*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*65*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Saida ta tabbatar mummy da Aayaan sun bar wajen sannan ta fito ta shige ɗakin da umminta suke zaune.
Tana shiga ta faɗa jikin ummi tana haki "lallai Madina, daga zuwa saiki faɗa jikinta Kamar kin faɗa saman gado?" Cewar Ammah tana hararar Nawaz."Ai Wallahi Ammah Bansan sanda Nawwarah zata dena yarinta tasan ta girma ba"
Ammah ce tayi dariya tare da cewa "hmmm ai Madinatul munawwarah bazata dena yarintaba sai taga wani ɗan Ko ƴar a hannunki, inaga shine Kawai Abinda zaisa ta haƙura.
Kunya ummin Nawaz taji, amma a cikin zuciyarta cewa tayi "Allah ka bayyanah Min mijina kila nima ina da rabon kuma ganin Wani ɗan nawa"
Ita dai Nawaz duk Maganar da akeyi bata ɗaga ummin tata ba, saima daɗa lanjarewa da tayi a saman cinyarta.
"Gobe War haka in'sha Allah muna gida abin mu" cewar Ammah tana samun gefen gado tana zama
"Nifa Ammah nasan tsohon mijinki Kawai kika ƙosa kije ki gani" cewar Nawaz tana kanne ido ɗaya."Eh ɗin ja'ira!! Mijin nawa nakeso naje na gani, ance muku mu irin kune da basu ɗauki miji a komai ba, saikiga mace tayi tafiya tabar miji a wata ƙasa kusan wata ɗaya wasuma har biyu...
Aimu Tunda Allah yace Aljannar mu tana kasan kafarsu muka saduda muke musu biyayya, idan kema zaki yiwa kanki faɗa to gwara kiyi duk da dai Bansan Yadda kamun ludayin naku zai kasance ba.Duk sai Nawaz taji ta zargi kanta, sai take ganin kamar Ammah tasan tsakaninta da Aayaan ne shiyasa take faɗa mata wadannan maganganun.
"To Ammah da kike faɗan wadannan maganganun cemiki yayi bana yi mishi abinda yakeso?"Banga alamun anayiba koda shi be faɗa minba, domin alamar ƙarfi ai tana ga mai ƙiba "
Balla mata harara Nawaz tayi tareda cewa "wani mai kibar Koh? Don wani siririn yafi kwarin ƙashi""Au Madina Rashin kunya zakiyimin saboda ina baki Shawara akan ki kula da mijinki domin ki samu Aljannah ranar gobe kiyama"
Miƙewa Nawaz tayi tana karkaɗe hijabinta tare da cewa "ba'a son shawarar taki, ƴar sa eyes a abinda be shafeta ba kawai"
"Yanzu Madina nice ƴar sa ayiss ɗin" kallon ummin Nawaz tayi tace "ke Rahmatu meye ayiss ɗin?
Dariya ummi tayi Sannan tace "eyes yana nufin ido da Hausa".
"Uwariyonki nace Madina, wato nice ƴar sa ido Koh?"
Ficewa Nawaz tayi daga ɗakin gaba ɗaya tunda dama a miƙe take ..."Ƴar ƙaniya! Allah ya raka taki gona, kuma kada ki sake ki dawo ɗakin nan tunda fitsara zaki riƙa yimin"
Ɗaga murya Nawaz tayi "zan gani idan ɗakin nakine da zakice kada na dawo''
Tana fita sukayi kicibis da Aayaan shima ya tawo da nufin shiga ɗakin, gani tayi ya daɗa yi mata kyau fuskarshi cike da farin ciki, idonshi har wani kyalli yakeyi, ga gashin kanshi yasha gyara haɗe da sajenshi.
Murmushi yayi mata me kyau "sweetheart keda waye nake jiyoku tun ina corridor?
Shagwaɓe fuska tayi "ba Ammah bace ta dameni ba"
Shagwaɓar da tayi sai yaji Kamar an tsikare shi, murmushi yayi aranshi yace "mun kusa shiga duniyar da shagwaɓar zatayi Amfani" amma a fili sai yace tafiyarki zanji da ita nasan kishi ne ke damunta, kinsan tunda taga kinfita Komai shine kullum take tononki da faɗa.Dariya Nawaz tayi ta Wuce abinta tare da mamakin Kasancewar Aayaaaann soja babu abinda ya hanashi, idan yana wani abun ma bazaka taɓa cewa shi soja bane illa jikinshi da zai tona shi saboda murɗewar tayi yawa dole sai dai sojan.
Shiga yayi suka cigaba da sabga dukda yana ɗan jin nauyin ummin Nawaz, "ummi Nawaz tayi muku Sallama kuwa?
BINABASA MO ANG
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...