*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*25*
*NA HAFSAT ALIYU SHUAIBU CHIKAJI*✍️
Hasken Rana ne ya haska cikin tent ɗin da Nawaz ke kwance, kasan cewar tent ɗin light blue ne kuma yana fuskantar gabas,
Hakan sai yasa cikin tent ɗin yayi wani irin hasken kamar wutar nepa,Tashi zaune Nawaz tayi tana mutstsike ido alamun farkawa daga barci, waige waige ta fara yi domin ta manta a inda take,
Shiru tayi sanda komai ya dawo mata, babu kowa a cikin ɗakin sai dai tana jiyo hayaniya a waje sosai..Mikewa tayi a hankali ta ɗan bude labulen tent ɗin ta leka waje, daarararammmm gaban Nawaz ya faɗi, dalilin ganin sojojin da tayi bila adad kowa na sharafin gabansa.
Ai da sauri ta saki labulen ta koma ta zauna, tunani ta fara "wai haka rayuwa take dama, duniya juyin juyi, yau ta kaika nan gobe ta kaika chan, Allah Sarki ko ina sarfraz? Yana raye koya mutu, kuma nasan duk inda mummy take tananan hankalinta a tashe, ummi nama nasan tana cikin damuwa..
Oooh nama manta da akwai waya a duniya, ƙilama suna ta kiram mu...
Hawayene ya ziraro daga idonta, bata samma ya zubo ba saboda gaba daya ruhin ta baya tare da ita, tunaninta yafi tafiya kan mummy SARFRAZ saboda shi kadai gare ta sannan bata bari yayi nesa da ita amma gashi sanadinta hakan ta faru, kuma tasan takira wayoyinsu har ta gaji...
Abu taji ana goga mata a fuska, firgigit ta dawo hayyacinta, Aayaan ta gani durkushe a gabanta rike ta very neat hankie yasa a fuskarta yana tsane mata hawaye.
Gira ɗaya ya ɗaga mata "why are you crying? Keda tun ɗazu ake jira ki tashi shine kuma zaki tashi da kuka?
Wani hawayen ne ya ƙara zubowa daga idonta "bansan wane hali SARFRAZ yake ciki ba.......
Ita kanta bata san sanda maganar ta fito daga bakintaba kawai dai taji ta gama faɗa ne.murmushi yayi mata me kyau "look insha Allah Babu abinda zai sameshi kin ji? Saboda tun tuni aka Turo Ambulance ta kwashe waɗanda suka ji ciwo aka kaisu asibiti don abasu taimakon gaggawa, waɗanda suka rasu kuma ankaisu mutuary kafin ƴan uwansu suzo su daukesu.
And please ki kwantar da hankalinki everything will be right insha Allah, Yanzu me zakici? And kuma nasan jiya daƙyar idan kinyi sallolinki koh?Mamakine ya kamata "au dama sojoji suna sallah, lallai Allah al Hakeem ne, ai ita tasha faɗa da harbe harbe be barinsu su tuna da sallah, to kuwa indai hakane sun isa a Sara musu.. Nawaz ke zancen zuci
Husky voice dinshi ta daɗa ji yace "sister bakice komai ba.
" To ameen Allah yasa yana raye, sannan ruwan alwala zaka fara bani inyi sallolin saboda tun sallar azahar ɗin jiya ban kuma yin Sallah ba.
"Okay bari nazo" fita waje yayi be daɗe ba ya dawo rike da bottle water Guda biyu.
Bata ruwan yayi sannan yace kiyi alwalarki a gefen nan kawai basai kin fita ba, akwai maza da yawa a waje.
Idan kuma za kiyi easing kanki ne to sai in raka gurin da zaifi _safe_.
Da sauri tace "A'a banaji Nagode, be kuma cewa komai ba ya juya ya fita daga ɗakin....
Gefe ta samu tayi alwalar sannan kuma ta koma ta zauna tana tunanin dame zata rufe jikinta tayi sallah, dai dai nan Aayaan ya dawo,
Be kula taba ya wuce ya bude wata luggage 🧳 me jikin sojoji ya ciro wani farin plain din zanin gado, hannunshi yasa ya yaga shi biyu, ajiye ɗayan yayi a gefe sannan ya miƙa mata dayan,
"Ki rufe jikinki da wannan sai kiyi sallar,
Amsa tayi "Nagode"
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...