Yana yiwa matan aure a shekara sha shida zuwa sha takwas
Amma sai yace tunda Muhammad namijine zaiyi karatu mai tsawo,
To Muhammad yanada kokari sosai, hakan yasa mahaifinshi yaje gurin chairman d'in yankinsu ya neman mai scholarship, Dayake yasan Manyan y'an siyasa .....
an kuwa dace ya samu Amma a Pakistan.......
lokacin tafiya tazo suka tafi...
yanata karatunshi cikin kwanciyar hankali har ya hadu da Wata bapakistaniya yar ajinsu..
sun shaku sosai da ita har soyayya Ta kullu tsakaninsu...
sai Bayan dasuka kusa gama makarantane mumtaz (wato maman safraz take cemai ita batasan iyayentaba a gidan marayu ta taso, batada Kowa....
hakan data fad'a yasa ya Kara jin kaunarta ga wani tausayinta daya mamaye zuciyarshi
achan aka daukeshi aiki a wani company Dayake Engineering ya karanta....
sanda ya dawo Hutu ya sanar da mahaifinshi labarin mumtaz shima ya tausaya mata sosai hakan yasa ya Kara karfafawa Muhammad gwuiwa.....
Bayan Kamar Wata bakwai akayi bikinsu....
zama suke Lapia domin babu me bukatar tashin hankalin Dan uwanshi.....
ana haka mumtaz ta samu ciki, murna gurin Muhammad babu magana shida danginshi domin duka suna kaunar mumtaz....
sunzo Nigeria sukayi Wata biyu,
basu dade da komawaba nakuda ta kama mumtaz.....
asibiti yakaita sannan ya Kira y'an uwa ya fad'a musu,
mumtaz Tasha wahala domin kwana uku tana nakuda amma bata haihuba duk da likitocin Dake Kai kawo a kanta.....
hakan ba karamin tararwa da muhammad hankali yayi ba.....
kullum Yana cikin sallah da addu'a....
a ranar dasu mamanshi suka sauka mumtaz ta haifi danta namiji.........
sai dai me😭😭 ita kuma Allah ya karbi ranta.......
kuka gurin muhammad ba'a magana domin cewa yayi bazai kuma aureba, kuma duk sanda ya Kalli yaron (sarfraz) sai yayi ta kuka domin da mumtaz yayi kama, babu ta inda ya barta....
Cewa Yayi aikinma yadena....
Haka suka koma Nigeria.....
Duk Muhammad ya lalace ko magana ma baya sonyi
yarinyar wajen Kanwar babanshi wato kareemah itace tunda suka dawo daga Pakistan sarfraz yake gurinta, hakanan Allah ya Dora mata so da wata irin kaunar yaron, domin ko kuka Yayi yanzu hankalinta zai tashi watarana har tayashi takeyi....
ganin irin kaunar data keyiwa sarfraz yasa umman Muhammad takirashi ta bashi shawarar cewa ya aure ta
domin tasan zata kula dashi da kuma d'an shi...
Da farko Fir Muhammad yaki amincewada auren kareemah Amma daga baya Sai ya amince.
anyi biki Lapia kuma suna zaune Lapia babu Wata Matsala,
Hakurin kareemah yasa Ahankali sonta yarika shiga zuciyar Muhammad....
haka rayuwa tacigaba,
sarfraz kullum cikin soda kauna ake nuna mishi..... domin Koda da wasa betaba sanin cewa ba kareemah (mummy) bace ta haifeshi saboda ita tsakani da Allah takesonshi .......
sarfraz ya taso irin mai ga'ba ga'ban jiki, ga Tsawo ga fad'i ga kuma wani irin kwarjini da Allah yayi mishi
Yana zuwa citizen success academy
Sannan kuma Yana zuwa HAYATUL ISLAM WA TATBIYATUL AULAD da yammah idan ya dawo daga boko...
akwaishi da farinjini hakan yasa duk inda ya shiga sai ya zama star kafin yabar wajen.

VOCÊ ESTÁ LENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...