13&14

7 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*13*

Written by Matar Rasheed

    This page is gratefully dedicated to all members of MATAR RASHEED NOVELS GROUP.....  Harda Marasa comment 👀

   

   Rudewa safraz yayi ya Fara kiran sunan mummy....

     Daga stairs mum take saukowa cikin sauri "Menene Kake kwalamin Kira Haka kamar kiran mafarauta,

   Bata gama maganarba tayi kan nawaz da gudu ganin zata fad'o Daga kujerar....

    "meya faru da ita?  Ko wani abun kayi mata?

   A'a mummy Allah banyi mata komaiba,  Muna magana kawai naji tana cewa "wayyo ummina zan mutu"

   Mum ta kasa daukanta saboda rud'ewa,  cewa tayi "SARFRAZ ɗauketa mutafi asibiti"

Ciccibarta Yayi zuwa mota,  bai jira mum ba kawai Yayi igniting motar yayi Waje.....

    Mum data fito fad'i take "SARFRAZ tsaya mu tafi tare mana!"

   Inah ai tuni SARFRAZ ya wuce domin yasha kwana ma.....

   Cewa tayi driver ya bi SARFRAZ,  Amma abin mamaki ko tayan motanshi basu ganiba...
    Elite hospital tace suje Kila chan yaje amma ,dasuka je babu SARFRAZ babu alamunshi.... 
    Gida tace su koma domin tasan wahala kawai zatasha saboda be dauki wayaba....

   Shi kuwa goga SARFRAZ yana aeydan health care center....

    Ganin yanda ya shiga da ita a hannu yasa ba'a jira komai ba aka amshesu,  gado aka d'orata "Sai zufa takeyi, tana murkususu domin da alamu batasan inda takebama....

   doctor ne yace please kad'an jiramu a Waje mister .....

  Kopar ward d'in ya fita ya tsaya..

   Sai sannan ya Kalli kanshi,  babu takalmima a kafarshi babu hula rigama T-shirt ce sai wandon shadda ....

   Kunyar kanshi yayi ya  Fara ji.....

   Wani ya gani yazo gurinshi rikeda takalmi, mi'ka mishi yayi "aboki sa wannan, naga sanda ka shigo a dimauce, saida na tuna sanda madam d'ina zata haihu nima,  domin ni singlet cema a jikina...

    Amma dai yanzu ta Fara nakudar koh?

   takalmin SARFRAZ ya Amsa yace "nagode aboki,
    sannan yayi murmushi yace "aiba haihuwa zatayiba,  domin ko ciki batada shi, zaune muke Muna hira sai ta Fara juye juye wai cikinta...

    Kyalkyale wa Mutumin Yayi da Daria  "amma dai a gidanku babu mata ne koh?
  
   shanmur SARFRAZ yayi "kai kuma meye na Daria?

mutumminne yace "ainaga yanda ka rudene saikace wadda zata haihu, ashema ba'kon watan tane....

   dai dai nan doctor ya fito "mister pls muje office,  binshi SARFRAZ yayi cikin office din, guri ya samu ya zauna.

    gyaran murya doctor Yayi "ehmmn dama matanka period takeyi, kuma wannan abinda kaga tanayi cramping ne saboda yanayin contracting d'in Kowa daban , wasu basuda hard contractions  wasu light ne shiyasa zakaga ko suna period Amma babu Wanda zai sani...

   to ita irin nata mai wahalane domin irin nata mutum saiyayi aure yayi mu'amular aure da mijinshi yake denawa....
   to kuma tunda ita tayi aure bata denaba sai dai asa rai idan ta haihu zata dena insha Allah....

   SARFRAZ ne yace "doctor Dan Allah yanzu babu Wata hanya da za'a bi domin ta dena ko kuma wani magani da za'a bata?

    Doctor yace "to be sincere babu abinda za'a iya yi mata gaskiya saboda halittatta ce haka,  Abu d'aya zan iya ce maka shine...
   duk sanda irin haka ta faru ka samu ruwan zapi da towel ka gasa mata mara Ahankali, sannan kuma tasha pain killers,
   Sannan yanzu zan rubuta maka wasu magunguna
   Sai a siya Ta ri'ka sha,  Insha Allah zata samu sauki.....

SARFRAZ Où les histoires vivent. Découvrez maintenant