85

3 1 0
                                    

*🎀🎀SARFRAZ🎀🎀*

*85*

*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*

_Assalamu alaikum_
   _Ina yiwa kowa Fatan Alkhairi, da fatan munyi Sallah lafiya, Allah ya amshi ibadun mu (AMEEN)_
 
   _Bayan hutu da mukayi na Ramadan, Allah cikin isar sa da mulkinsa  ya ƙara bamu aron rai yau cikin ikon shi zan cigaba da littafina mai suna *SARFRAZ* Allah ya bamu ikon gama shi lafiya *(AMEEN)*_ _duk da dai dama saura pages ƙalilan mu kammala, Wanda daga bisani zan cigaba da posting ɗin ɗayan littafina mai suna *IZAYAR RAYUWA* In sha Allah_

   Da gudu Ummin Nawaz ta tafi ta faɗa cikin ƙirjin shi, Sosai kuka ya kuma kwace mata "dama kana raye? Dama Zan kuma ganin ka? Dama da rabon ganawar mu?"
   Riƙe ta Abban Nawaz yayi sosai a cikin jikinshi, tun daga cikin zuciyarshi yakeji kamar wani Abu na fita tare da duk wata damuwa daya daɗe a ciki suka kwararewa a ƙasa, sakayau haka ya koma jinshi "Rahma nayi kewarki, nayi kuka da idona duk a kanki, ko Yanzu tararrabin shigowa gidan nan na gama yi a waje Kafin na shigo, domin duk iya tunanina na aje cewa bakya Cikin gidan nan"
   Duk wannan abin dai Ummin Nawaz na cikin jikinshi taƙi sakin shi

   Riƙe ta yayi Sosai sannan ya fara tafiya yana nufar hanyar dakin su "muje in samu in ɗan zauna kona samu na dawo dai-dai masoyiyata!" Kunya maganar taba Ummin Nawaz "wai masoyiyata" _Ni kuwa matar Rasheed nace "Ai soyayya bata tsufa, Gara dai shima ya ɗan taɓa"_

    A saman three sitters sofa ɗin dake faloun ya zauna, ajiyar zuciya yaketa saukewa a jejjere kamar yaron dayasha kuka ya godewa Allah.

    Kafin wasu mintuna tuni ummin Nawaz ta cika mishi gaba da abubuwan motsa baki, "Allah Sarki Rahma mai karamci! Ashe dai har yanzu baki chanza ba?" Cewar Abban Nawaz yana ɗaukar Ruwan data ajiye mai yana buɗewa.
    Jikinta har rawa yakeyi tsabar farinciki, Kamar a mafarki haka take ganin komai, wai yau itace gata ga Muhammad dinta har yana yaba mata akan ta kawo mishi wani abuu,
    ciki ta shiga ta kuma auno wata shinkafar ta wanke ta zuba Sannan ta  leka ɗakin umma don ta gaya mata Abban Nawaz ya dawo, ganinta tayi tana barci kuma da alamun barcin yayi mata daɗi, kyaleta tayi bata tasheta ba, ta juya ta koma ɗaki, koda zata shiga da sassarfa ta shiga ɗakin saboda yadda takejin idon Abban Nawaz akanta.

   Hakanan ta samu kanta da wata irin jin kunya da nauyin shi gaba ɗaya sun lullubeta, "ina yini?" Ummin Nawaz tace a ɗan ɗarare, domin bata saki jiki a saman kujerar data zauna ba.

   "Lafiya Lau hasken idaniya ta, fatan na sameki lafiya?"

   Dan murmushi tayi tana ganin kamar ya ɗan chanza saboda yadda yaketa faman zolayar ta tunda suka haɗu, daga bisani kuma tace "lafiya Lau Alhamdulillah, ya bayan saduwa?"

   "Hmmm Rahma babu daɗi, Bama naso na tuna samm.."

   "To Allah ya kyauta ya kiyaye gaba"

  "Ameen Rahmatullah" cewar Abban Nawaz yaya zancen zuci cikin zuciyarshi  "Lallai Rahma har yanzu baza ta chanza ba kenan daga wannan kawaicin nata da yakana" yasan muddin bashi ya faɗa mata abubuwan da suka faruba, da Dalilin rashin dawowarshi ba to tabbas ita bazata taɓa tambayar shi ba.... Domin ita a nata gurin zata ga idan ta tambaye shi zaiga kamar tana ƙalubalantar shine.

   Nan ya matsa kusa da ita  ya zauna ya fara bata Labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyar shi har zuwa yanzun ɗaya dawo gida, shiru kawai tayi tana girgiza Kai tare da ƙara amanna da buwayar Ubangiji "lallai duk abinda Allah ya tsara babu makawa saiya faru, koda kuwa duka duniya zasuyi tawaye akan abin.
   Bata Ankara ba saijin ƙauri tayi, shinkafar da take dafawa har ta fara konewa domin ita sam tama manta da ita.
     Fita tayi da sauri ta sauke Sannan ta kwashe wadda bata ƙone ba  ta zubawa Abban Nawaz a plate sannan ta zubawa Umma itama, ɗakin takai mata ta ajiye saboda har zuwa lokacin bata farka ba.

  In takaice muku zance dai, Abban Nawaz dai be nemi umma ba kuma beyi maganar taba, koda Ummin Nawaz tayi mishi magana cewa yayi "Rahma Don Allah kada ki bata Min rai, ina cikin farin ciki fa, kuma angoncewa nakeso muyi bayan na watsa Ruwa, kuma wallahi yau sonake a kaini inda ban taɓa zuwaba domin shekara daya ba kwana ɗaya bace, nayi kewarki sosai, "ina ummina?"   Murmushi ummin Nawaz tayi Sannan tace "umminka tana gidan mijinta.."

   A maimakon ya nuna bacin rai sai ya nuna farincikin shi a fili, har sujada yayiwa Ubangiji "lallai addu'a bata taɓa faduwa ƙasa banza, Allah Nagode, Nagode, Nagode maka sosai." Abinda Abban Nawaz keta maimaitawa kenan

   Mamaki ne kecin Ummin Nawaz, sak Muhammad ɗin data sani baya Kafin ta haifi Nawaz shi take gani yanzu, dadine har cikin zuciyarta, maganar da yayi ta cewa nayaso ya Angonce ita ta ƙara bata kunya sai tayi sauri ta miƙe Domin shiga ɗaki, abin kuma da yayi najin cewa anyiwa Nawaz Aure sai yasa ta tsaya tana Binshi da Kallo cike da jin daɗi da mamaki.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

   Aayaan be direta a ko ina ba sai saman gado, "Nifa yaya ka rabu dani, nace maka ba anan zan kwana ba amma saida kasan yadda kayi ka kawoni, Alhalin idan nace maka banaso ba bari kakeyi ba"
 
    "Wallahi Sweetheart nasan bazan iya barci bane idan bakya kusa dani shiyasa kika ga na matsa, amma idan zan takura miki to ki taso na maidake" shiru Nawaz tayi tana ganin idan tace zata koma ɗin lallai bata yi mai adalci ba "na fasa zan kwana anan ɗin kawai, amma promise bazaka yi min komai ba?"
    "Dear kenan! Babu abin da zanyi Miki, kuma ko jiyan ma aike kika ja har hakan ta faru, Ni Sam banyi niyar yi miki wani abuba har zuwa mu koma gida, amma saida kika susutani ya zamana nemarwa kaina mafita kawai nakeyi lokacin" cewar Aayaan yana zama a gefen ta tare da miƙe ƙafafunshi a saman gado.

    Bata tanka shiba duk da taji duka abinda yace, Duba takai zuwa yatsunshi, tunda take bata taɓa zaton sun kai haka tsawo ba, ga wasu irin kwantattun gashi bakake sidik a saman yatsunshi da kuma gefen ƙafar shi "yaya wai dama haka yatsun kafarka suke da tsawo kamar na hannu? Kai Allah waɗan nan ma sai su iya fin na hannun wani tsawo." Hannu takai zata riko yatsun, ai da sauri Aayaan ya janye ƙafar domin yasan idan ya barta zata kuma jagwalgwala shi ne kuma ya nemi sauƙi ita kuma tace ya matsa mata.

    "Yaya ka bari in gani pls"

   "Nope muje muyi wanka tukuna" be saurari me zata ce ba ya sunkuceta yayi cikin bathroom ɗin da ita, ko a bayin ma a gurguje yayi musu wankan saboda shi kadai yasan abinda yakeji akanta.

   Koda suka fito basu shafa koda mai ba, haka zalika towel ne kadai a jikinsu ya ja musu bargo suka rufa, inda Nawaz take rumgume a ƙirjinshi yana bubbuga mata baya ahankali don ya samu barci ya ɗauketa da wuri.
  Cikin ikon Allah kuwa ba'a ɗauki lokaci mai tsawo ba barci ya ɗauke ta, shima ganin tayi Barci saiya daɗa gyara mata kwanciya Cikin ƙirjinshi tare da rungumeta Sosai, a haka shima barcin yayi gaba dashi.

    Dai-dai Kiran sallar asbah Aayaan ya tashi, cike da ƙauna da soyayyah ya tashi Nawaz don suyi raka'a tainil firij kafin ya tafi masallaci.

     Koda ya dawo daga masallaci bega Nawaz a cikin ɗakin ba, mamakine ya kamashi "to ina zata da asbar farii"

  *CIGIYA* *CIGIYA* *CIGIYA*

   *Don Allah akwai wata wadda mukayi magana zan sai frame's a gurinta kafin sallah, to matsalar da aka samu itace banyi saving ɗin Number dinta ba kuma sai Whatsapp ɗina ya samu Matsala, yanzu haka na rasa contact dinta, to dayake dama tana bibiyar wannan littafin, to Don Allah idan taga wannan cigiyar tayi min magana ta wannan Number 08093215055,* Nagode

Matar Rasheed ❤️

SARFRAZ Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin