47&48

1 1 0
                                    

*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*47*

*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*

       Koda Aayaan ya shiga ɗaki kasa zama yayi, yama rasa me zaiyi yaji daɗi! Idonshi gaba ɗaya ya kaɗa ya koma jaa,  jikinshi kuma har wani irin huci yake fitarwa.

    Bathroom ya shiga ba Tare Da ya cire ko ɗaya daga cikin Kayan jikinshiba ya sakarwa kanshi shower 🚿, yafi ƙarfin minti Talatin a tsaye Ruwan yana zuba a jikinshi Sannan ya samu ya cire kayan yayi normal wanka, babu Abinda ya ragun mishi daga raɗaɗin dayake ji a cikin zuciyarshi illah zazzaɓi da yaji ya rufe shi likaci guda.
     Bathrobe yasa Sannan ya fita daga bayin zuciyar shi na tunani kala kala, yama kasa ko shirya wa, ko mai bai iya shafawa ba, komawa kan gado kawai yayi  yaja duvet ya rufe jikinshi Sakamakon wani Irin sanyi dayaji yanaji, Sannan ya dau wayarshi wadda ke ajiye a gefe,  Number Nawaz ya nema ya kira, Amma sai akace switch off.
      Sosai yake mamakin wai me akayi wa Nawaz da har ta yanke wannan tsatstsauran hukuncin?   Shi Yanzu ko nemanta zaiyi baisan ta inda zai Fara ba.      
      Shiyasa yaso sanda Mummy ta faɗa mishi cewa Nawaz  matar shice da an sanar da Nawaz ɗin itama.

     Gallery ya koma inda ya nuno photon Nawaz ya ƙura mishi ido, "why did you choose to run away? Why did you not think of what will happen before going, how i wish you were here when I'm back..... Haka dai Aayaan yaketa magana shi kaɗai sai kace Nawaz ɗin tana zaune a gaban shi..

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

    Sosai Hassu ke ihu tana tafe kuma tana kwalawa SARFRAZ kira ga duhun dare ya fara sauka, saura kaɗan ta ƙarasa gidan baffa ta hango wani Cikin raƙuma kamar SARFRAZ, ai kuwa da gudu ta kwasa zuwa gurin tana kwalawa SARFRAZ kira....

      Waigowa SARFRAZ yayi  yana dariya "Hassu zo kigansu Masu kyau, mu bamuda irin wadannan sai dai irin su gwalbo...

     Wani tuƙuƙin baƙin ciki ne ya turniƙe hassu "Wato yanzu da Ban fito ba da Shikenan binsu zakayi, Ni na taɓa ce maka idan kaga Wasu ka bisu koda mutane balle raƙumi!

   Saroro SARFRAZ ya tsaya, exactly dai Kamar yadda yara sukeyi idan sunyi laifi, harara ta balla mishi "ba tsayawa zakayi ka zuba min ido ba, daka ɓace daka gane kuranka....
     Juyawa tayi ta tafi ba tare data ce zo muje ba, ai kuwa shima saiya bita da gudu yana cewa "kijirani mu tafi"
     Hassu da baƙin ciki ya dameta akan Cewa da Yanzu sarfraz ya ɓace data shiga uku duk saitaji haushin shima takeji, ƙin kulashi tayi taci gaba da tafiyarta.

   Aikuwa SARFRAZ Yana ƙarasawa kusa da ita ya faɗa jikinta yana cewa "inata cewa kijirani anma kikayi banza dani!
    Taga-taga Hassu tayi zata faɗi sai kuwa ya taro ta suka faɗi ƙasa tare yana dariya, Cikin kwayar idonta yake kallo itama Haka, Sanin cewa a Banza "wai an yakushi kakkausa" tasan shi bema san meyakeyiba, ta tashi tana kakkaɓe zaninta.

    Daɗa riƙo ta yayi ta faɗo jikinshi yana ƙara cewa "meyasa baki jirani ba?"
     "Don Allah SARFRAZ ka kyaleni mana" hassu tace tana tureshi daga jikinta, "kaso ka kasheni wallahi, fisbilillah da Allah besa na fito yanzu ba Shikenan ka ɓata kenan?
   "Ni dai Gaskiya har dai kanason in cigaba da zama ƙawarka kada ka kuma bin koma me kagani"

     "To bazan kumaba"; SARFRAZ yace yana riƙe hannun Hassu tare da haɗa su guri ɗaya da nashi yana  sarƙafe yatsunshi cikin na Hassu, sannan suka dauki hanyar komawa gida.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

      Jama'a wai kam Babu Wanda ya taɓa cigiyar umma, anya kuwa? Kodayake dama ai mutum mai baƙin hali bashida farin jini, amma dai yau Ni zan leƙa ko don naga ƙwaƙwaf!

SARFRAZ Where stories live. Discover now