*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*
*39*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️
Wace matar tawa kike nufi?
Balla mishi harara Nawaz tayi "au matan naka har nawane da zakace saina banbance maka wacce daga ciki.." Hmmm yarinya zaki sani ne, wato kin fara rainani Koh?
Murguɗa Baki Nawaz tayi "niba yarinya bace"
"Au ashefa sunanki maman boy ko? Sorry na manta"
"Eh sunana haka ɗin saime?" Wajen muhsien ta waiga "muhsien ɗana zoka zauna a cinyata kaji daga yau sunana mummynka"
Cinyarta muhsien ya dawo yana kallon fuskarta "Aunty da gaske kema mamana ce?
Murmushi tayi mishi "eh muhsien, Nima mamankace kaji?"
Aayann kam sakin baki yayi yana kallonta "wai ɗan ta bata min rai take wannan? Murmushi yayi kawai be kulataba ya tada motar yayi gaba..Dai dai sunzo zasu wuce layin baaba Ahmad Nawaz tace "Please anan gaba kaɗan akwai gidan wata ƙawata Nafisa tare mukayi Junior secondary school da ita idan ba damuwa dan Allah inaso kaɗan tsaya zan shiga mu gaisa.
"Okay babu matsala nunamin inda zamubi.
Dai dai Kofar gate ɗin gidan yayi Parking Sannan Nawaz ta fito riƙe da hannun muhsien, shima sai ya fito ta ɗaya ƙofar ya jingina da motar yana kallon Nawaz ɗin, wacce tayi wani irin shu'umin kyau, "ku shiga Ni zan tsaya daga nan in ɗan ga gari.
"To" Nawaz tace tare da tura gate ɗin suna shiga ciki.
Durkushe Nafisa take tana Alwala taji an buɗe gate an shigo, da sauri da ɗago kai don ganin waye, Aikuwa da gudu ta saki butar ta nufi Nawaz ta ruƙunƙumeta "wayyooo Allah yau juma'ar ta musamman ce, Nawaz kece? Wallahi nayi kewarki.
Babu abinda Nawaz take yi sai murmushi, Sakinta Nafisa tayi Sannan ta Kama hannun muhsin suka shiga ɗaki, a kujera ta zaunar dashi sannan ta kwaso kayan ciye ciye kala kala na yara ta miƙa mishi, ita kuma Nawaz ta kawo mata drinks."Oh Nawaz ashe rai kanga rai? Aini Nasha munyi hannun riga bazamu sake haɗuwa ba, kinsan rabonda mu haɗu tun bikina, Gashi dama Ni bansan gidankuba kuma numberki bata shiga.
Hmm wallahi kuwa, Nima abubuwane sukamun yawa kinsan fa bayan Nagama NCE Saida na ɗora da B.ED.
"Ikon Allah kice kunbarmu a baya, nida nayi aure a jss3 kinsan bebari naci gaba ba."Haka ne Allah kinsan wasu mazan basason suga matansu suna zirga zirga cikin maza. Cewar Nawaz tana daukar ruwa
"Wallahi kam, Allah dai ya bamu zaman Lafiya a gidajen aurenmu ya kaɗe fitina.
Nawaz tace "Ameen tana ajiye Ruwan bayan ta kurɓa, "wai kuwa yaranki nawa yanzu?
Dariya Nafisa tayi "yarana biyar"
😳 Eyee wai wasa kike ko gaske? Amma Nafisa kece da ya'ya biyar? Nawaz tace cike da mamaki.
"Wallahi dagaske nake, saidai haihuwata huɗu, saboda Akwai ƴan biyu shiyasa ƴaƴan suka zama biyar.
Murmushi Nawaz tayi "haba koda naji amma ko a huɗun ma sunyi yawa, inasuke?.
"Kai Nawaz ko don ke haihuwar ƴan gayu kikeyi? Suna gidan kakansu.
"Hmmm aini banyi aureba har yanzu, sai dai ku taysamu da addu'a. Da suna nan Aida na gansu
"Harara ta balla mata, lallai NAWAZ aiko makaho ya shafa fuskar ɗan nan ya shafa taki yasan kece mamar shi balle Nida Nasan yawan shekarunki, tundama shekara biyu na baki Kinga kuwa yanzu ina 27 Kinga ke kina 25 kenan.
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...