*🎀🎀 SARFRAZ🎀🎀*
*33*
*Na Hafsat Aliyu Shuaibu Chikaji ✍️*
Jin abinda Aayaan yace yasa Nawaz tayi saurin matsawa gefe ta bashi tazara sosai.
Matsawa kusa da ita ya ƙarayi "so kin yarda inyi Miki duk abinda naga dama kenan?
Kwaɓe fuskarta tayi "nifa ya Aayaan don Allah kayi hakuri, Ni bansan meyasa ba, kuma Ni wallahi kunya kake Sawa inaji. Ta karashe zancen cikin Muryar shagwaɓa Wadda ita batasan ma tayiba.
Murmushi kawai Aayaan yayi "shikenan nabarki yanzu but ya zama assignment, zaki nemomin amsar bayan mun dawo gida.....
Nawaz kuwa mamaki abin ya bata "wai inmun dawo gida, sai aka ce mishi a garin zanta zama kenan.
Komawa tafiyar kurame akayi saboda babu Wanda ke cewa ɗan uwanshi ƙala. Kowa akwai abinda yake saƙawa a zuciyarshi.....Cikin husky voice dinshi taji yace: naga kamar kinajin barci, ko in gyara Miki kirjina ki kwanta akai naga you feel safe there, saboda rannan ma har muka dawo gida baki tashiba.
Ruɗewa Nawaz tayi, sam ita bataso yanayi mata haka, a yanzu gani takeyi ma Aayaan yafi SARFRAZ rashin ta ido....
"Ni banajin barci, Nagode. Shiru Aayaan yayi ganin beci sa'ar neman zance ba, saboda katse maganar tayi bata yarda Tayi tsawo ba....
°
Achan ɗaya motar kuma mummy ce keta murmushi."Mum what's good? Naga kinata murmushi ne, cewar Aseey wadda ke sonjin ƙarin bayani daga bakin mummy.
"Wallahi daughter wani ci gaba naga yanata samun mu.
"Mummy wane cigaba ne, cewar Aseey cikin son jin amsar mummy ta gaba.
Mummy tace "Aseey Kinga tun randa Allah ya haɗa fuska ta data Nawaz naji wata irin ƙaunar ta acikin zuciya ta, kuma take nayiwa Aayaan sha'awar ta a matsayin mata kuma cikin ikon Allah da mukaje chan gidan kakanninta sai na lura kakanta baffa yanamin hannunka mai sanda, yana nunamin zai ba Aayaan ɗin Auren Nawaz amma sai an shirya...
"Kai kai kai Alhamdulillah, Allah yasa hakan ya faru, domin idan haka ya faru sainafi kowa jin daɗi domin naga Nawaz ɗin akwai hankali da kunya.
Numfasawa mum tayi "kuma abinda yasa nakejin daɗin, baya wuce ganin Aayaan yana nuna zumuɗi akanta. To amma dai bansan manufarshi ba.Aseey tace "mum amma gaskia akwai matsala.
Da sauri mum tace"Aseey wace matsala ce kuma?
" Kada ki tada hankalin ki mum, bawai wani babban abu bane, na lura da wani abune daga gurin Nawaz ɗin.
Mum ce tace "Ƙaniyarki Aseey wato Ni kike jawa rai koh? Come"on zaki faɗa min ko kuwa saina saɓa Miki!
Wai dama gani nayi Nawaz na mugun jin tsoron Aayaan, kuma ko yanzu ma saboda shi taƙi shigowa motar nan, Gashi kuma ya bita....
"Tsoro kamar ya? Cewar mum tana kama haɓarta
Gyara Zama Aseey tayi "mum Nasha ganinsu tare, sai inganta ta firgita shikuwa yayita murmushi, nifa gani nakeyi kamar daɗi yakeji idan yana bata tsoron.
"Oh shikuma Aayaan irin tashi soyayyar kenan, Lallai Amma Allah ya zaɓa mana Abinda yafi Alkhairi....... Mummy tace tana gyara zaman muhsien wanda tuni yayi barci a cinyarta...
Ƙarar shigowar kiran mijin Aseey ne a waya yasa mum yin shiru ita kuma Aseey ta ɗaga fuskarta cike da murmushi.....
°
Aayann nanan yanata faman neman hanyar dazai tsokani Nawaz amma Sam taƙi biye mishi,
YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...