31&32

10 1 0
                                    

*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*

*Episode 31*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji*✍️

   
      Muryar ta na rawa tace "don Allah kada ka cire.
     "To ki faɗa min waya baki?

     "Sarfraz ne ya bani"
  Sakin mata hannu yayi saboda wani irin zafi da yaji kirjin shi nayi, "right wai waye sarfraz ɗin nan ne? Nifa da mukaje gidanku babu  wanda yayi maganar wani sarfraz, ke kaɗai kawai akace kin tawo ba tare da wani ba.
    Kuma Ni sam na manta ban tambayesuba, amma bari na kira wayar baffa in tambayeshi yanzu..

    "No don Allah kada ka kirashi" Nawaz tace jikinta naci gaba da rawa.

     "So tell me who is he idan bakya so na kirashi.
     "Dalibinane" tace a takaice

    Wani abu Aayaan yaji ya tokare mishi wuya ga idonshi har wani yaji yaji yake mishi, shi kanshi ya rasa meyasa hakan.
     Da kyar ya Iya daurewa yace "look Nawaz ba wasa mukeyi ba please be serious waye shi?
    "Allah dalibinane"
"Idan shi dalibinki ne ya akayi ya baki zobe kuma kikasa a yatsanki? Sannan kuma ya akayi kuke tare dashi sanda zakizo garinnan?

    Hawayene ya zubo mata a fuska "bazaka ganeba Wallahi ɗalibinane kuma zoben da kanshi ya bani sannan sanda zan tawo shima kakanninshi anan suke zai zo gaishe dasu shine muka taso tare.

    Zubar hawayen Nawaz yana dai dai da kamar an zubawa Aayaan garwashi a cikin zuciyarshi.

    "Look bance kiyi min kukaba, daga na tambayeki? So i am sorry kawai dai ina so na sanine saboda zoben yanada dogon tarihi a rayuwar mummy na.

     "Mummy kuma? Nidai sarfraz ne ya bani Wallahi ba na mumy na dauka ba, bana daukar abin mutane .

    "A'a calm down mana meyasa kike da saurin rudewane? I don't mean na mummy kika dauka, dama ai zoben guda biyu ne, amma ki bari yanzu zan kira mummy sai tayi Miki bayani...

     Tafin hannunshi ta kalla ganin ya cire bandage ɗin sai ciwon yayi wani irin pink, wani zafi taji a zuciyarta ganin yanda yakeshan wannan azabar a dalilinta.
     "I am very sorry naga ciwonka is still new, sannu yana maka zafi koh?

     "No never mind, Kim manta ni soldier ne? Ai wannan ba wani abu bane aguri na, Wallahi mantawa ma nakeyi dashi...

    Kallonshi yakai kan muhsien wanda ya miƙe ƙafa a kasan tile's sai cin chips ɗin shi yake yi hankali kwance...
     Tsugunawa yayi dai dai shi "Superman babu magana ne?
   Chuno baki yayi "bakai bane kaketa yiwa Aunty faɗa, kumani ina sonta saboda Nima tana sona.
    "Oh no ba faɗa nayi mata ba, kawai dai na tambaye tane.

    "Ba har tears naga suna rolling a cheeks ɗinta ba, kuma babu ruwana dakai tunda kasa Aunty na tayi kuka....

    Janyo shi yayi zuwa kirjinshi "i am sorry bazan kuma ɓatawa Aunty ranta ba.
    "To ka bata hakuri" muhsien yace yana ci gaba da cin chips ɗin shi hankali kwance.

      Juyawa Aayaan yayi daidai Nawaz ya haɗa hannunshi guri ɗaya "Aunty Don Allah kiyi hakuri bazan kuma ba...

    Da sauri Nawaz tace "please ka bari yaya Aayaann "
     Ji yayi kamar babu wanda ya kaita iya pronouncing ɗin sunanshi.
      Murmushi muhsien yayi "yauwa to yanzu Nima na hakuri, ɗauke Ni muje falour to.

    Sunkutar shi Aayaan yayi suka nufi falour, sai sannan Nawaz taji ta fara samun nutsuwa.
     Ta rasa meyasa idan Aayaan yana kusa da ita take neman natsuwarta ta rasa ga wani uban tsoronshi da takeji sannan zuciyarta tayita bugawa.

     A hankali take tafiya ta fito daga kitchen ɗin rikeda ragowar chips ɗin muhsien.

     Aunty kinga uncle ya cinye min chips ɗina Koh? Muhsien yace yana kwaɓa fuska kamar zaiyi kuka...

SARFRAZ Donde viven las historias. Descúbrelo ahora