*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*55*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Gaishesu haidar yayi cikin sakin fuska don a tunanin shi patient aka kawo mishi,
Kicin kicin da rai baban yaron yayi tare da cewa "niba gaisuwa ta kawoniba, gurin baƙinka nazo.
Cike da mamaki haidar yace "me baƙi na zasuyi maka?
"Nazo ne su faɗa min abinda yasa suka kamamin ɗana sukayi mishi wannan ɗanyen dukan Kamar sun kama ɓarawo.
Murtuke fuska haidar yayi don yaga alamun rainin wayau a lamarin, shidai yasan sarfraz be taɓa dukan waniba, a dai abarshi da tsokanar fada da shiga sharo babu shanu, idan kuma tayi ƙamari shine ya haurawa Mutane cikin garden yayi barnar fruit Yadda yaga dama.
A yaushe su baƙin nawa sukayi mishi wannan dukan? Haidar ya tambaya don tabbatar da zargin su da yake yi nason shiryawa SARFRAZ sharri.
"Ko cikakkiyar minti talatin ba'a yiba, don yana zuwa gida ya faɗa min mukayo nan.
Wata dariyar rainin hankali haidar yayi "sannu da ƙokari, to ku sani ƙaryarku bata samu shiga ba Saboda Ni Na dawo dasu cikin gidan nan da hannuna kuma tunda suka shiga ɗakunan su basu fitoba domin Yanzu haka barci ma sukeyi, kuma koda ma ba barcin sukeyiba babu Yadda za'ayi su fita waje saboda na rufe ƙofa da mukulli..
Cikin Muryar kuka yaron yace "Wallahi shi ya bigeni.
Shidai haidar cewa yayi "na gama magana, domin Babu Yadda za'ayi yara basuyi abuba ace sunyi, dayaga Kamar basu yarda ba sai ya shiga ciki ya taso SARFRAZ ya tawo dashi.
Koda SARFRAZ yagansu saida zuciyarshi ta buga, amma dayake cikakken ɗan basaja ne sai ya maze beko nuna alamar rashin Gaskiya ba.
"Sarfraz inaso ka kalli wannan yaron dakyau, shin ka taɓa ganinshi?
"Gaskiya ban taɓa ganinshiba! Wani abunne ya faru? Cewar sarfraz cikin dakiya.
Girgiza Kai haidar yayi "you see ni dama nasan basu bane, kawai Idan zaku tafi ku tafi ni zan shiga gida inada abin yi, rantse rantse yaron ya Fara yi tare da cewa "baba na rantse da Allah shine ya bigeni, Allah ba karya nakeyi ba. Shi dai baban yaron ganin abinda ya faru sai ya yarda Cewa ba SARFRAZ bane, dakawa yaron tasawa yayi tare da cewa "Wuce muje! Nasan kila Wasu ka tsokana sukayi maka haka, shine Ni zaka zo kamin karya donka haɗani da makwabcina.
Shikam sarfraz Har ya ƙosa yaje daki don yaba bandi labarin cewa yaudai haidar ya shigammusu faɗa.
Shi kuma haidar mayar da kofar yayi ya rufe tare da wucewa nashi ɗakin...
Aikam SARFRAZ na shiga daki ko zama beyiba ya fara ba bandi labarin abinda ya faru, harda kwatanta wa bandi yadda yaron yake rantsewa, shi ko bandi babu abinda yakeyi inbanda dariya...
Hassu kumi tuni barcin gaske ya tafi da ita saboda cikin magungunan da aka bata a asibiti akwai na Barci....
Saukar C.A kenan a British airport, dayake dama Anan suke ajiye jet ɗin idan aiki ya kawosu England ɗin, wayarshi ya ciro yayi dialling ɗin number haidar Amma Abin haushi switch off, cab ya tara yace takaishi St Leo's Street.
Cikin minti 15 suka iso ƙofar gidan haidar, sallamar me cab ɗin Aayaan yayi sannan shi ya nufi cikin harabar gidan, murmushi sosai ne a Fuskarshi na farincikin yau zasu samu lokaci mai tsawo Tare Da ɗan uwanshi su tattauna, kuma yasan yanzu in'sha Allah bazasu kumayin nisa da juna ba.
Ya buga kofar yafi sau goma amma babu alamun an tawo buɗewa, tsaki Aayaan yayi don wani zubin be cika son jiraba barin idan Akwai abinda ya ƙagu ya samu, "Nasan sunanan tunda ga motar haidar ɗin a compound"
Ɗan ƙara bugawa yayi saboda yayi tunanin ko basa kusa, dadai yaga alamun baza'a buɗeba sai ya samu wata kujera a cikin varendar ya zauna.
Sai tsaki yakeyi gashi ya ƙara kiran haidar ɗin still numbershi a kashe.
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...
