*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*59*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Zuciyarta kamar ta fashe saboda tsoro, gashi babu damar yin ihu tunda har yanzu bakinsu a haɗe yake.
Zaro ido tayi sosai Yadda taji tudun length Dinshi na taɓa mata saman mara tasan idan ya chafketa ba ƙaramar wahala zata sha ba.Ji tayi kamar an sakata a Aljannah jin ana buga ƙofar ɗakin.
Chak Aayaan ya tsaya da Abinda yakeyi, be ɗaga taba Saida aƙalla aka buga ƙofar ɗakin sau Kusan Biyar Sannan ya dagata yana cewa "Allah ya Taimakemu dukanmu, amma da yau hmmm, jeki buɗe kofar" cikin wata irin kasalalliyar murya
Rimi-rimi Nawaz ta tashi daga gadon kamar zata buɗe ƙofar, ai kuwa ta faki idonshi ta afka bayi da gudu tare da zira jamlock.
Murmushi yayi Tare Da girgiza kai Sannan ya miƙe ya nufi kofar, saida ya tsaya ya ɗan gyara zaman rigarshi tare da barbaza gashin kanshi Sannan ya buɗe kofar.
Aseey ce tsaye da gani ta ƙagu da'a buɗe mata kofar, kallon Farko data yi mishi ta gane ba ƙalau ba (kundai san Aseey tayi degree a wajen sa ido).
Cikin ɗakin take kallo "ina sister Nawaz ɗin?
"Tana bathroom" Aayaan yace Tare Da bata hanya tana shiga cikin ɗakin, shima bayanta yabi ya koma ya zauna a bakin gado.Murya Aseey ta ɗaga tare da cewa "sister yi sauri ki fito Akwai labari mai zafi banso ya huce.
Kallon Aayaan takeyi tanason tayi dariya amma bataso ya ɗauki wani abu a ranshi, a zuciyarta take zancen zuci "A to aikai ka sani, adaiyi mugani idan tusa zata hura wuta! tunda ka zauna wai kai mai mata, bakaso ta wahala, aikai kuma kayanki ticket ɗin wahala, abinda da anyi so ɗaya an Wuce gun amma har yanzu fama akeyi wai kai me tausayi, zan dai ga ƙarshen wannan tausayin"
Saida murmushi yayi nasarar suɓuce mata.Ɗage gira Aayaan yayi "lafiya dai kike dariya ke kaɗai?
Ɗan daburdabur tayi sannan tace "wallahi shirmen hassu da sarfraz ne yake bani dariya"
Kafaɗa ya ɗage alamun ko oho, "nifa Banga lefin suba.
Domin dole ne na nunawa wanda nakeso inasonshi, babu wani shirme"Nawaz dake cikin bayi Saida taji dama ƙasa ta tsage ta rufta ciki jin Muryar Aseey datayi, tasanta dasa ido ga bin ƙwaƙwƙwafin tsiya.
Kunna pampo tayi ta wanke fuskarta, sannan ta duƙa don tayi fitsari sai taji pant ɗinta a jiƙe, tsaki tayi "Mtsewwwss" don tasan ko menene koda bata duba ba.
"Wai meyasa zuciya take hakane? Duk irin firgicin danake ciki saida tasa jikina yayi reacting."
Gama gyara jikinta tayi sannan ta ɗauki towel ta goge fuskarta.Cikin sanɗa ta buɗe ƙofar, aikam karaf suka haɗa Ido da Aseey, ɗan murmushi Aseey tayi don Yadda taga idon Nawaz yayi wuri-wuri ga laɓɓanta sunyi wani irin pink, ko ba'a faɗa mataba tasan ƙaninta ya rage zafi. "Sister yi sauri ki ƙaraso mana! Kada fa Labarin ya huce!
Ɗan ƙara karsashin jikinta tayi tare da ƙarasawa kusa da Aseey ɗin tana zama.
Sosai Aayaann ya dage yanaso su haɗa ido amma fir Nawaz taki yarda, duka ta maida hankalinta kan Aseey, amma Wata Irin kunya na lullube da ita, don Babu yadda zatayi ne shiyasa kawai na danne ta fito.
"Mummy ce tace zamu tafi sudan wajen yan uwanta nachan, kuma daganan zamuje gidan Aunty khatoume tayi mana gyaran jiki na sati ɗaya, Amma kafin nan sai mun fara komawa maiduguri saboda kije kiga ƴan uwa.
Kuma wai za'a tafi da Daddy harda mummy da Sarfraz ma, au harda su hassu fa, koma ince duka zamu tafi saboda wai za'a je a nemawa Sarfraz auren hassu kuma shima SARFRAZ ɗin zaije danginshi, and mummy ma tace tanaso kije dangin dad ɗinmu su ganki saboda suma basu sanki ba.Aayaann ne yace "haba sis ji yanda kiketa haɗa magana guri ɗaya, ai ba lallai ta fahimci me kike son faɗa mata ba.
"To mai mata, ai sai ka koyamin yadda ake magana, Nidai yanzu zan fara shiri saboda gobe da wuri zamu ɗauki hanya, kuma bari kaji, a Maiduguri zamu barku kaida SARFRAZ domin baza ku bimu sudan ɗinba nasanku da rashin ta Ido, nida hassu da sister Nawaz da Mummy kawai zamu tafi. Ku kuma saiku zauna achan Maiduguri, idan kuma zaku biyo su Mummy da Daddy ku dawo Zarian ne ku kuka sani.

ESTÁS LEYENDO
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...