*🎀🎀 SARFRAZ 🎀🎀*
*81*
*Na Hafsat Aliyu Shu'aibu Chikaji*
Jiri ne ya kama Nawaz kafin su ƙaraso kusa da ita, baya tayi zata faɗa, amma tana ƙoƙarin tsaida kanta daga faduwar, sai ya zamana kamar tana layi, Aayaann dake jingine da kujera ne ya gane faduwa zatayi amma take ƙoƙarin hana kanta, cikin Rashin kwarin jiki ya tashi da sassarfa ya nufi inda take.
Dai dai nan itama Aseey ta lura da abinda zai faru, dagudu ta ƙarasa dai-dai zuwan Aayaan gurin, dai dai lokacin kuma Nawaz ta yanke jiki ta fadi amma kafin takai kasa Aayaan ya tareta da ƙirjinshi.Kowa tsaye yayi yana kallon Aayaan ɗin cike da mamaki, mutumin dake shirye cikin likkafani amma yanzu gashi tsaye har yana iya taimakon wani mai rai.
Aseey kam da sauri ta rungumeshi haɗe da Nawaz ɗin, itama Mummy kansu tayi tana kabbara, baffan Aayaan ne yace "ku lura fa! Kunsan ba kwari ne da Ayatullah ɗin ba, balle ita kuma Nawwarah ɗin.
Sakin shi sukayi badon suna soba domin gani suke zai bace, suna sakinshi shima yayi baya zai faɗi, kawu da baffa ne suka rike shi gam, harda taimakon Aseey.
Kwantar dashi akayi a saman carpet sannan aka cire Nawaz da itama ke sume a ƙirjinshi.
"Innalillahi wa'inna alaihi raji'un!!! Mummy tace tana tafa hannu ganin jini yana bin ƙafar Nawaz yana sauka a ƙasa, hankalin kowa saida ya tashi ganin jinin jajir dashi, Ummin Nawaz ɗin tafi kowa shiga tashin hankali saboda yadda tasan tasha wuya sosai akan zubar jini, tayi ɓarin ciki da zubar jini yafi sau biyar..
Ruwa Aseey ta miƙo aka yayyafa musu amma shiru babu wanda ya tashi, sai dai duka suna numfashi, waje Sarfraz yayi cikin ƴan kai gawa yana cewa don Allah waye Doctor a cikinku?
Kusan mutum biyar ne suka ɗaga hannu "kuzo muje, don Allah ana buƙatar taimakonku aciki"
Bin bayanshi sukayi ahankali suna tunanin kodai Aayaan ɗin be mutu bane da gaske kamar yadda sukaji wasu na faɗa?, hankalinsu ya tashi matuƙa ganin yadda su biyun suka galabaita sosai, da sauri wani daga cikinsu ya rubuta magunguna a takarda ya miƙawa Sarfraz yace "kayi sauri ka Kawo waɗannan magungunan saboda da alamun guba a Tare dasu duka"Jikin SARFRAZ har rawa yake tsabar tashin hankali, tsoro yakeyi kada suga samu kuma suga rashi, be ɗauki mota ba Kawai ya samu wani zaune akan mashin yace mishi "taimaka ka kaini asibiti"
"Wai da gaske be mutu ba!" Mutane keta tambayar Sarfraz"Eh be mutu ba ya tashi" Cewar Sarfraz dai dai sanda mutumin yaja mashin ɗin da gudu zuwa hanyar babban titi.
Mamaki ne ya kama kowa jin wai Aayaan be mutu ba, wasu har cewa sukeyi ƙaryane, kuma wai baza su tafi ba suna nan sai sunga yadda za'a ƙare.
A cikin gidan kuwa an samu an kai su Nawaz da Aayaan cikin ɗaki kan gado, duba Aayaan ɗin sukayi sosai inda suka tabbatar da guba ce ta sarƙafe huhunshi kuma duka jikinshi ya amshi gubar shiyasa har numfashinshi ya ɗauke na wasu awanni donma Allah ne yasa jininshi ya yaƙi gubar amma da bazai tashi ba.
Kan Nawaz suka koma suna duba me yasata zubar jini haka, cikin idonta suka bude, sai tafin hannnunta da jijiyar wuyanta.
Amma mama itama fa alamun poisoning ne tare da ita, me taci ne?
"Ai Kusan kwana uku bata ci abinci ba saboda koda yaushe allurar Barci akeyi mata, amma ana sa mata drip sosai. Cewar mummy cike da tashin hankali.
Ɗaya Daga cikin likitocin ne yace "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, allurar barci akeyi mata ko da yaushe? Kasheta kukaso kuyi kenan? Ga kuma Alamun ciki nan tattare da ita, yanzu haka idan ba ayi wasa ba cikin ya lalace shiyasa ta fara zubar jini.

YOU ARE READING
SARFRAZ
RomanceLabarine akan Nawaz baiwar Allah, Wadda ta haɗu da gwagwarmaya a rayuwarta, kishiyar uwa ta hanata sakat sa asiri, ta hana kowa kulata, shekararta ishirin da biyar amma batada ko saurayi, daga baya kuma ta turo Yan iska suyi mata fyaɗe, sai gashi ku...