*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*9*
✍🏻 by Matar Rasheed
Ganin sarfraz Hankalinshi kwance yanata faman barci......
Hancinshi ta matse iska ta daina shiga, Dasauri ya bud'e ido ya tashi......
Mitstsike idonshi Yayi sannan yace mummy kin tashi ashe😳
Mum tace "ban tashiba Kai yakamata in tambaya koka tashi?Murmushi yayi "mum menayi kuma?
Cewa tayi "kazauna tambayata Bayan kacemin 1:00pm kakeda lecture kuma gashi yanzu 1:30pmKayi sauri ka tashi ka shirya, kasamu kaci abincin ko kadanne saika tafi....
Cewa Yayi to mum, sannan ya fita.
Juyawar da Mum zatayi kawai ta hango nawaz sai faman barci takeyi, duk ta saki jiki..
Karasawa tayi tad'an tasheta kad'an, bud'e ido tayi suka had'a ido da mum, da sauri ta tashi domin Sam ta manta ba'a gida takeba.....Mum tace meyasa kikazo d'akin sarfraz?
Maimakon kizo nawa, inma bakyason nawa ai akwai d'akuna da yawa....Cewa tayi d'akin sarfraz 😳❓
mummy wallahi bansan d'akin shi bane 🤨.
Kuma aishi yace nazo nan😔"kada ki damu my dear ☺, nasan halin sarfraz zaiyi fiye da hakama.
yanzu kizo muje kici abinci kiyi sallah koh?"to" tace sannan ta Mike tabi Bayan mummy.
A dining suka tarar da sarfraz har Yayi serving dinsu, mummy ta balla mishi Harara "wayace maka yanzu zamuci daka wani zuba mana ❓
cewa Yayi ai nafiso taci da wuri saboda mu tafi da wuri kada na rasa lecture na🤨..
Mum tace ban gane ku tafiba 🤔
cewa Yayi "dama dazu da Muna girkine tacemin Dan Allah idan zan tafi makaranta zata bini in siyan mata kayan kwalliya da hijab shine nace mata to.
kallon nawaz yayi "koh malama 😋😉❓☹ 'bata rai nawaz tayi "yaushe nace maka haka 😟?
fuskar mamaki sarfraz yayi "haba malama fisbilillahi Don kinajin kunyar mum saiki chanza magana 😉😎
Cewa tayi "Allah niban ce maka hakaba 😡
mum tace "shikenan yi sauri kici abincin kiyi sallah kibishi kada ya rigaki,
"Mum Allah niban ce mishi hakaba 😦
mummy tace " shikenan, koda bakiceba tunda Yayi niyyah saikije ya siyan miki d'in, yi sauri my daughter ☺
Nawaz ta cika tayi bam ji take Kamar ta zabga ihu, Shiko sarfraz murna fal cikinshi.....
bini bini ya kalleta Yayi mata gwalo 😛😋😜...
sunkuyar dakai tayi takicin abincin, mum ce ta ta'ba ta "my daughter kici abincin mana!
Charaf sarfraz yace "mum tun dazu tacemin Idan muka fita in siya mata ice-cream 🍦 da chocolate 🍫, wai su take sha'awa yau...
OK "tunda bakyajin cin abincin to yi sauri kije kiyi sallah kafin ya gama.....
Tashi tayi ta nufin d'akin mum,
Tana shiga tace "wayyoo oh ooo 🤯
wai me wannan sarfraz d'in yake nema danine ❓ya daukeni tamkar sa'ar shi, to kuwa zan koya mishi hankali, wallahi donma Ina jin kunyar mummyn shine.....
Bathroom ta shiga donyin alwala, amma me?
Jikinta ta gani a 'bace, cewa tayi na shiga uku, baka kyautamin ba coz bakazo a lokacin daya daceba...

أنت تقرأ
SARFRAZ
عاطفيةLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...